MAKAUNIYAR KADDARA 59

Page 59
…………Koda ya dawo bedroom ɗin wanka kawai ya shiga batare daya tada Zinneerah ba. Harko ya fito ya kammala shirinsa tsaf cikin ƙananun kayan da sukai
masa matuƙar ƙyau da ƙara fidda kwarjininsa da ƙuruciya bata farkaba. Yana tsaka da saka turare ya jiyo ana danna door bell, ajiye turaren yayi ya ɗauka
wayarsa da ƙarasowa gaban gadon saitin da take kwance. Wani lallausan murmushi yake saki yana ƙarema fuskarta kallo musamman bakin daya tsuƙe. A hankali ya
ranƙwafo ya sumbaci bakin da hancinta da goshinta, yana motsa laɓɓansa a hankali wajen ambaton, “ALLAH ya albarkaci rayuwarki”.
Daga haka ya fice abinsa. Yana buɗe ƙofar da Hajiya iya da Moos’ab ya kawo yaci karo. Ta zuba masa harara da faɗin, “Shegen gida kamar na ƴan yankan
kai, sai ka danna ƙararrawa an gama yarfaka za’a buɗe maka”.
“Oh-oh daga zuwanki sai neman faɗa, yi haƙuri ni yau bana faɗa”.
“A lallai ai naga alama a goshin ka ma ja’iri mara kunya”. Hajiya iya ta faɗa tana turesa da shigowa cikin falon abinta.
Murmushi ya ɗanyi dakai hannu ya murza goshinsa. A ransa yana faɗin ‘Mi matarnan ke nufi dani?’. Bashi da mai bashi amsa dan haka yay ƙoƙarin bin
bayanta. hannunta ya riƙo ganin ta nufi sashen Zinneerah. “Kinga inda zakiyi nan madam”.
“Kai ni sakeni naje na fara ganin Inno tukunna, haka kawai ka wani tattaromu sai kace ƴaƴanka”.
“Uhm ke dama ba’ayi miki dai-dai, ai Innon taki na inda zan kaikin ko”.
“Ato muje naga abuta dan nikam ban yarda da wannan munafurcin nakaba yau Moddibo”.
Murmushi kawai yayi batare da yace mata komaiba suka nufi sashensa. Kamar jira suna isa falon saiga sallamar Haneef. Zaunar da hajiya iya yayi sannan ya
amsa da cewa “Shigo da su”.
Kasancewar dama Haneef na tare da Mahma da Gwaggo Maryama da duk hankalinsu ke tashe da wannan kira na AK ɗin sai ya matsa musu alamar su shiga. Shi
kuma ya juya.
Cikin girmamawa AK yay zaman gaishesu su duka. Cikin rashin haƙuri Hajiya Iya tace, “Mukam dai duk ka tada hankalinmu Moddibo, mike faruwa ne? Ina
Inno kuma?”.
Ɗan dubanta AK yay yana maida kansa gefe da faɗin, “Ku kwantar da hankalinku ba wani abu bane, na saku zuwa nanne domin ku zama na farko dazan fara
tabbatarmawa kafin kowama ya sani”.
Hajiya iya dake cikin jimamai tace, “To muna saurarenka, ALLAH ya jishemu alkairi”.
Da amin Mahma da Gwaggo Maryama suka amsa. AK ya gyara zamansa kansa a ƙasa dan nauyin maganar da zaiyi. “Kuyi haƙuri duk da ba magana bace wadda ya
kamata kusani, amma saboda wasu dalilai naga ya dace ku sani ku kuma zama hujja akan binciken da zan ƙarasa. Mu dukanmu nan munsan cewar Zinneerah ta haihu
a shekarun baya, kuma koda yaushe maganarta shine batasan a inda ta samo ciki ba. Wasu kan ɗauketa mara hankali, wasu na ganin tana wasa da hankalin
mutanene kawai ko rainin wayo da makamantan haka. Wasu kuma kan mata uziri da cewar ƙaddara ce ta afka mata. Tabbas ƙaddara ce, da a zahirance zamu iya
kiranta MAKAUNIYAR ƘADDARA. ALLAH shine shaidata ban taɓa taɓa ƴar kowa ba da nufin fasiƙanci. hakkane ya tada hankalina matuƙa akan Zinneerah har takai
bana iya barci, a ƴan kwanakin nan gaba ɗaya cikin shan maganin hawan jini nake saboda tashin hankali da tunanin ta hanyar da aka samar da Abdul-Mutallab,
sai da Granny ta kawo wani zance da Khalipha yayi akan dashen ciki sannan ALLAH ya haskamin hanya. A dalilin haka na cigaba da bibiyar abubuwa da dama a
ɓoye batare da sanin kowaba, har ALLAH ya tabbatar a yau nakai gaɓar da nine na farko da zan fara tabbatarma duniya lallai dashen cikin Abdul-Mutallab
akaima Zinneerah bata hanyar banza ta samoshi ba. Dan bata taɓa tarayya da namiji ba sai daren jiya. Inaji a raina ALLAH ya keɓance tane daga haihuwa da
kanta sai cs akai mata domin irin wannan ranar dazai wanketa ga kowa”.
