MADADI Page 51 to 60

Mmn Ladi na had’a tea tace”Ke rabu dani dan Allah wallahi jiya da kyar nayi bacci saboda tsabar takaicin da mutumin nan ya ‘kunsa min haba me za’ayi da talauci ace kullum a gidanka baka da sakakken abinci sai shinkafa da wake da mai da yaji haba jama’a wannan wace irin masifa ce ace kudin cefane dari biyu mtsssw!” takare maganar tare da jan dogon tsaki
Mmn Sajida tace”To ina laifi da kika samu shinkafa da waken ni na samu mana! kina kallo fa ni nake ciyar da kaina da ‘ya’yana ke kin samu kina rainawa wallahi ki dinga godewa kad’an sai kiga Allah ya wadataki.” Mmn Ladi kur’bar tea take tana dangwalar bread da miya tace”Duk yanda zanso ki fahimta ba zaki fahimta ba mu bar maganar kawai.”
Mmn Sajida tace”To ai dole na bari tunda bakya so a fada miki gaskiya.” Dariya kawai tayi ta cigaba da cinye musu naman dake cikin miyar gabansu.
Naja’atu tun abun na matar na bata mamaki har ya dawo bata dariya ikon Allah kenan wannan shi ake kira Allah daya gari bambam! Mmn Ladi sai da ta cika cikinta tsaf sannan ta karkad’e zaninta mike tare da kad’a kan yaran ta tafi kaisu makaranta…Naja’atu sai so takeyi suyi gulmar Mmn Ladi ita kuma Mmn Sajidan ta’ki yarda, ta lura da Mmn Sajida tana da kyakkyawar zuciya akan matar.
Naja’atu tayi mamakin ganin gidansu Munira, ita kam bata dauka zata ganshi haka ba sabida irin karyar da Munira take musu a aji cewar babanta mai kudi ne tsohon dan jarida ne da yake aiki a tashar bbc ta kasar waje! bayan nan kuma yana da company na siyar da motoci da sauransu ‘karya iri iri Munira keyi musu su kuma suna yarda sabida ganin irin yanda ake zuwar mata ziyara cikin babbar mota hade da kayan abinci iri iri shiyasa suka amincewa………..Munira bata gidan wai sun tafi shopping ita da Muktar..Mmn Ladi bayan ta huta ta mike da niyyar tafiya, Naja’atu taji kwallah na kokarin zubo mata dan zaman da tayi da matar taji bata son rabuwa da ita… Mahaifiyar Munnira na hakkince a kan kujera Cikin nuna isa da nuna ita wata me kudi ce ta kalli Mmn Ladi da fadin”Ba zaki bari a kawo abinci kici ba sai kice zaki tafi.”
Mmn Ladi tace”Alhamdullhi Hajiya kafin na fito daga gida sai da na karya tukkuna.” Mommyn Munira ta dan gyara zamanta cikin isa ta dauki pose dinta dake gefanta ta zuge zif din ta dauko dubu daya sabuwa kar da ita ta mika mata da fadin”Gashi ki shiga napep.”
Murmushin takaici Mmn Ladi tayi tace”Nagode hajiya wallahi bazan karbi kudinki ba domun kuwa ina da kudin motar komawa gida ta kalli Naja’atu da fad’in” To Naja’atu saduwar alkairi idan kin koma gida ki gaishe da mutan gidanku.” Naja’atu tace”Nagode sosai insha Allah zan fada musu.” Mmn Ladi sa kai tayi ta fita daga palon tana mamakin izgili da wulakanci irin na matar gidan koda yake dama tun kafin ta tako kafarta cikin gidan take da labarinta sai ‘karyar arziki alhalin kowa yasan aikin da babban d’ansu yake yi a gari ‘Ri’ka’kken d’an 419 ne (damfara) Laya ta mussaman ce dashi wace yake ma’kalawa a ‘kugunsa yana shiga ko ina yayi satarsa ya fito ba tare da an ganshi ba, shiyasa komai na rayuwa baya yanke musu a gidan kuma iyayensa sun sani basu hanashi ba sai ma ‘kara masa kwarin gwiwa da suke!…..Duk kuwa d’an kasuwar da ya sake yayi mu’amula da *Bash* to ya zama sorry dan sai yayi masa tas! kuma yasa malamansa sun d’aure masa baki *Bash* mugun hatsabibin mutum ne…….Jama’ar garin kuwa tamkar masu jin tsoro an rasa wanda zai fito yayi magana kowa yaja bakinsa yayi shuru sai dai idan surutu ya tashi ayi a bayan fage.
