MAKAUNIYAR KADDARA 55

karonma na yanke shawarar a Nigeria zata haihu babu inda zataj……”
Tassss!!! kakejin sautin fashewar kofin hannun Farah da take shan tea tun shigowarsa. aunty Zakiyya kam a bazata tace, “What!”. Mammah kuma ta ɗan
zabura jikin kujera da faɗin, “Baka isaba ko!”.
Yanda sukai ɗin ba ƙaramin mamaki ya bama Mahma ba, shiko sai yay wani shegen murmushi da komawa ya lafe jikin kujera yana zuƙar sassanyan numfashi da
iskar ac ke busowa.
Mahma tace, “To minenen abin razana anan? Dan kawai yace a Nigeria matarsa zata haihu? Ai hakan da yay shine dai-dai, kuma shine zai ƙara kawo dai-
daito tsakaninta Farah da ƴan uwansa ko?”.
“Adda bazai yuwuba wlhy, karma ki goya bayansa a wannan gaɓar dan tafiya da Farah kamar nayi na gama ne, sannan maganar yarinyar dake gidanka yaya
muke ciki?”.
“Ki tayamu addu’a kawai Mammah”. Ya faɗa kansa tsaye.
“Uban addu’a zan tayaku ba addu’a ba Abdul-Mutallab, ni kake gayama na tayaka addu’a akan wannan figaggiyar yarinyar da’a haihuwar kaji ka isa
haifarta, to wlhy tunma muna shaida juna ka sakar musu yarinya ko na ɓata maka ranka”..
“To amma Mammah baƙya ganin idan na aikata hakan shima Baffah zai ɓata ran nawa? Kiyi haƙuri kawai kamar yanda nai biyya a zaɓinki shima nayi biyayya
anasa. sannan kuma idan ina sonta kuma fa….”
Kafinma ya rufe baki Farah ta fashe da wani irin razanannen kuka sai da Mahma ta daka mata tsawa tasa hannu ta toshe bakinta tana faɗawa kan Mammah.
A zafafe aunty Zakiyya tace, “Wlhy inma baka saketaba da ƙafarta saita bar gidan”.
Banza yay kamar bai jitaba, zata sake magana Mahma ta harareta dole tai shiru tana ƙunƙuni. Cikin rawar murya na alamar jin zafi Mammah tace, “Abdul-
Mutallab na rantse zan iya tsine maka akan auren yarinyarnan. Dan haka na baka kwanaki bakwai kacal ka sallameta. Idan kuma ka kuskura ko ɗan yatsanta ka
taɓa ALLAH ya is……”
Da sauri yace, “Oh Mammah Please!…..”
Yanda yay maganar cike da ƙosawa ya sata dakatawa tana kallonsa. Cikin ƙunar da zuciyarsa ke masa yace, “Bama sai kinyi wani ALLAH ya isaba haba
sweetheart, nifa wasa nake miki kawai dan naga yaya ƴarki zatayi? Tana sona har yanzu kokuwa?, indai nine ki bani wata ɗaya kacal zanyi komai a tsare yanda
shima Baffah bazaiga na masa tsageranci ba harya canja wata hanyar da ni dake zamu gaza ganewa kuma ok?”.
A yanda yay maganar seriously yasata yarda dashi, dan tasan halinsa bayason dukkan abinda zai ɓata mata rai, cikin gamsuwa tace, “Idan ka saɓamin
alƙawari Abdul-Mutallab bazan maka da sauƙiba fa”.
“Karki wani damu kanki Noorunnisa, sai dai ga shawara, dan akwai abinda naɗan hango idan akace na saketa yanzun, kiɗan sassauta kinsan shima Baffah
akwai taurin kai, idan wata ɗaya bataiba zan iya kaiwa biyu ko uku haka, dan dole na haɗa da Granny, kinga hakan na nufin kenan gara ayi sakin cikin hikima
yanda zan ɗaura laifin akan wani abu taimin ita yarinyar bawai kece kika saniba. Dan wlhy yanda Baffah ya fusata nace zan saki yarinyarnan yanzu to kuwa zai
auramin mata uku rana ɗaya, ya kuma kafamin sharuɗɗan masu tsauri da bazan iya yin wani abuba, kinga kema yaci galaba a kanki kenan, amma idan cikin hikima
mukai komai sai a rabu lafiya. Taɓa yarinya kuwa ki ɗauka ko kallo bata ishi Abdul-Mutallab ɗinki ba, na Farah ɗinkine kawai har a aljanna”.