Kallon kallo aka shigayi tsakani Mahma da Granny da Gwaggo Maryama, shi dai AK tunda ya fara bayaninsa harya ƙare bai yarda ya kallesu ba idanunsa a
ƙasa.
Cikin karfin hali Mahma ta katse tararrabin su ta hanyar kallon AK da faɗin, “Abdul-Mutallab ka sakamu a duhu nikam, kenan tayaya aka dasama baiwar
ALLAH nan gudan jininka?”.
“Wannan ne nakeson sani yanzun, amma Mahma kiyi haƙuri, inaga wannan abin ba kowa bane ya ƙullasa sai Zakiyya, Farah da Mammah, dan naji wasu zantuka
nasu da suka rikitani jiya da rana sanda nazo gidan nan, to kafin na shigo na fara samunsu a garden ne amma su basu san na jiba. Sannan idan kin lura duk
sanda akai maganar dashen cikin nan sai sun razana. Dalilina na biyu Dr Mahmud ya tabbatar min shi baiga wani alamun mai ciki tattare da Farah ba. Sannan ni
kaina idan zanyi aiki da hankalina ai ciki girma yakeyi a jikin mace, amma ace kusan 5months babu wani alamarsa a jikin Farah. Idan baki mantaba cikin farko
data samu tun yana wata uku suka matsa sai da ta tafi Morocco, bata dawo London ba sai da tai ɓari kamar yanda suka faɗa. To wannan ma a ƙiyasina tun yana
wattani ukun ta shiga damuna zataje, amma zuwan danai da Granny ya sani taka mata birki. Hujja ta biyu a labarin da Zinneerah ta bamu na zuwanta katsina
aikatau yayi kama da wadda aka yaudara saboda ƙuruciyarta, bayan an cutar da itane ta gudo batare da saninsu ba. Abinda kawai ban fahimtaba anan shine
Mammah tasan hakan kokuwa ita Zakiyya da Farah ne kawai suka sani ko itama Farah bata sani ba? Hujjata ta ƙarshe samun Zinneerah da martabarta ta ƴa mace”.
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un” Mahma dasu Granny keta ambata, hawaye suka shiga sakkoma Mahma, tasa hannu ta sharesu da faɗin, “Lallai biri zai
iyayin kama da mutum Abdul-Mutallab, dan nima kaina ina mamakin rashin tasawar cikin Farah. Sannan akwai wasu abubuwa na rashin gaskiya da zakaga suna shan
aikatawa a wani lokaci kuma, lokacin cikin farko na taɓajin wata wayarta da Adilah lokacin tana hostel a makaranta, sai dai ina shiga ta yanke wayar. Indai
kuwa hakane sun cutar da yarinyar nan matuƙa, sun ɓata mata suna, sun sakata wahala da ƙarancin shekaru. Wane irin son zuciya ne wannan? Kai kanka damu sun
cutar ai”.
Ta kare maganar tana kuka sosai. Gwaggo Maryama ma hawaye takeyi, Granny dai idanunta sunyi matuƙar yin jajur alamar shiga ƙololuwar ɓacin rai. taja
numfashi mai zafi da faɗin, “Lallai kayi haƙuri Moddibo, idan har ta kasance wannan zancen ya zama gaskiya sai nayi shari’a da uwarka da matarka. Dan wlhy
sai na bima inno kadin haƙƙinta. Yanzu abinda nakeso da kai kar kai musu maganar komai, kuma tabbas inaga Zakiyya itace hajiyar da aka kai Inno gidanta. To
karka yarda su haɗu anan gidan yanzun, dan idan suka gane itace zasu iya bin wata hanyar suga sun rufe asirinsu. Abinda nakeso dakai yanzu daganan zuwa
safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu ka aika hukuma a kama matar data kai Zinneerah aikatau katsina, itace zata kaimu ga hajiyar farko, ita kuma ta kaimu wajen