MAKAUNIYAR KADDARA 57

irin ƙamshi mai daɗi dake fita a cikinsa.
Ya fahimci ta matuƙar ƙwarewa da iya cuɗa hannunta cikin na juna idan tana waje a takure ko makamancin hakan. Ya danyi gyaran murya nason gusar da
shirun nasu. Ɗagowa tai ta kallesa.
Idanunsa a cikin nata yace, “Kin kira su baba ne? Kinji yanda su gwaggo sukaje gida lafiya”.
Ya sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi, atake idanunta suka ciko da ƙwalla ta girgiza masa kai. “A’a ai bani da waya ta ɓata”.
“Ɓata fa? A ina kenan?”.
Da damuwa sosai a fuskarta tace, “A can gida, tun lokacin da Granny bata da lafiya zaku wuce london”.
Cikin ɗan taɓe baki yace, “Kin dai jefashi wani waje”.
“A’a wlhy Yayanmu, nifa ina gama waya da Mama a ranar daga ajiyewa naje na tarosu na nemeta na rasa. har yanzu kuma ban ganshiba, kuma ko ina su Meenal
sun tayani na duba”.
“Uhm to wani ya sace kenan”.
Ya bata amsa cike da basarwa.
Itako tace, “Amma kuma a gidan nan wazai saci waya?”.
Wani ɗan murmushin daya bata mamaki taga yayi yana lunshe idanunsa. Cikin basar da maganar yace, “Ganyen shayin nan yanada daɗi waya baki?”.
Badan taso barin waccan maganarba tace, “Hajiya Falmata”.
“Wacece ita?”.
“Nima sai kwanan nan na santa suna mutuncine da Granny”.
“Uhm! Itace ta baki wannan turaren mai ƙamshi haka?”. Ya faɗa murya a shaƙe dan shayin da yasha ya fara aikinsa.
Rasa amsar da zata bashi tayi, sai ta ɗan jinjina kanta kawai.
“Baki da baki ne?”.
“A’a kayi haƙuri itace ta haɗa, khumrah ne”.
Komai bai sake faɗaba ya sauke lap-top ɗin dan aikin kam bazai iya cigabuwaba, ƙafafunsa ya zaro daga kusa da ita ya ajiye ɗaya a ƙasa ya tanƙwashe
ɗayar, sake ɗaukar butan shayin yayi ya tsiyaya dasa suga ɗaya a ciki ya motsa. Cigaba da shan abinsa yayi da maida hankalinsa ga television. Itama gyara
zamansa da yayi ya sakata jin ɗan sanyi ta koma kallon television ɗin da satar kallonsa. dan ya dage sai ɗora shayin yake hankali kwance. Daya shanye yake
karawa, tanata lissafi sai da yasha kusa cups bakwai duk da dai ɗan mitsitsine kofin.
Sai da aka kammala labaran da suke kallo ya miƙe, batare da yayi mata magana ba ya fice gaba ɗaya a sashen har tana mamakin ina zaije? Bata da mai
bata amsa dan haka ta ƙudiri aniyar zaman jiransa ya dawo ita dai taje ta kwanta ta farajin barci.
Shiko daya fita kai tsaye sashenta ya nufa, kitchen ya fara shiga ya kaso wutar can ya rufosa. ta Dining ma ya kashe tare da leƙa bedrooms ɗin dake a
falon duk yaga akashe sannan ya nufi nacan ciki da take amfani da shi.
Akwatin kayanta ya buɗe, duk da shi ba mutum bane mai buƙatar matarsa tasa kayan barci idan zasu kwanta tare ba, yafi buƙatar tazo masa a natural
ɗinta, hakan bai hanashi ɗauka mata suba. Sai dai yau ba kamar jiyaba sai da ya zaɓo dai-dai da ra’ayinsa. Gaban Mirror ɗinta yaje nanma ya shiga shinshina
turarurrukan wajen kamar mai neman wani daban. Sai dai abin mamaki ya kasa tantance wanda yake buƙatar jin, har takai ya fara buɗe kwalaben khumra dake
wajen kusan kala shidda dan bama a kawo mata sauranba tukunna. Ya ɗan samu wasu a ciki, harya ɗauka biyu sai idonsa ya sauka akan kananun ƙwalabe dake cikin
wani haɗaɗɗen kwandon saƙa na kaba da aka zubasu ciki kusan kala goma nanma. Murmushi ya danyi dan shi mutum ne mai son ƙamshi, ƙamshi yana ɗaya daga cikin
abinda Farah tai galaba a kansa kenan dan itama gwanace wajen baza turare. Nanma shinshinawa ya ringayi ɗaya bayan ɗaya, sai dai ya kasa tantance wanda yafi
daɗi da wanda yaji a jikinta. Sai ma neman rikita masa lissafi sukeyi. Nanma biyu ya zaɓa a ciki ya fice bayan ya kashe komai. falukanma duk kashe komai
yayi ya rufe sashen baki ɗaya ya nufi nasa.
