MAKAUNIYAR KADDARA 56

kana buƙata zan iya baka number wani likita ƙwararre akan wannan fanin kawai dazai maka ƙarin bayani sosai, zaima iya nuna maka yanda akeyin komai insha
ALLAHU”.
Murmushi AK yayi da ɗaukar ruwa yasha. “Ai ko haka aka tsaya ma na gamsu Khalipha, na kumaji a raina baka wasa da karatunka, tunda gashi tun a yanzu
mun faracin tagomashinsa, inaga nan gaba kuma ka zama cikakke. ALLAH yay maka albarka ya ƙara ƙwaƙwalwa. Akwai wasu bayanai da nakeson sake tattarawa, dana
kammala zan baka wani aiki insha ALLAHU”.
“To yayanmu ngd sosai. ALLAH ya ƙara girma da nasarorin rayuwa”.
Murmushi kawai AK yayi da amsawa da amin akan laɓɓansa. Daga haka suka koma wata hirar kuma.
_______★
Sam su Zinneerah basusan da dawowar AK gidanba, tunda su Jamal suka ƙaru sai sukai zaman sake babin sabuwar shafta, sun dai san Khalipha na nan, tunda
bayan mai gyaran ya kammala ya sanar mata zai jira dawowar Yayan nasu.
Kiran sallar la’asar ya saka Jamal da Nawaf fitowa massallaci, shine suka haɗu da Khalipha da yayan nasu. Sunata faman sinne kawuna da tunanin zai
musu faɗa sai sukaji tsit, tundama ya amsa gaisuwarsu yay gaba bai sake cewa dasu uffanba har aka idar da salla suka fito.
Khalipha ne ya dubesu lokacin da suke shigowa harabar gidan. “Guys kuje ku tattaro waɗan can sauran yan-yan ɗin muwuce gida haka nan”.
Cikin marairaicewa Jamal yace, “Wayyo Yaya Khalipha Please sai anyi magriba zamu dawo fa, can gidan duk mutane, ni wlhy suna takuramin”.
“Ƙaniyarkace mutanen, dalla jeka kirasu mu wuce. Mutanen da kake magana ba duk sun kama gabansu ba, ga aiki can a gida kunzo nan kun zauna”.
Baki cike da iska Jamal ya wuce ciki kiransu Meenal. Duk wannan abin dake faruwa AK na ɗan gefensu kaɗan yana waya, sarai kuma yanajinsu amma sai
baima nuna kunnensa na akansun ba. Ba’afi mintuna uku ba sai gasu sun fito harda Zinneerah da fuskarta ke a ƙwaɓe.
Sam bata lura da AK ba, dan haka kai tsaye ta isa gaban Khalipha. “Wayyo Yah Khalipha dan ALLAH ka barsu, hirafa suke tayani”. Ta ƙare maganar hawaye
na sakko mata a kumatu.
Tausayi ta bashi dan yasan shaƙuwa da sabon dake a tsakaninsu, sannan kuma akwai rashin sabon nan ɗin tattare da ita. Balle Yayan nasu daba sakewa ya
iya da jama’a ba sai yaso dan kansa.
Murya ya kwantar sosai cikin lallashi yace, “Haba auta ai abun sai ya zama rashin hankali kuma. Kiyi haƙuri gobe idan ALLAH ya kaimu sai su dawo ku
ɗora daga inda kuka tsaya tunda ku shiririta bata ƙare muku. Kinga yanzu aikine a gidan can sosai, su kuma da zasu taimaka sunzo nan sun zauna aikin yama su
Ni’ima yawa.”
“Amma Yah Khalipha zasu koma ai, kaga yanzu suna tayani hira”.
“Indai hirace karki damu ga Yayanmu nan a gida ai zai tayaki”.
Batare da tunanin yana a wajanba tace, “Tab, Yayanmu ne zaiyi hira? Wanda ko dariya yana shekara baiyita ba ma……”
Karaf Bahijja ta katseta da faɗin, “Baya hira, amma ya iya soyayya, nifa nan gidan zanma dawo da zama yasin nasha kallo, dan na taɓa ganin wata
zazzafan soyayyar Yayanmu da aunty Farah wani zuwa da sukayi na rakasu gidan Uncle Yusif, ku kunga abu, wlhy Zinneerah zaki sh…….”
“K!”.
