MADADI Page 51 to 60

Naja’atu murmushi kawai take dadi na ziyartar zuciyarta salon kallon soyayyar da *Bash* ke mata shine yake sake rikita ta tana jin sonsa na sake karuwa a cikin zuciyarta..
Tare suka shiga dakin ita da Munira ta zauna gefan gado tana ta duba wayar Bash din Hotonansa ne kala kala yawancin pictures din bana Najeria bane yayi su a kasashe daban daban! ganinshi rungume da turawa black americas bai dameta ba tana ganin ai wayersa da kudinsa ya cancanta yayi mu’amula da kowane irin jinsin mutum..Munira ta fito daga wanka tana kintsa jikinta tace”Gaskiya Naja’atu kinsha wuya na tausaya miki kuma wannan matar data taimake ki yana da kyau naje nayi mata godiya.” Tace”Gaskiya kam yana da kyau idan an kwana biyu muje na rakaki gidanta…Munira ta zauna kusa da ita tare da fad’in “To alhamdullhi Yanzu mun samu ciki ya zube ba tare da munsha doguwar wahala ba yanzu babban abunda yake gabanmu shine rabuwa da wannan tsohon.
Hankalinta nakan wani had’ad’dan hoton *Bash* wanda ya dauke shi yana sanye da kayan wanka a bakin swimming hoton yayi masifar dauke mata hankali ganin zahirin *Bash din* ya sake firgitata sai ta sake kwadaituwa da auransa hakika ta samu nasarar auransa to ta kere sa’a kuma zata iya shiga koina dashi ta nuna shi da sunan mijinta ba kamar Abbah Abbas ba da take jin kunya a dangatata dashi a matsayin miji…
Munira ganin Naja’atu bata fuskantar maganar da take yasa ta le’ka cikin wayar tana dubawa! Dariya tayi tace” Naja’atu kenan naga alama kema kin mutu akan Brother d’ina Humm! na taya ki farin cikin samun zuciyar *Bash* ‘Yan mata da yawa suna sonsa baya ta’ba sauraransu amma ke gani daya yayi miki ya haukace harda maganar aure duk da kasancewarki bazawara yana da kyau kiyi gaggawar nemawa kanki mafita tun kafin damar da kika samu ta kufce miki.”
Ajiyar zuciya ta sauke tace”Yanzu wace shawara kike ganin ta dace? Ni da cewa nayi zan tura masa da text na fada masa cikinsa ya zube kuma ina nan ina jiran takardarta.” Munira tace”Wannan shawarar tayi…..Kawo wayar na rubuta masa text din…Naja’atu tasa numbarsa da yake amfani da ita a saudia, Munira babu sallama ta shiga rubuta text din kamar haka.
_Ni ce Naja’atu ina so in tabbatar maka da cewar wannan cikin daka yi min yabi rariya dama tun kafin haka ta faru sai da na fad’a maka bani da ra’ayin zama da kai ballantana har na haihu dakai komai ya faru son zuciyarka ne ya janyo maka….Abbah banso muyi irin wannan rabuwar da kai ba amma ina ganin hakan shine daidai Ni ce dai Naja’atu ina nan cikin koshin lafiya bayan samun nasarar rabuwa da masifar daka ‘kunsa mun a cikina ina nan ina jiran saki daga gareka idan baka sakeni ba to kuwa zanyi ta zama a inda nake har’karshen rayuwata_
Kafin a tura text din Naja’atu sai da ta karanta kusan sau biyar tana ganin kamar maganganun sunyi tsauri da yawa! amma kamar wacce aka sawa lemon tsami a baki ta kasa cewa komai tana kallo Munira ta tura text din ya tafi gabanta sai ya tsananta fad’uwa cikin zuciyarta tana ji kamar bata kyauta ba…Munira tace”Yana da kyau ma a tura masa ta whasap dan naga kamar yanayi ko.”? A sanyaye tace”Duba ki gani.” Munira ta shiga dubawa taga numbarsa tana whasap amma kuma kwanansa biyu bai hau ba, dan tun ranar daya bude ya saurari audion da Salim ya turo masa bai sake kunna data ba dan dama ba kasafai yake shiga whasap din ba…..Tace” Ya kwana biyu baya kai amma Bari a tura masa domin ya dauki abin da muhimanci.”
Naja’atu dai shuru tayi Munira sai zartar da hukunci takeyi ita kuma gabanta sai faduwa yake tana adduar Allah yasa ya mayo da martanin saki.
