MAKAUNIYAR KADDARA 58

Ruwa AK ya shiga da kansa ya haɗa mata a toilet, sannan ya fito da kansa ya taimaka mata ta sauka a gadon hawaye na rige-rigen sauka mata, ganin
tafiyar tasu babu sauri yasashi ɗaukarta kawai. Ajiyar zuciya ta sauke mai haɗe da kuka, dan hakan da yay mata ba ƙaramin taimakonta yayi ba.
Koda suka shiga ba kai tsaye ya tsundumata a ruwanba, cikin dabara da lallashi yay mata. Zinneerah nada dauriya sosai, koshi ya shaida hakan dan ta
nuna masa jarumta yau duk da taci kuka, amma tun ihun farko datai lokacin isarsa gareta bata ƙara buɗe baki domin yin kwakwazo ba, sai dai hawayene kam da
suna ƙarewa yau da sun ƙare gareta. A yanzunma hawayenne kawai sai ƙanƙamesa da tayi amma ko uhum batace ba.
Hakan ya masa daɗi, dan ya tsani kwakwazo a rayuwarsa da hayaniya, yafison komai a silent kuma da nutsuwa, wannan yana ɗaya daga cikin hallayarta
data fara jan hankalinsa gareta batare da ita ta sani ba. Kanta dake kwance a ƙirjinsa ya rinƙa shafawa yana hura mata iskar bakinsa cikin kunne. Hakan ya
matuƙar shagaltar da ita har ruwan ya ratsata yanda ya kamata ya ƙara mata wani kuma. Sai da ya tabbatar taji daɗin duka jikintama ba wajen kawai ba sannan
yace mata tayi wankan.
Duk da tanajin nauyinsa ga zazzaɓi dake neman rufeta haka tabi umarninsa tayi, dan tsaye yay a kanta da alama yana son tabbatar da ingancin abinda
zatayin. Yaji daɗin ganin yanda tayi komai dai-dai, sai kawai ya ɗauka mata bathrobe ya saka mata. Zai ƙara ɗaukarta cikin dasashshiyar muryarta tace,
“Zan iya”
Baice komaiba ya matsa ya bata hanya, cikin dauriya ta fice a toilet ɗin, saida ta fita gaba ɗaya ta cije bakinta da jingina jikin bango tana maida
numfashi, tayi hutun kusan minti ɗaya sannan ta ƙarasa kaiwa gadon dake a hargitse. A ranta tace, ‘Dole ka hargitse gado dan nima an hargitsani’.
(????????wayaga mai cikuykuya an zinni????????).
Ƙarasawa tai ta fara ƙoƙarin ganin ta gyara don buƙatarta kawai takai kwance. A dai-dai nan boss ya fito yana tsane jikinsa. Ƙarasowa yay inda take
yana murmushi tausayinta fal ransa. Batare da sanin fitowar tasa ba taji an rungumeta ta baya da amshe bedsheet ɗin hannunta. “Uhm-uhm waya saki wannan
aikin?”.
Sosai tsigar jikinta ta tashi saboda yanda yay maganar a cikin kunnenta. Bai damu da amsawarta ba ya ɗauketa ya dire a saman sofa. Shi kuma ya juya
gaban gadon ya kimtsa musu shi, gabanta ya dawo ya durƙusa, tai saurin yin ƙasa da kanta saboda matsananciyar kunyarsa dake neman halakata, gashi yanzu babu
riga a jikinsa sai towel daya ɗan yafa a wuyansa ƙarami bayan wanda yake ɗaure da shi. Lallausan murmushi ya saki yana lumshe idanu da sake buɗewa akanta
lokacin da yake warware towel ɗin data naɗo gashinta dan ya tsane. Towel ɗin ya warware yana ƙara tsane mata gashin da ƙyau gudun kamuwa da mura.
“Duk zafinsa naƙuda tafisa ko?”. Ya faɗa yana zame towel ɗin daga cikin kanta.
Rashin fahimtar tanbayar tata ya sata ɗago kumburarrun idanunta ta kallesa. Ya sakar mata lallausan murmushi da ɗan jinjina kansa. Kanta ta maida
ƙasa kawai gabanta na ɗan faɗuwa da tunanin koya san itace ta haifa little ne?.