Khalipha da abin ya ishesa yay saurin katseta. tun fara sakin zancen nata yake mata alamar tai shiri amma taƙi fahimta. Suko su Jamal hannu suka ɗora bisa
kawunansu suna zaro ido da bubbuga bakinsu na mata alamar tai shiru, amma ina yarinyarnan kamar an kunna mata batir. Tsawan da Khalipha yay mata kuwa baki
ta turo, cikin ƙunƙuni tace, “Yah Khalipha labarifa nake baku dan kuma ku koya irin ƙwarewan Yayanmu kuma ku dinga yi”.
Kai kawai Khalipha ya girgiza yana ƙoƙarin danne dariyar dake neman kufce masa ganin Yayan nasu ya nufo inda suke yana saka wayarsa aljihu alamar ya
gama.
Gyaran murya ya ɗanyi, ba Bahijja mai bada lecture ba hatta Zinneerah sai da hanjin cikinta ya wantsala suka juyo a firgice su uku harda meenal dan
sune dai suka juyama inda yake baya.
Kafinma yace dasu wani abu Bahijja da Meenal sun kwasa da gudu hanyar gate, Jamal da Nawaf duk da sunsan dashi a wajen suma dai rufa musu baya sukayi
dan hanyar lafiya a bita da shekara.
A bazata dariya ta suɓucema Zinneerah duk da itama fa a tsoracen take. Amma yanda su Jamal suka dafe ƙeya dasu Bahijja ya bata matuƙar dariya.
Khalipha da shima dariyar yake dannewa tana kufcewa ya afka mota yana faɗin, “Mu kwana lafiya Yayanmu”.
Kai kawai ya jinjina masa tashi fuskar babu ko ɗigon murmushi ammafa a ransa dariya yake ɗan rainin wayon????. Dan duk dauriyarka dolene abinda su
Meenal sukai ya baka dariya. Maigadi kansa dariya yakeyi dan har bangajesa sukai wajen gudu.
Ganin Khalipha zai wuce Zinneerah ta shirya nata gudun itama amma tana ɗaga ƙafa zata fece taji an cafko mata hannu. Gaba ɗaya ta rikice, dariyar data
rage a saman fuskarta ta ɓace ɓat. Baya ya dawo da ita gabansa yana kallonta da birkitattun idanunsa dake neman sakata sakin fitsari dan fuskar ta kuma
tsukewa tamau. Shi dai Khalipha motarsa ya harba yana dariyar ƙeta, dan yasan dai Bahijja ta kunno wuta. Kuma gaskiya ta faɗa indai soyayya ce kam Yah
Abdul-Mutallab ba’a magana, shi da yake rayuwa a gidansu yake shan kallo.
Cikin tsagwaron marairaicewa Zinneerah da idanunta ke tara ƙwalla tace, “Yayanmu wlhy bance komaiba, ALLAH Bahijja ce ka tambayi Yah Khalipha kuma.
Uffan baice mataba, sai jawota da yay a hankali ta faɗa saman jikinsa, rawa jikinta ya fara, batare da yabi takanta ba ya ɗauketa cak a bazata. Babu shiri
ta cusa kanta a ƙirjinsa dason sauka amma tama kasa motsawa. Koda suka iso ƙofar falon da ƙafa ya tura, hakama da sukaje ta sashensa da ƙafa ya tura, duk
yanda take zame-zame bai direta a ko inaba sai falonsa.
Tanajin ya ajiyeta ta ɗago fuskarta daga jikinsa dajan jikinta dake ɓarin tsoro baya dan catake ko duka zataci, duk da dai bata taɓaji a tarihi ko
labarinsa ya taɓa dukan kowaba a gidan nasu, barsa dai da barazana da mazurai, hana rantsuwa marin da yayma matarsa a london sanda ta shaƙeta, shima ba wani
lura tai da ƙyauba ranar dan a firgice take sai da su Meenal suka bata labari.
Baya ta dinga ja tana girgiza kanta. “Yayanmu ALLAH bance komaiba, ka tambayi Yah Khalipha”.
Hannayensa ya zuba a aljihu duka biyu yana binta a baya fuska a tamke, sai wani lumshe idanu da buɗewa yakeyi akan lips ɗinda dake motsawa a hankali da
yanayin tsoron daya bayyana ƙarara a fuskarta. Tana tafiya yana binta sai ji tai ta dangane da bango, juyawa tai a firgice ta kalli bayanta, ganin dai da