MAKAUNIYAR KADDARA 57

Page 57
………..“Nine kuma bana dariya sai shekara-shekara ko?”.
“A’a wlhy Yayanmu bakai nake nufi ba, wani ne acan Danya”. Zinneerah ta faɗa tana duban gefen daya janye hannunsa. Hakan yayi dai-dai da wayarsa ta
fara tsuwwa. Aljihunsa ya kalla da ƙoƙarin zira hannunsa zai ɗakko, ‘Alhmdllh’. Zinneerah ta faɗa a zuciyarta tana kwasa da gudu.
Duk yanda AK yaso danne dariya a yanzu kam ya kasa, dole yay murmushi har haƙoransa na fitowa tare da girgiza kansa kawai.
yace, ‘Zan kamaki har inda zakije ɗin ai” daga haka ya kai wayarsa kunnensa dan Hajiya iya ce.
Zinneerah kam bata tsaya a ko inaba sai bedroom ɗinta nacan ciki, ta murzawa ƙofar key tana sauke numfashi da faɗin, ‘ALLAH na godema daka kuɓutar
dani, Bahijja taso jamin salalan tsiya yau, dan ƙila zaneni yay niyyar yi ma’.
Sai kuma ta kwashe da dariya saboda tuno su Bahijja, inama tanada waya yau data kirasu taji yanda aka kwashe. Bata taɓajin takaicin rashin wayarta
irin yau ba, harta kaita da zama tunanin yanda wayar ta ɓata abin kamar almara
★★★
Tun abinda ya faru Zinneerah da AK basu sake ganin junaba har akai sallar magriba. Sai lokacin ta fito daga ɗakinta ta duba dining ɗin. Tasha mamaki ganin
anci abinci data ajiye. Aranta take tunanin ashe ya shigo yaci abincin. Wajen ta tattara tare da falon, ta saka turaren wuta sannan ta koma ɗaki tai wanka.
Tana fitowa sallar isha’i ta gabatar, bayan ta idar tai zamar gyara jikinta ranta fal tunanin mmn sadiq dasu Abdull, harma da Little da rabota dashi tun
randa zata wuce danya. Tana kewarsa sosai harma da ƴan danya ɗin, yanzu da tanada waya ai da ta kira taji yanda suka sauka lafiya da jikin Tinene kuma.
Tsaki ta ɗan ja ranta duk babu daɗi. Doguwar riga kawai ta saka yanda zata sake, tana ɗaure gashinta data taje taji an turo ƙofar ɗakin.
Juyowa tai a hankali tana duban ƙofar aɗan rikice, wanda tayi zaton dai shine, yana sanye cikin wando jeans baƙi da baƙar t-shirt, sosai kayan sukai
masa ƙyau duk da alamu sun nuna badan kwalliya ya sakaba.
Ganin yanda idanunsa ke a kanta yasata yin ƙasa da nata, ya ƙaraso cikin ɗakin kansa tsaye da tafiyarnan tasa daba garaje, ga fuskar kuma babu
alamar fara’a kamar ko yaushe, amma hakan bai hana ƙyawunsa da kwarjininsa fita ba a bayyane.
“Barka da dare”.
Ta faɗa kanta a ƙasa da ƙoƙarin jan gyalen jallabiyar zata yane kanta duk da bata kamla ɗaure gashin ba. AK da tunda ya shigo idanun nasa ke akan gashin
nata ya janyesu yana zama bakin gadon. Batare da yayi mata magana ba ya miƙa mata wayarsa.
Amsa tayi duk da bata fahimci mi yake nufi ba, sai dai ganin sunan Granny da alamar tana online yasata kai wayar kunnenta tai sallama murya a
marairaice.
Dariya Granny tayi daga can da cewar, “Inno irin wannan marairaicewa haka?”.
“Granny nayi kewarki ne”.
“Nima haka Inno, shiyyasa nace Moddibo ya banike na karajin muryarki kafin na kwanta”.
A take hawaye suka ziraro a kumatun Zinneerah, muryarta ta fara rawa alamun kuka. Kai kawai AK ya ɗan girgiza da mikewa tsaye, batare da yace komaiba
ya zare wayar daka kunnenta….
Da sauri ta kallesa dai-dai yana maida wayar kunnensa. Idanun nasa ya ɗan juya mata da faɗin, “Daga gaisuwa kuma sai ki samin ita kuka Granny? To an
fasa gaisuwar dake sai da safe”.