Naja’atu har duhun dare ya shigo tana zaune a guri guda a rakube dan dama Mommyn Munira bata da sakin fuska tunda suka gaisa wata magana bata sake shiga tsakaninsu ba….Sai bayan magariba ne da taga zaman palon ya isheta ta mike salo salo ta nufi wani daki dake cikin palon taje ta zabga tagumi tana tunanin wannan wane irin shopping ne Munira ta tafi tun safe bata dawo ba gashi dare yayi…Gaskiya sai dai tana tunanin bayan shopping din sunje wani gurin ita da saurayin nata……Abinda naja’atu bata sani ba shine Munira ma kwata kwata bata kwana a gidan ba tana can gidan Muktar din kwananta biyu kawai dai Mommyn tata ce ta tsara cewar sun tafi shopping ne………….. Kwanciya tayi tana share hawaye abin duniya ya isheta gabadaya kuma hankalinta yayi gida tana tunanin yanzu wane hali iyayenta suke ciki sai Musaddiq da yake yawan fad’o mata a rai! Abbah Abbas kuwa dama tuni ta cireshi daga cikin ranta tana ganin ta ku’buta daga hannunsa har abada.
Mai Aikinsu ce ta shigo da sallama a bakinta tace”Wai ki fito kici abinci inji Hajiya.” ta mike da sauri tare da fadin”To gani nan.”
Mai aikin ta juya ta fita daga dakin minti biyu ta mike tabi bayanta..Tana fita taga Mommy a zaune a gurin cin abinci da waya a hannunta tana fad’in “Munira kina da hankali kuwa yau kwananki biyu a waje ko kiran waya bakya yi ashe kina so jama’ar gari su fargaba da lalacewar da kukeyi keda muktar din tun kafin auranku ace kungama sanin junanku wannan wace irin rayuwa ce? to komai dare ki dawo gida domun tun safe kike da ba’kuwa kawarki ce tazo daga kano.
sama sama taji muryar Munirar na fad’in ” Ayya Mommy dama yau zan dawo wallahi Muktar din ne bashi da lafiya shine na tsaya na kula dashi.” Mommyn tace”Bashi da iyayene da lallai sai kece zaki kula dashi ai koma meye zai faru sai ku bari a shafa fatiha tukkuna.” Tace”mommy ba lallai ne ya samu kulawar da yake bukata ba daga gurin mamansa ni kuma shiyasa na tsaya na kula dashi har ya warware kuma mommy meye yayi saura a tsakanina dashi tunda iyayenmu sun mallaka mana junanmu muktar ya bada sadakina ni banga laifi ba dan na kwana a gidansa ba.”
Tace”Ni ba cewa nayi kiyi min tsari ba duk rayuwar da kike so ita za kiyi ni dai nace ki dawo gida yau kinji na fada miki.” Tace”Insha Allahu ko dan saboda Naja’atu zan dawo yau.”
Naja’atu jikinta ne yayi bala’in sanyi jin irin abunda ke faruwa da rayuwar Munira! dama sai da tayi zargin wani abu ashe Munira bata da kamun kai tana bin saurayi har gidansa tana kwana dashi ba tare da aure ba, gaskiya al’amarin ya bata mamaki mutuka…….Mommyn ta kalleta bbu fara’a a fuskarta tace”Kixo ki zauna kici abinci munyi waya da ita tace”Gata nan a hanya.” Naja’atu kawar da mamakin fuskarta tayi ta nuna kamar ba taji wayarsu ba taje ta zauna gurin cin abincin tace”To bbu komai Allah ya dawo da ita lafiya.”
Tana kokarin mikewa daga gurin ta amsa da “amin” *Bash* ne ya shigo palon yana sanye da k’ananun kaya wanda sukayi masa kyau sosai *Bash* irin mazan nan ne masu tsayi da murd’ad’adan jiki shiyasa k’ananun kaya suke masa kyau fari ne tas gashi kyakkyawan gaske! kyawunsa da kudinsa da kuma yanayin tsarin hallitarsa yasa ‘yan mata suke haukacewa a kansa! shi kuma yana cin karansa babu babbaka a kansu duk wacce ya bukaci yayi sex da ita babu gardama zata amince masa *Bash* mugun manemin mata ne kuma dan shaye-shaye na bugawa a jarida ga neman nemanta ga *Luwad’i* duk yana yi…sana’arsa tafi kala goma domin *Luwadin* ma da manyan mutane yake suna bashi mahaukatan kudi….Shiyasa gabad’aya bashi da ra’ayin aure yana ganin aure kamar damuwa ne tunda babu abunda ya nema ya rasa to zai iya kare rayuwarsa ba tare da ya auri wata mace ba.