MAKAUNIYAR KADDARA 55

tabbatar miki a randa yaran nan sukaje London inhar kika sakamin ciwon kai sai na baki na zuciya. Koda yake wannan duk bashine a gabanaba yanzu, dan idan na
tafi kema kinsan bana waiwaye. Gargaɗi zan miki idan kinbi kin huta, idan kinmin taurin kai da shirya samun ciwon kai wlhy sai na saka miki na jini bayan na
zuciyar da kika samu yanzun, kindai sanni sarai. Koda ban miki gargaɗin nanba nasan baki da wata dama ta sake barin ƙasar nan yanzu, amma dole zan miki.
Kiyi duk yanda zakiyi ki tabbatarma da Mammah zaki haihu a Nigeria, inba hakaba wlhy ki kuka da kanki, dan inhar ta ɓata ranta a kaina toke zuciyarki da
kamanninki zan ɓata gaba ɗaya a rasa ganeki. Ki kuma nutsu akan wannan haukar sumar da kuka da kikema mutane, bake kika jawa kanki kishiyar ba, saurama biyu
zan ƙaro bayan wannan shashasha kawai”.
Ya ƙare maganar da sauke ƙafarsa ƙasa yana binta da wasu shegun looks masu riƙe maƙoshi da ƙahon zuciya.
Sai da yaje gab da ƙofa ya juyo cikin wani gargaɗin yace, daga nan zuwa kwana biyu ki dawo inda na ajiyeki, na baki kwana biyunne ma dan banason
takurar kowa a cikinsu, idan kuma kin fita yanzu ki sanar musu duk abinda mukai a ɗakin nan, ni kuma na tabbatar miki sunana Abdul-Mutallab Kabeer Shira”.
Daga haka yay ficewarsa. Koda ya fito falon babu wata alamar akan fuskarsa dazai nuna ba lallashin Farah yayba da gaske. Bai zaunaba yay musu
sallama akan yana son yin wani uziri ƙilama ya wuce Jigawa duba masu aiki.
Mammah ce ta kallesa cikin harara, “Ban gane zaka wuce Jigawa ba tickets ɗinmu fa?”.
“Oh GOD, Mammah Please kibar maganar zuwa Morocco ɗin nan dan babu ita, idan haihuwarta a london ne baƙyaso nace miki zata haihu anan ne. Zaku iya
barmata Mahma su zauna tare kokuma a samo tsohuwa daga Morocco ɗin ta zauna da ita, ke kanki akwai maganar business da nakeson nayi dake wani abokina
yanason kaya naga kuma kina dasu. Bye bye ana jirana nikam”.
Daga haka ya fice abinsa dan baiso ta ƙara tofa komai…………….✍
[ad_2]