Karan farko ta saki tattausan murmushi da cewa, “To ALLAH yay maka albarka, naɗan gamsu da bayaninka danni shaidace akan Kabeer da halayensa, amma
kamar yanda ka faɗa ta wannan hanyarne kawai zamuyi maganinsa da wannan kakar taku sarkin iko wa ƴaƴan wasu”.
“Amin sweet Mammah”. Ya faɗa yana wani shegen murmushi daya zafafa zuciyar aunty Zakiyya ta miƙe fuuu ta shige. dan itakam tsaf ta fahimci shirya
rainama uwar tasa hankali yayi kawai.
Mahma kuwa murmushi tayi itama da cewar “Nasan zaka iya Abdul-Mutallab, kamar yanda Hindatu ta faɗa haka mukeson kayi, abinda yasa zan goya bayanka
kamar nan da wata ukun saboda dalilan daka faɗa suna akan hanya”.
“Nagode Mahma” ya faɗa yana wani lumshe idanu da komawa jikin kujera ya lafe abinsa.
Sosai dariya kecin zuciyar Mahma tanata ƙoƙarin danneta, a ransa kuwa tanata saka masa albarka da ƙarajin ƙaunar AK ɗin har cikin ranta. A kullum
ƙoƙarin sa yaga ya kauce ɓacin ran mahaifiyarsa koda ace ya fita gaskiya, irin wannan ƴaƴan sune abin buƙatar kowa, dan suna ƙoƙarin kiyayewa daga fushin
mahaifiya, su kuma kautar da ita faɗawa halaka itama dake zuwa akan dokin fushi kona son zuciya.
Farah ma tashi tai ta shige ɗaki tana rusar kuka. Hakan yasa AK miƙewa yabi bayanta. Mammah zata bisu Mahma ta dakatar da ita.
“Kinga barsu ya lallashi abarsa da kansa. Babu ruwanki a wannan sabgar tunda kinji daɗi yace zai miki abinda kika buƙata saboda ƴar so ɗin taki”.
Ƙaramar dariya kawai Mammah tayi da komawa ta zauna. “Oh Addah kemafa kina bayanmu wannan karon bare kimana wa’azi”.
“Ai nabi bayankunne kawai saboda farin cikinki, sannan nima matar tasa bataminba tayi ƙarama da yawa”.
“To kema dai ƙya faɗa Addah, bandama namiji baida kunya ba, ta ina zai fara nuna wannan ƴar ficilar yarinya matsayin matarsa”.
Dariya sosai Mahma tayi abinta.
AK da Farah kam kusan tare suka shiga ɗakin, ta faɗa saman gado tana sake fashewa da kuka mai cin rai. Shiko yana shigowa ya ɗaure fuskarsa tamau da
murzawa ƙofar key sannan ya ƙaraso gaban gadon cikin takun izza da bayyanar ɗacin da zuciyarsa ke masa ƙuru-ƙuru akan fuskarsa. Cikin tsananin kaushin murya
yace, “K tashi zaune!”.
Sosai yanda taji muryarsa ya ƙara razanata. Dole ta miƙe zaunen dayace tana kallonsa idanunta cike da tsoronsa. Ƙafarsa ɗaya ya ɗora saman gadon ɗayar
na ƙasa yana binta da wani shegen kallo daya saka jikinta fara tsuma tana girgiza masa kanta hawaye na rige-rigen fitowa.
“Share waɗan nan hawayen, kuma ki nutsumin wlhy kona karyaki a ɗakin nan na karya banza”. yay maganar yana matsar da fuskarsa gab da tata da nunata da
ɗan yatsansa cikin gargaɗi. Hannu tasa da sauri ta goge hawayen tana magana cikin rawar murya, “Yah Abdul-Mutallab wlhy ba laifina bane, ni bani nace zanzo
nan ba, tashi kawai nayi na ganni anan gidan”.
“Bashi na tambayekiba, dan matdalarkice ba tawaba wannan”. Ya katseta a kausashe.
“Dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy banason kishiya, zan iya mutuwa ka taimakeni ka barni ni kaɗai, na rantse da ALLAH zan dinga maka duk abinda kake so
daga yanzun”.
“Daga baya kenan yarinya. ai kin makaro kuma, dan na baki damammaki bama damaba amma kika cigaba da ɗaukata ɗan iska ko maijin tsoronki ma. Dama na