MAKAUNIYAR KADDARA 57

ita a kansa._
Lumshe idanunta tayi tana sauraren daddaɗan muryarsa mai cike da kamun kai da nutsuwa. Bayan ya kammala ya juya da ɗaga hannayensa sama ya cigaba da
kwararo addu’oi kala-kala da harshen larabci.
Sai da suka kammala addu’ar ya juyo yana fuskantarta da ƙyau. Tambayoyin ya fara mata a fannoni daban-daban daya shafi addini, wasu ta amsa wasu tace
bata saniba dan a yanzu take kan neman ilimi, danma Alhmdllh batai wasaba akan hakan tunda ta dawo da zama kano.
Ya gamsu da yanda tayi ɗin, ya kuma karba uzirinta, daga haka ya miƙe yana magana batare daya kalletaba. “Ga kayan barci nan ki canja”.
Yana fa ɗaya yana nufi hanyar toilet. Kaɗan ya rage Zinneerah ta saki kuka amma ta dake ranta fal tsoro. Kenan anan zata kwana tare da shi yau ma?. Ta
ayyana a ranta. Sanin bata da mafita kuma baya maimaita magana, gashi batason ya fito ya sameta batai abinda yaceba yasata ƙoƙarin canja kayan. Ganin
turarrukanta tare da kayan ta mulke jikinta dasu duk da kuwa ƙamshin take dama. Tana gamawa yana fitowa ɗaure da towel jikinsa nata raɓar ruwa. Ƙasa tai
saurin yi da kanta tana gyara zaman hijjab ɗinta data ɗora saman kayan barcin. Komai baice mataba ya hau tsane jikinsa da towel ɗin daya ratayo a wuya.
Da wannan damar ta wuce toilet ɗin nasa sumi-sumi danyin brush tunda taga sabbi a toilet ɗin, dan ta tuna Hajiya Falmata tace duk rintsi karta kwanta
batai brush ba, idan da dama ma ta haɗa da much freshener, sannan ta tabbatar duk sanda zata kwanta barci tayi tsarki da ruwan ɗumi koda ace ta yini amfani
da shine.
Brush ɗin ta farayi, sannan tai fitsari dayin tsarki da ruwan ɗumi. Much fresheners ɗinsa data gani ajiye a ɗan drawer ɗin glass ɗin toilet ɗin ta
ɗauka, dan gasunan kala-kala, banana, cucumber, kai kala-kala ta fannin fruit duk gasu nan. Son da takema S…barry ya sata ɗaukarsa shi da banana ta saka
sannan ta fito cikin sanɗa, a ranta tana addu’ar ALLAH yasa ya gama shiryawa dan shiyyasama ta daɗe danta bashi dama.
Tsaye ta iskesa gaban mirror sanye da wando 3quarter iya cinya da riga mai buɗaɗen ƙirji farare tas. Yana fesa turare. Ta madubi yake kallonta harya
kammala sannan ya juyo………..✍