MAKAUNIYAR KADDARA 56

gaske tazo ƙarshe hankalinta ya ƙara tashi, ta dubesa da saurin yin ƙasa zata durƙushe ya riƙo hannunta.
“Yayanmu wl…..”
“Shiiii!!!..”
Ya faɗa a hankali yana saka idanunsa da suka canja launi cikin nata, tare da saka duka hannayensa a bangon ya dogareta yanda babu damar kuɓuta kenan.
Gashi ya hana kuka dole kuma ta haɗiyesa, sai dai zuciyarta kamar zata faso ƙirjinta ta fito.
A wani irin ƙasa da murya sosai ya fara magana idanunsa cikin nata da takeson janyewa ya hana. “Dama idan kuka zauna gulman mutane kawai kuka iya
ko?”.
“Wlhy a’a Yayanmu, bama gulmar kowa ka tambayi Granny”.
“Ni yanzu danaji ana tawa fa?”.
“Y…y…Yayanmu ba gulm…ma bane fa?”.
“To miye sunansa?”
Shiru tai dan batasan mi kuma zatace ba itakam. Hakan datai ya sashi juya idanunsa yana sauke hannunsa ɗaya dake dafe da bango ya maida cikin aljihu. Yace,
“Anyhow zan fara hukuntaki kafin ita mai baku lecture ɗin na kamata da sauran ɗaliban nata”.
“Wayyo Yayanmu, wayyo Yayanmu”. Zinneerah ta faɗada iyakar marairaicewar data saka AK cije lip ɗinsa, yana binta da wani irin ƙasalallen kallon daya
saka hawayen ƙaryarta ɗaukewa ɗaf ta shiga mar mar da idanu zuciyarta na harbawa da sauri-sauri……….✍
[ad_2]