Hannunsa ya ziro ta ƙugunta, ɗayan ya ɗago haɓarta sosai suna kallon juna. Duk yanda taso janye idanunta da suka shige cikin nasa hakan ya gagara,
dan shu’umin kallon da yake mata tamkar yana zuba mata wasu sinadaraine masu matuƙar daraja da tsada, ta ɗan fara mar-mar da idanunta dake cikowa da ƙwalla.
Kansa ya girgiza mata alamar kartayi, kafin ya saki fuskar tata da matsota jikinsa ya rungumeta a haka suna sauke ajiyar zuciya a tare. “Aure
jarabawane kuma ibadace, haƙuri a cikinsa nasarace kuma daraja ce. Riƙe mutunci da kame kai martaba ce, mutuntawace ga iyaye da tarbiyyarsu. Dan duk namijin
daya sami mace a yanda yay hasashe ba ita kaɗaice ke samun kima a garesaba har iyayenta ma mutunci da kima suke ƙarawa. Kinsha wahalhalun rayuwa amma hakan
baisaki yin gaggawa ba wajen ƴanta kanki har sai da ALLAH ya iyakance miki. Daga yau ke sarauniyace a fadar Abdul-Mutallab, ki ɗauka kin mallakesa shi da
komansa. Kin bashi ƙyauta mafi daraja guda biyu da bazai manta da itaba. Kin haifamin Abdul-Mutallab, kin daɗamin da tukiycin budurci. ALLAH yayi miki
albarka. ya yalwata rayuwarki da tarin farin ciki, ya share hawayenki ya yaye damuwarki, ya ɗaga darajarki ya cigaba da kare mutuncinki fiye da yanda kika
kare nawa”.
Sosai tsoro ya kama Zinneerah jin ya ambaci haihuwar little, sai dai daɗaɗan kalamansa da batasan zai iya kwantar da kai wajen furtasu ga mace ba
suna ratsata. Ya ɗago fuskarta yana kallonta. Lumshe nata idanun tayi saboda nauyinsa da kwarninsa.
Ɗan murmusawa yay da miƙewa tsaye, ya kamo hannunta suka nufi gaban mirror batare datasan mi zaiyiba. Dan barci takeji sosai tanada tabbacin kuma
asuba ta gabato, ga zazzaɓi jikinta zau, tasan kuma yanajin zafin. Baice mata komaiba ya zaunar da ita a kujerar mirror ɗin, kanta a ƙasa harya jona
handryer dake ajiye, gashinta ya fara busar mata sannu a hankali, sannan ya tufƙe matashi da ƙyau yanda bazai takura mataba. Rigarsa ya juya ya ɗakko cikin
Wadrobe yazo ya fesheta da turare sannan ya saka mata bayan ya zame bathrobe ɗin tanata noƙe-noƙe dan kunya. Rigan ya kai mata har cinya dan haka ta saki
ajiyar zuciya. Sake kamata yay ya kai bakin gado ya zaunar, ya buɗe drawer gefen gadon ya ciro magani dan yaji zazzaɓi a jikinta. Bata yay, babu musu tasha
saboda bukatarsa da takeyi. Tana sha yana shafa kanta harta shanye ta miƙa masa ruwan.
“Good girl.”
Ya faɗa yana kamata ya kwantar, tare da ja mata bargo ya lulluɓa mata iya rabi sannan ya sumbaci goshinta da cewa “Good night”.
Kanta kawai taɗan jinjina masa tana lumshe idanu. Wahala tasa barcin ɗaukarta cikin ƙanƙanin lokaci, sai saukar numfashinta ya rinƙaji a hankali. Lip
ɗinsa ya cije yana firzar da wani irin huci mai ɗaci dan tabbas bazai bar duk mai hannu a al’amarin nanba. Matakin farko zai fara ajiye hujja ga iyayensu a
safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu, zai kuma saka bincike na kwanaki biyu zuwa uku domin tabbatarwa da kama masu hannu a ciki dumu-dumu.
Duk da shima barcin yakeji bai kwantaba, alwala yayo da saka jallabiya ya fara nafilfili dan asuba ta gabato ma, yasan idan ya kwanta zasu makarane
kawai. Zinneerah kam tasha tarin addu’oi harma da iyayenta, yana a wajen har akai sallar asuba dan bai fita massallaci ba yau bayajin ƙarfin jikinsa sam.
Badan yaso ba ya tada ita da ƙyar domin yin salla. Aiko yasha langaɓe dan sai faman lumshe idanu take, sai da ya taimaka mata zuwa toilet ɗinma tayo