Da alama wata baƙar maganar ta faɗa masa daga can, dan janye wayar yay yana murmushi. Batare da yacema Zinneerah dake sharar ƙwalla uffanba ya raɓata
ya wuce inda ta ajiye masa system ɗinsa daya bari a ɗakin jiya. Ɗauka yay tare da nufar ƙofa yana faɗin, “Ki kawomin lipton”.
Baki ta kuma tunzurawa tana matso hawaye da bin bayansa da kallo harya fice, babu yanda ta iya dole bayan ta gama kukanta ta share hawayen da ɗaukar
turare ta ƙara a jikinta, hardasu fesa much freshener kamar yanda Hajiya Falmata ta koya mata, ta ɗauka wani ɗan kwalban turare da batasan kona minene ba ta
shafa a bayan kinnenta da wuyanta, kamar yanda Hajiya falmatan ta sanar mata ta ringa shafa shi duk dare idan tai wanka, ta kuma ƙara da khumra mai shegen
daɗi da narkar da mai shaƙa.
Daga haka ta ɗau hijjab mai hannu jaa ta saka sannan ta fito. Kitchen ta nufa ta ɗaura masa lipton ɗin da ganyen shayin da hajiya Falmata ta bata
shima, rashin wayonta yasa batai tunanin ko ganyen shayin na wani abu baneba daban. A wani butar shayi mai azabar ƙyau daya ɗauka hankalinta ta juye tare da
kananun kofunansa tasa biyu, sai ɗan bowl ɗin data zuba suger shima ta ɗora da tea spoon guda ɗaya ta ɗauka tray ɗin tana addu’ar ALLAH yasa tayi komai
dai-dai.
Yana zaune a doguwar kujera ƙafarsa a miƙe yasa filo da ɗaura lap-top ɗinsa saman filon. Koda tai sallama bai dagoba amma ya amsa mata a saman
laɓɓa yana cigaba da aikinsa.
Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke idanunta, a centre table ɗin tsakkiyar falon ta ɗaura ƙaramin tray ɗin da jawosa kusa da shi tace, “Yayanmu gashi”.
Ɗan ɗagowa yay yayi mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa, a taƙaice yace, “Zuba”.
Kanta ta jinjina masa kawai ta tsugunna gaban table ɗin tana ƙoƙarin fara zubawar, yanda hijjab ɗinta yay ɗan bula lokacin da take kaiwa tsugunne ya
bama hancinsa damar shaƙo fitinannun ƙamshin turarurrukan data sakama jikinta, duk da tun shigowarta ya jisu, sai haka datai ya ƙara ƙarfinsu fiye da farko
a cikin hancinsa.
Wani irin harbawa zuciyarsa tayi, har baisan yatsunsa sun kauce wajen tafa saƙon shirme ba a system ɗin. Ya lumshe idanu ya sake buɗewa a kanta yana
ɗan cizar lip dinsa na ƙasa.
Zinneerah da batasan mi yake cikiba ta miƙo masa ɗan mitsilin tea cup ɗin irin na larabawa bayan tasa suga ɗaya dan tasan yanda yake so tunda yasha
sata aikin sanda suna gida, tsaf ta gama haddace adadin da yake so.
Idanunsa da suka canja launi lokaci guda ya zuba mata, dai-dai yana amsar shayin muryarsa a ƙasan maƙoshi yace, “Cire wannan hijjab ɗin banaso”.
Mamakin maganar tasa yasata ware idanu sosai tana kallonsa. Sai dai yanda fuskarsa ke a ɗinke ya sata yin ƙasa da kanta ta hau ƙoƙarin cirewa tana
haɗiye abinda ya tokare mata maƙoshi, dan duk da doguwar riga ce a jikinta tsananin kunyar zama take a gabansa a haka saboda santsin rigar yasa ta kwanta
mata a jiki ta lafe, musamman da yazam ita da kanta ta rage faɗin rigar tun suna gida ita dasu Bahijja.
Hannu ya miƙa mata alamar ta bashi, dole ta miƙa masa, kusa dashi ya ajiye hijjab ɗin dan son tabbatar da shike ƙamshin ko ita?.
“Zauna”. Ya faɗa yana matsar da ƙafafunsa. Yanzun kam kasa haƙuri tayi sai da tace, “Yayanmu zanje na kwanta inajin barci”.
“Nima ba gadin gidan zanyiba ai”. Ya bata amsa a daƙile.
Tashi tai tsam ta zauna inda ya nuna matan har jikinta na neman hayemasa ƙafafu, tai saurin muskutawa kanta a ƙasa.
Idanu ya tsira mata yana kurɓar shayin kaɗan-kaɗan saboda zafinsa. Amma dai haka yafi bukatarsa musamman wannan da yay masa matuƙar daɗi, ga wani