MADADI 1-END

MADADI Page 51 to 60

 Mddbhrmbn46

A nutse ya linke takardar da yayi rubutun ya bud’e tsakiyar memo d’in yasa ya mayar da jakar ya rufe tare da mikewa da ita a hannunsa zuwa yayi a dana ta a inda take kana ya nufi bed din ya kwanta yana jin nutsuwa da kwanciyar hankali na saukar masa a zuciyarsa tabbas rabuwa da auran Naja’atu shine alkairi a tare dashi, dan idan ya tilasta kansa zama da ita to kuwa zai ta had’uwa da takaici da ‘bacin rai watakila ma sanadiyar hakan ciwo ya kamashi dan a yanda yake da kaunar ‘ya’ya gami da adduar Allah ya bashi zuria da yawa baya tsammanin zai iya zama da kowacce irin macece mutukar zaiyi wahalar dasa ‘kwai ta zubar masa babu shakka ko wacece zai iya rabuwa da ita rabuwa ta har abada…Cikin kwanciyar hankali yayi bacci da asubah ya tashi zuciyarsa wasai baya ta’ba nadamar abinda ya aikata ga yarinyar.

‘Bangaran Naja’atu kuwa kwana tayi tana munanan mafarkai wanda taga Halimatu tazo mata da wasu fararan kaya masu kyalkyali sai dai yanayin yanda taga ‘Yar uwartata ya bata tsoro fuskar Halimatun babu walwala ta tsira mata ido kawai tana kallonta ita kuma sai magana take mata tana kokarin rike hannunta sai ta fizge ta bar gurin da sauri ta dinga waige waige tana kiran sunanta amma bata ganta ba……Sannan kuma duk a cikin mafarkin taga mahaifiyar ta na kuka ita da Mussadiq suna kiranta….a tsananin firgice ta tashi tana had’a gumi! ta dinga kallon dakin gabanta na fad’uwa gaskiya mafarkin nan ya bata tsoro tunda Halimatu ta rasu bata ta’ba yin mafarki da ita ba sai yau shiyasa jikinta yayi sanyi…Wayar *Bash* ta dauka ta kunna ta haske dakin a maimakon ta tashi taje ta dauro alwala sai kawai ta shiga dube dube a wayar wai ko bayan kwanciyarta Abbah Abbas ya turo replay ta gama dube duben ta ba taga komai ba a sanyaye ta ajiye wayar ta mike ta nufi bandaki domin yin alwala…..Kafin ta tayar da sallah sai da ta tashi Munira tukkuna ta hau dadduma…Munira kuwa zuwa tai tayi fitsari ta dawo ta sake kwanciya dama can Munira bata sallah sai gari ya waye…Naja’atu bayan ta idar da sallah zama tayi kan daddumar abin duniya ya dameta mafarkin da tayi yayi masifar bata tsoro mussaman ganin mahaifiyarta na hawaye tasan duk inda suke suna can cikin tashin hankali da damuwa, ta dinga share hawaye tana fad’in Ba laifina bane tun farko na fada muku bana so bana sonsa kuka kasa fahimtata.” Munira tayi firgigt ta mike zaune tana kallonta tace”Naja’atu lafiya kike kuka.”? Hawaye ta share tace”Munira wani mummunan mafarki nayi wallahi tabbas iyayena na cikin damuwa da rashin ganina.” Munira tace”To ai dama dole su shiga damuwa da rashin ganinki ai tun farko laifinsu ne yanzu dan sun neme ki sun rasa ai kansu zasu tuhuma sai su gane auran dole ba abune mai alfanu ba.” 

Girgiza kanta kawai tayi tace”Munira naga Yaya Halimatu a mafarki tana cikin ‘bacin rai ga Mussadiq na kuka yana kiran sunana jikina ya soma sanyi da wannan al’amarin wallahi.” Munira taja tsaki tace”Ai shikkenan sai kije kiyi tayi waye ya fada miki mafarki gaskiya ne? dan Allah ki daina wannan maganar idan zaki saki jikinki ki saki jikinki kawai ki watsar dasu koma meye ya faru ai sune suka janyo me yasa suka aura miki wanda bakya so.”

Girgixa kanta ta cigaba dayi hawaye na sake zubo mata…Ita kuwa Munira ta mike ta nufi bandaki tana surutai kan damuwar da taga Naja’atun ta shiga….

Abbah Magaji na zaune yana karya kummalo Halisa ta fito daga dakinta hannunta rike da wayarta ta zauna kusa dashi, tace”Kaga ina ta kiran numbar ba dauka ba kuma wannan numbar itace nake tsammanin ta ‘Kawarta, dan bana mance ranar da tazo tace na bata aron waya zata kira ‘kawarta a jos.”