Zinneerah da har ta gaji da jiran dawowarsa ta jingina da makarin kujera tana lumshe idanu ta buɗesu a hankali jin sallamarsa. Bataga mike hannunsaba
dan kai tsaye bedroom ɗinsa ya nufa. Zamanta ta gyara da ɗaukar hijjab ɗinta ta riƙe a hannu gudun kar tai laifi.
Babu jimawa kuwa sai gashi ya fito, batare da yay mata magana ba ya ɗauka remote ɗin tv ya kashe tare da nufar fridge, yana juyowa ɗauke da fura a hannu
tana miƙewa. Fuskarta a marairaice tace, “Yayanmu zanje na kwanta barci nakeji”.
Baiyi maganaba sai da ya karaso, ya ajiye roban furan da kamo hannunta ya zaunar. “Zauna kisha wannan sai kije ki kwanta”.
Cikin langaɓe kai tace, “ALLAH yayanmu na ƙoshi barci nakeji kawai”.
Harar daya zuba mata tasata ɗauka dan harya buɗe mata robar, cokalin dake haɗe da robar furan ta ɗauka ta fara sha a hankali tana lumshe ido dan
barci takeji, sosai furan na mata dadi sai dai barci na neman kwafsa mata. Shiko lap-top ɗinsa ya ɗauka yana ƙarasa aikin nasa.
“Yayanmu ALLAH ta isheni barci”.
Ɗan ɗagowa yay ya kalleta, yaɗan jinjina mata kai kawai yana ajiye lap-top din daya kashe gaba ɗaya. Miƙewa yay hannunsa ɗauke da remote na ac ya kashe.
Sannan ya tattara wayoyinsa da nuna mata hanyar ɗakinsa.
Sosai ta ɗan waro masa manyan idanunta dake cike da barci waje. Sai dai yanda ya tsuke fuska dole ta haɗiye abinda ke bakinta ta maida kanta ƙasa.
Sum-sum ta fara tafiya hanyar ɗakin da bata taɓa shigaba. Kasancewar ya tsaya kashe fitila ta rigasa shiga ɗakin. Da wani ni’imtaccen ƙamshi tafara cin
karo, ta ware idanunta sosai tanabin bedroom ɗin da kallo baki sake. Komai yaji masha ALLAH, white and golden kamar kaci dan ɗaukar idon mai kallo. Ga uban
sanyin ac.
Tana tsaye a wajen harya shigo bata saniba. Sai jitai kawai anyi sama da ita gaba dayanta. Sosai ta firgita sai dai babu damar yin magana. Bai direta
ko inaba sai toilet ɗinsa da komai yake a tsare kuma a tsaftace. Dan shi kansa kamshi yake na musamman.
“Kiyi alwala”. Ya faɗa kansa tsaye. Sabo da alwalar kwanciya barci yasa bataji komai a rantaba, gashi dama ko shafa’i da wutiri ma bataiba. Alwalar
ta ɗaura yana kallonta cike da nazari, da alama yana tabbatar da ingancinta a fannin addinine ne. Sai da ta kammala shima ya ɗaura tasa suka fito tare kamar
yanda yay mata alama da ido.
Da kansa ya sa musu abin salla. Ganin yayi tsayuwar alamar jansu salla yasata kallonsa da mamaki. “Yayanmu nayi sallar isha’i”.
“Nima nayi ai”.
Shiru tai bata ƙara maganaba harya tada sallar, itama tayarwar tayi dan bin umarni shine masalaha a gareta. Sunyi salla raka’a biyu suka ɗora da shafa’i da
wutiri, sannan ya juyi ya dafa goshinta da ambaton.
اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا، وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا، وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ
Allahumma innee as-aluka khayraha wakhayra ma jabaltaha ‘alayh, wa-a’oothu bika min sharriha washarri ma jabaltaha ‘alayh.
_Ya ALLAH ina rokon Ka laherinta da alhrin da Ka dabi’antar da ita a kansa, kuma ina neman sarinka daga sharrinta da shaarrin Da ka dabi’antar da