MAKAUNIYAR KADDARA 58

alwala sannan. Tanako idar da salar yau babu zancen azkar ta ɓingire a wajen. Ɗagata yay cak ya maida a gadon ya kwantar shima yabi sahunta dan kansa ya
fara masa ciwo saboda barci. Cikin so da ƙauna ya rungume matarsa cikin jikinsa suka lula duniyar barci.
*_12:5pm_*
Sai ƙarfe sha biyu da mintuna biyar AK ya farka saboda kiran wayarsa da akayi, ƙaramin tsaki yaja dan barcin sam bai ishesaba. Da ƙyar ya lalubo wayar
ya buɗe ido yana kallon mai kiran. Ganin Granny ya sashi gyara kwanciya sannan yakai kunne.
“Assalamu alaiki, Granny barka da asuba”.
“Ai dama barka da dare kacemin, kujimin iya shege da ranar ALLAH kake kiramin barka da asuba. Kai ko moddibo kana lafiya yau kuwa kai da inno? An aiko
muku da abinci kusan mutum uku suna zuwa amma an ƙwanƙwasa ƙofa ko motsinku babu”.
“Oh God! Granny sai kin mana kwakwazo duniya tasan bamu tashi ba? To barci mukeyi”.
“Eh lallai ai nafaji barci kukeyi ja’iri, sai ka tashi ka buɗe ƙofa ka amsa ka koma ku cigaba da barcin”.
Murmushi ya saki da ajiye wayar yana faɗin, ‘Hajiyar matsala’. Daga haka ya ɗan leƙa fuskar Zinneerah dake barcinta hankali kwance sannan ya zare
jikinsa a hankali ya sauka a gadon. Jallabiya ya ɗauka ya ɗaura saman boxer ɗinsa ya fito.
Haneef ya samu zaune a saman motar da yazo, yana ganinsa ya duro ya nufosa ɗauke da basket. “Yayanmu barka da hantsi?”. Ya faɗa cike da girmamawa.
Amsa masa yay da kulawa yana tambayarsa jama’ar gidan.
“Kowa lafiya yake yayanmu”.
“Alhmdllh, yanzu daga nan ina zaka?”.
“Ba ko’ina zan koma gidane”.
“Okay to kabar zuwa gidan, gidan Abba zan aikeka kaje ka ɗakko min Gwaggo Maryama, sai ka biya ta gidan dasu Mammah suka sauka ka ɗakkomin Mahma. Kafin kaje
duk zan kirasu”.
Kai Haneef ya jinjina ransa fal wasiwasin lafiya kuwa?. Rashin mai basa amsa ya sashi miƙa masa basket ɗin kawai ya juya domin cika umarninsa..
Shima ciki ya koma kai tsaye sashensa. a dining ɗin falon nasa ya ajiye basket ɗin ya koma ciki. Wayarsa ya ɗauka yay zaman kiran Hajiya iya, sun ɗanyi
magana ya maida kiran ga Mahma kuma sannan ya kira Abba na gidan mmn sadiq……………✍
[ad_2]