MADADI Page 81 to 90

Abbah Abbas yaji dad’in samun wannan kyakkyawan result d’in dan har sai da ya kasa ‘boyewa ya nuna a fuskarsa kyautar kudi masu kauri yayi Dr din suka kama hanya suka tafi, Dr Sa’adatu ta dinga murmushi tana jin wani iri a jikinta hakika mutumin na burgeta mutuka tana adduar Allah ya bata miji mai irin halinsa.
Tun daga ranar Abbah da Halisa suka d’inke Halisa aka dawo amarya aka dinga gwangwajewa da ango ana biyan bukatar juna, sai dai bangaran mutumin naku daurewa kawai yake amma ba wani daidai yake ji ba dan ya tsani yaji ya shiga gurin yaji shi sakwaf-sakwaf! Halisa ta riga ta gama bud’ewa magungunan gurin ‘yar Sa’adu sunyi mata mummunar illah! Haka dai yake hakuri yana biya wa kanshi bukata ba tare da ya nuna mata wani abuba, sai duk sanda takaici ya ishe shi kasa hakura yake a cikin kwananta zuwa yake gurin Zainab ya baje kolinsa yanda ranshi yake so sai bayan ya samu nutsuwa zai dawo yana da ya sani dan Zainab kwana takeyi tana kuka da fad’in cikinta ciwo yake hankalinsa ya tashi da kyar yake rarrashinta.
Salim abin duniya ya isheshi ya rasa makama kullum yana gida a kwance yana tunani gabadaya yanzu kunyar fitowa yake saboda irin kallon da Jama’ar gari ke masa! Ya kai sati biyu a gida baya fitowa sai da daddare nan ma baya dadewa zai dawo gida ya kwanta, mahaifinsa kuwa har ya koma bakin sana’arsa baya amsa gaisuwarsa fushi yake dashi sosai da sosai………Ranar Lahadi ya shirya tsaf domin zuwa gidansu Salimat budurwasa wacce aka kai kudin aure da sa rana, ya fito da key din motarsa simi simi ya fita daga gidan kai tsaye motarsa ya shiga ya nufi gidansu Salimat……….
Salimat ta sameshi a cikin mota a zaune ta bude ta shiga ta zauna ta kalleshi tana ta’be bakinta tace”Wai dan Allah kwana biyu me yake damunka ne naga duk kabi ka susuce ka ma daina zuwa gurina kullum kuma idan na kira wayarka sai naji ka a cikin hali na damuwa wai ko ka daina sona ne.”? Salim ya girgiza kansa yana kallonta yace”Ba haka bane salimat kwana biyu bana jin dadi wallahi shiyasa kika kasa gane kaina amma yanxu naji sauki sosai inaso ki fad’a min meye damuwarki.”
Ta’be bakinta tayi tace”Kasan bani da wata damuwa sai ta kud’i yanzu ma inaso ka sanja min waya sannan na kwana biyu banyi ciye ciye ba inaso muje ka siya min kayan kwalliya da sauran abunda nake bukata.”
Yace.”Okey shikkenan kada ki damu.” Motar ya kunna kai tsaye suka fita daga cikin unguwar…….Kafin su tafi shopping din sai da suka tsaya a P.O.S tana kallo Salim ya bada atm dinsa da accont number nasa, suka bashi abun yasa nambobin sirrin sa duk akan idonta kudin da yake bukata suka miqa masa ya kar’bi atm dinsa suka fita daga gurin….
Lokacin da suka shiga motar ya manta bai mayar da atm din cikin wallet dinsa ba ya fad’i kasan site a kan idonta sunayi parking a daidai gate din Jujin lambo ya bude motar ya fita ita kuma tana ganin fitarsa tayi saurin sunkuya ta lalubi atm din tasa a cikin pose din dake hannunta ta bude motar tabi bayansa cikin gurun……Siyayya yayi mata sosai da sosai suka fito da kaya a hannunsu, kafin ya kaita gida sai da ya siya mata kayan ciye ciye irin wanda take so sannan ya kaita gida, to yaso su danyi abun da suka saba kafin su rabu taki bashi damar hakan tace ita ta gaji gobe ya dawo da wuri zata bashi mamaki! yace shikkenan, sallama sukayi da juna yaja motar yayi gaba………A ranar Salimat kasa bacci tayi saboda tunanin yanda za’ayi ta cire kudaden dake cikin account din Salim gashi ita ba account ne da ita ba, sai ta samu Yayanta Mai suna Naburago mugun dan son banza ne Naburago baya gudun Allah ya isa duk inda yaga bashi sai yaci bashi da sana’a sai buge buge da ita suke rufawa kansu asiri kasancewar su marayu ubansu ya mutu shine kuma namiji shiyasa wahala tayi yawa a kansa, talauci yasa Salimat lalacewa maza babu irin wanda bata sani ba shi kuwa Naburago rigima ko ta uwar uban waye saka kansa yake a ciki ayi ta fafatawa dashi a rabu dashi dan idan yaci bashi aka zo aka turkeshi ya biya sai ya mayar da abun wasa idan mutum ya kaishi gurin ‘yan sanda kai tsaye yake fad’a musu bashi da kudin da zai biya bashi idan kuma ana kar’bar shekaru zai lissafa shekarunsa ya biya…..Su kansu ‘Yan sandan sun sallamawa Naburago shegen kansa gashi da kwarjin tsiya komai takatsantsan di’nka a kan kayan sana’ar ka idan yazo kar’ba bashi mutum baya sanin sanda yake dauka ya bashi…….Salimat shi ta samu da maganar ta fada masa abunda ke faruwa, Naburago yayi tsalle da juyi a dakinsa yace.”Bani atm din jeki kwanta ki huta kudi zasu koma account d’ina wahala ta yanke mana.” Salimat ta fad’a masa numbobin sirrin na Salim din yace to magana ta kare…….Alwala yayi ya yay sallah ya fita da atm din cikin aljihunsa.