Yana goge bakinsa yace.”Bani numbar na gwada kira.” Wayar ta mika masa yasa numbar a wayarsa cikin ikon Allah tana fara ringing aka dauka….Hands free yasa yayi sallama…Munira ta amsa da fad’in ” Da waye nake magana.”? Yace.”Kina magana da wani bawan Allah ne daga kano shin ko kinsan wata yarinya Naja’atu.”?

 Naja’atu sai da ta kusa sakin fitsari a wando jin muryar Abbah Magaji radau a kunnanta!!! Munira tayi saurin kallonta idanunta duk sunyi gwale gwale. Abbah Magaji yayi gyaran murya had’e da fad’in “Hello kina jina kuwa.”? Munira ta shiga inda inda da fad’in ” A’a ban santa ba wallahi.” Yanayin yanda take maganar cikin rashin gaskiya yasa ya fahimci cewar yarinyar da hadin bakinta dangane da faruwar al’amari…Yana kokarin yayi magana Munira ta kashe wayar suka ‘kurawa juna ido ita da Naja’atu, ya akayi tun ba’aje ko ina ba asirinsu zai tuno..Naja”atu kuwa ai tuni hawaye sun ‘balle mata fargaba da tsoro duk sun cika mata zuciya.

Abbah Magaji yabi wayar da kallo yana mamakin kashe masa da yarinyar tayi girgiza kansa yayi tabbas biri yayi kama da mutu, wayar ya sake kira….Munira ta zabura tana kallon wayar ta’ki dauka har ta katse Abbah magaji ya sake kiran wayar nan ma Munira taki dauk’a..Sai kawai ya ajiye wayar yana murmushi hade da kallon anty Maryam yace.”Duk yanda akayi yarinyar nan tasan inda Naja’atu take kuma da alama da akwai hadin bakinta dangane da faruwar al’amarin.” Anty maryam tace”Nima tunda naji yanda take amsa maka a tsorace yasa na fahimci tana da masaniya akan abinda yake faruwa yanzu koda anje jos din ai ba’asan a ina za’a same inda yarinyar take ba ballantana a tambayeta inda Naja’atun take.” Yace.”Kada ki damu mutukar layin yana aiki zansa ayi min bunkicen inda suke gobe zan shirya na nufi jos din.

Tace”To Allah yasa a dace ai gobe ma abokin naka zasu dawo ko.”? Yace.”Eh insha Allah bana tsammanin ma zai sameni dan da wuri zan tafi.” ajiyar zuciya ta sauke tana sake tausayawa Naja’atu halin data jefa kanta.

Munira tace”Dallah ki daina kuka mtwwss wai sai me idan sunzo sunga inda kike ke ba zaki iya kaisu kuto bane alkali ya kwatar miki ‘yancin ki ko dole ne akace sai kin zauna da wanda suke so ni wallahi banta’ba ganin inda akayi hakaba.” Naja’atu na kokarin yin magana Bash ya shigo dakin yana sanye da t_shat fari tas da 3qutar wuyansa sanye da siririyar sarqa tamkar wani arne sai wani irin kamshin turare yake mai dadi! Yana ganin Naja’atu na kuka yaji hankalinsa ya tashi ba tare da tunanin komai ba ya zauna kusa da ita had’e da rungumo kafadarta yana tambayar abinda yasa ta kuka! Naja’atu tsorata tayi ta matsa gefe tana share fuskarta…Munira ce ta shiga fad’a masa abinda yake faruwa…Tsaki yaja ya dauko wayarsa dake cikin aljihun wandon jikinsa ya mikawa Munira wayar da fad’in “Ki samin numbar mutumin da ya kira yanzu ni zan fada masa Naja’atu tana jos sai me.”?

Da sauri Naja’atu ta kalleshi yace”Baby maganar rufe rufe bata kamata ba gwara ayi komai a bayyane ni zan tsaya miki a duk inda za’aje ba zaki koma gidan wannan tsohon ba tunda bakya sonsa zan shigar miki da ‘kara kuto.”

Munira tace”Nima haka nace mata ta daina kuka tana tayar da hankalinta ai akwai sharia! 

Naja’atu girgiza kanta tayi tana hawaye tace”Bash ina ganin kima da darajar iyayena bana so na ‘bata musu rai ko kuma na tozartasu dan Allah kada wata mummunar kalma ta shiga tsakaninka da yayana kaji ko.”

Yace.”Baby ke kina daukar al’amarin da sauki ko? okey na fahimci kaunar da kikewa mahaifanki bai kai wanda kike min ba ina ganin zan cireki daga rayuwata kawai shi yafi alkairi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button