Munira kayan ciye ciyen data shigo dashi ta baje musu suka dinga ci suna hira Naja’atu dai daurewa kawai take bini bini sai ta duba wayar dake hannunta wai ko ya turo amsa…..Jiki a sanyaye ta ajiye wayar ta nufi toilet din dake cikin dakin tayi wanka ta kimtsa jikinta tare da sanja pad ta fito Munira ta bata sababbin kayan bacci tasa tasa turare ta zauna tare da daukar wayar tana sake dubawa…Ita kuwa Munira tana kwance a bad daga ita sai ‘karamar vest da gajeran wando wanda ya matseta sosai pictures take dauka kala kala tana turawa Muktar ta whasap…..
*Allah ya shiryaki Munira*
‘Bangaran Abbah Abbas kuwa bai samu damar duba wayarsa ba sai lokacin da yazo kwanciya dan basu dade da shiga masaukin nasu ba sun fita duk gabadayansu sun dan shiga kasuwa dalilin barin ‘kasar da za suyi jibi idan Allah ya nufa dama kwana goma sukeyi ko sati biyu suke dawowa……..Halisa na kokarin kwanciya a kusa dashi taga ya mi’ke zumbur! Gabanta ne ya fad’i! tayi saurin matsawa dan ta dauka marinta zai yi! sai dai kuma ganin ya tsirawa fuskar wayarsa ido yasa da sauri ta ‘leka kanta tana dubawa! Text din ta karanta tsaf! kuma ta fahimci daga Naja’atu yake…Wani matsiyacin dad’i ya rufeta wayyo yau da ita kadaice a gurin sai ta taka rawa ciki ya zube burinta ya cika…….Kukan munafurci ta fashe dashi ta shiga tafa hannu tana fad’in”Innalilihi wa’ina ilahi raji’una! yanzu yarinyar nan sai da ta zubar da cikin nan? anya naja’atu tayi maka adalci kuwa? me kayi mata take maka irin wannan ‘kiyayyar Allah ya baka zuria tayi maka asararsa kuma sabida bata da kunya cikin izigila take fad’a maka ga abunda ta aikata maka kai jama’a amma wannan yarinyar bata kyauta ba wallahi.”
Shuru yayi domun bakinsa mutuwa yayi murus! ya dinga kallon fuskar wayar yana ta karanta text din kamar me koyon karatu!! ya jima cikin wannan yanayin kafin ya samu damar furta kalmar innalilihi wa’ina ilaihi raji’un!!! Ya kashe wayar ya ajiyeta kana ya mike ya nufi toilet domun dauro alwala…Halisa murmushin jin dadi tayi ta juya bayanta tare da jan bargo ta rufe jikinta cike sa nishadi da farin ciki bacci mai dadi ya dauketa.
Dadduma ya tsaya ya fuskanci al’kibula ya tayar da sallah…Raka’a biyu yayi ya jima a sujjadar karshe yana rokon Ubangiji sassauci ya d’ago tare da sallame sallahr nan ma ya jima hannunsa a sama yana addua kafin ya shafa a fuskarsa ya mike yana jin wani kuzari a jikinsa zuciyarsa tayi wasai babu wani bacin rai tabbas tunda har Allah ya zartar da irin wannan hukunci to hakan shine alkairi a rayuwarsa…..’Yar jakarshi da yake tafiya da ita ya dauko ya zauna kasan kafet ya bud’eta a nutse ya dauko wani memo ya ya bud’e ya yagi pepar d’aya ya dauki biro a nutse ya soma rubutu a jiki….
*Jikina na karkarwa na le’ka domun naga mai yake rubutawa……???? yanke jiki nayi na fad’i hawaye na ziraro min shikkenan Naja’atu ta cuci kanta*
_NI ABBAS SAMA’ILA NA SAKI MATA TA NAJA’ATU MALAM SANI SAKI DAYA INA RO’KON ALLAH YASA HAKA SHINE YAFI ALKAIRI A TSAKANINMU._
*Kuyi hakuri dan Allah???????????? Nima ba’a son raina ba Labari ne yazo a haka*
*Littafin na kudi ne..!*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abun yake.
Vip group #600
Normal gruop#300
accont 0542382124…Binta umar gtbank..Idan katin waya zaki turo kiyi min mgn ta whasap da wannan numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*MANZIR _ALWAFIR ABUJA????????*
_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu babu almundahana a ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar dasu to kukanki ya ‘kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_