A ranar Naburago ya kwashe kudaden account din Salim tas ya mayar nasa accont din……Salim sai shigowar alert kawai yaji yana dubawa yaga a’lamarin daya afku babu abinda ya fara dubawa sai wallet d’insa ya nemi atm dinsa ya rasa a gigice ya nufi motarsa ya shiga dubawa sako da loko babu atm! cikin tsantsar tashin hankali ya shiga motar ya kunna a guje ya nufi P.O.S din da sukaje kawai ya fad’a musu guri kamar mahaukaci yana dube dube….Ai a take wani Police dake gurin ya damqe shi a cewarsa yaga yayi yanayi da masu laifi dan yanda yaga ya shigo gurin a kid’ime ya nuna masa hakan! aikuwa jama’ar dake gurin suka gazgata hakan dan ganin yanda Salim din ke muzurai yana wani irin gumi! sai rawar baki yake ya kasa magana…..Yana ji yana gani aka sashi a mota aka tafi dashi police stion kamar wanda aka daurewa baki ya kasa cewa komai zufa ce kawai ke tsatstsafowa daga jikinsa……….
_*Yau tafe nake da ‘yar tsaraba ta ????*_
*’Kawata matso kiji wata muhimiyar magana☺️ A kwai gurare masu daraja da muhimanci a jikinki….1 Headquarter naki…2 Hamtarki….3 qasan nonuwanki…..4 Tsakanin cibiyarki! Wad’annan guraran nada mutukar mahimanci a gurinki yana da kyau ki kula dasu ki mutunta su…..Na farko dai ke kanki kin san barin gashin hammata dana headquarter babbar matsala ce a gurinki waccan ka iya janyo miki imfaction gami da rashin jituwa da miji kullum ya kasance kin zama abar kyama a gurinsa, barin gashin hammata a gurinki sam! bai dace ba, ba dan komai ba sai dan ansan ita mace daban take da namiji kada kiga mijinki da gashin hammata kice kema ba zakiyi aski ba a kull!???? ke daban shi daban! ke ai abun kunya ne a gurinki ki d’aga hammatar ki a ga gashi! Wallahi duk ranar da kikayi kuskure kika bar mijinki yaga d’audar hammatarki kin cuci kanki????????♀️ sannan kika sake mijinki ya shaqi warin hammatarki kin zubar da qimarki????????♀️ duk da kasancewar yanzu muna lokacin sanyi kada kice ai yanxu sanyi ne ba’a wari kiqi yin aski wallahi duk turaran da zaki saka sai yaji warin jikinki saboda haka kiyi hattara………Warin qasan nono na mussaman ne???? ba ko wace macece ke kula da da wanke qasan nononta ba, to bari kiji mutukar kika ga mijinki a lokacin da kuke sex yana kauda kansa daga gurin nono ki to wallahi wannan warin yake damunsa, ina amfani ace kinyi wanka baki d’aga nonuwanki kin wanke ba???? ai kamar ba kiyi wanka ba k’awata! Kisa sabulu ki wanke kasan nono tas kisa masa turare na mussaman sai kiga maigida na zumud’in kai kansa gurin……..Ramin cibiya yana tara daud’a saboda gurin a tsuke yake baida spece sosai, yana da kyau kullum idan kinzo wanka kina sa bakin soso a hankali a hankali kina wankewa kada ki bar ramin cibiyarki da daud’a domin hakan na iya janyo miki matsala mai girma………..Wannan tsarabar tawa ba ta mantan aure bace kawai har daku ‘Yan mata da zawarawa ‘yan kwalisa ????……To sai mun sake had’uwa daku a fita ta biyu????????♀️*