MAKAUNIYAR KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAUNIYAR KADDARA 59

wadda Zinneerah ta faɗa mana tata jerangiya da ita asibiti, na tabbatar zamu kamo bakin zaren insha ALLAHU.”
         Duk da kalaman cewar sai tayi shari’a dasu Mammah ya bashi tsoro dan yasan Granny akan tsayawa wanda aka zalinta hakan bai hanashi ɗaga mata kai ba

cikin girmamawa yace, “An gama insha ALLAH, dan yanzu hakama zancen da nake miki tana police station tare da Khalipha. Tun da safe yaje Dayan akanta, ya

tatar tana katsina, shine ya zarce can har inda take bisa taimakon wani bawan ALLAH ɗan nan Danya ɗin. Dan da nace a fara kamamin matar baba sai Khalipha ya

bani haƙuri akan a barta kodan darajarsa dan yama tarar itama bata da lafiya. Mu kama matar dai kawai tunda ta hanyartane kawai za’a iya bin diddigin abun”.
       Mahma tace, “Alhmdllh hakan da kukai shine dai-dai, yanzu yaya akai mi matar tace?”.
     “Mahma ba’akai ga tambayarta komai ba, dan inaga ko mintuna goma basuyi da isowaba ma, ina gama waya daku ya kirani yake sanarmin ya dawo harda matarma

tana station yanzu haka”.
         Gwaggo Maryama dai ta kasa tofa komai, sai hawaye taketa faman zirararwa. Hajiya iya tace, “Kabeer ya san duk wannan?”.
      “A’a ban faɗa masa ba”.
“To ya kamata ya sani dagashi har Ahmad da Abubakar (Abba mijin maman sadiq) da baban ita Zinneerah, dan babbar maganace wannan data wuce yinta iya mu

kaɗai”.
       “Babu damuwa Granny, dama ai dole zasu sani, dama munason mu kammala gano inda mutanen suke tukkuna sai na sanar dasu. Amma tunda kinga ya dace su

sani tun yanzu shikenan”.
         Mammah ta buɗe baki zatai magana kenan sai ga Zinneerah ta fito tana tafiya a hankali batare da tasan da zamansu a falonba. Ita cama take AK ɗin

baya gidan, dan tun ɗazu ta tashi, cikin ƙarfin hali ta gyara masa ɗakin da wanke toilet, yanzuma ta fito ɗaukar kayan sharane.
       Tun fitowarta ƙamshin turarenta ya isar masa hanci, dan haka ya waiwayo domin tabbatarwa. sai dai yayi dai-dai da suma duk suka ganta ɗin.
     Sai dai babu wanda ya iya cewa komai a cikinsu harta iso kusan tsakkiyar falon, turus taja ta tsaya gabanta na faɗuwa ganin yanda suke mata kallon

ƙurulla su duka. Sai duk ta daburce dan gani take kamar duk sun san miya faru da ita a daren jiya. Da sauri ta juya zata koma inda ta fito Hajiya Iya tace,

“Inno ba gaisuwa?”.
      Matse idanunta tai da cije lips ɗinta waje guda tamkar zata nutse dan kunya. Musamman daya kasance cike da tsokana hajiya iya tai maganar.
      AK dake binta da kallo ƙasa-ƙasa yace, “Granny ke baki iya gani ki ƙyale?”.
         Dariya duk suka ɗanyi, dai-dai Zinneerah na isowa inda suken kanta a ƙasa. Can jikin kujera ta lafe tana gaishesu, saika rantse wasu baƙin tane da

bata saniba ko take matuƙar jin kunyar haɗuwa dasu. Yanda tayi ɗin ya bama AK dariya matuƙa amma ya gimtse baiyiba.
      “Oh kajimin ja’ira wa kikema wannan lafe-lafen anan to? Koda yake sai dai idan surukarki Zaliha”. hajiya iya ta faɗa tana nuna Mahma dake kallon

Zinneerah ɗin da murmushi a fuskarta tanajin tausayi da ƙaunar yarinyar har cikin bargonta. Itace ta tashi tsam ta kamo hannun Zinneerah data kasa tasowa

duk da maganar da Granny tayi.
      “Haba ɗiyata minene najin kunya, mufa nan duk iyayenki ne, ga kuma kaka nan. ALLAH yay miki albarka kinji, ya sakanka miki da alkairi mai yawa ta inda

bakiyi zatoba. ALLAH ya tsare gabanki da bayanki ya ƙara ɗaga darajarki a wajen mijinki”.
      Babu kunya AK yabi sahun ƴan amsawa da amin, sai dai shi a saman laɓɓa yayi saɓanin su hajiya iya da sukai a fili. Ita dai Zinneerah ta kasa kallonsu

koda sau ɗaya dan jitake kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki. Dama kuma ga miskilanci data ƙware kuma ta haddace duk da bataima Hajiya iya yau dai itama ta

shafeta kam.
     Duk yanda sukaso ta sake hakan ya gagara, hakan yasa hajiya iya cewar, “Tunda yanzu baƙya yayina Inno tashi kije abinki, ai gobema rana ce”.
     Tsam ta mike a tunaninsu tafiyar zatai, sai sukaga ta nufi hajiya iya. Tana zuwa a jiki ta faɗa mata hawaye na gangaro mata.
      “Oh ashe moddibo ne ya fara koya miki gulmarsa ta basarwa kina yina”. Hajiya iya ta faɗa tana shafa kan Zinneerah ranta fes da so da kaunarta data

kara ninkuwa a ranta, ga ɗunbin tausayinta kuma.
    Albarka suka dinga saka mata AK na tayata da amsawa. Daga ƙarshe hajiya iya ta sata sake basu labarin abinda ya faru a zuwanta katsina. Suka kuma dora

mata da ƴan tambayoyin abinda ya shige musu duhu musamman Mahma da hausar tata ba cika yay ba.
         Sallamar Zinneerah sukai su kuma suka cigaba da tattarawa, da wannan damar ta samu kuɓuta ta koma ɗakinsa. Barin batun shara tai ta shige toilet

tai wanka da sake gasa jikinta da ƙyau, yunwa takeji sosai ga jikinta da takeji fayau, sai bakinta dake ɗaci amma babu zazzaɓin. Sai dai illahirin gaɓɓanta

babu inda baya mata ciwo. Taji daɗin ruwan zafin sosai. Dan sai da ta tabbatar ko wace gaɓa tata ta gamsu kafin tai wanka ta fito ɗaure da towel ɗinsa daya

tsaya mata iya cinya. Batai tunanin samunsa a ɗakinba tunda tasan yana tare da baƙi, sai dai kuma tana fitowa tai turus saboda cin karo datai dashi zaune a

bakin gado yana waya.
       Da baya-baya ta dinga jan ƙafarta zata koma AK ya miƙe yana binta da wani shu’umin kallo daya nema harmutsa hanjin cikinta dan tsoro, dan ita dai

harga ALLAH wani irin tsoronsane ya sake tasiri a ranta bayan matsananciyar kunyarsa da bata taɓa ji ga wani ba. Ganin ya taso ɗin ya sata kara sauri, sai

dai babu nasara dan taku baifi huɗu yayba ya cafkota. Gaba ɗayanta ya jawo jikinsa yana faɗin, “Okay Baffah sai nazo gidan zuwa anjima ɗin”.
    Daga haka ya ajiye wayar a ƴar drawer ɗin wajen da suke gab da ita.
       “Anya wannan jikan na Granny zatai jarumta?”.
    Ya faɗa cikin wani irin kasalalliyar murya dai-dai yana sa kansa a wuyanta. Duk da wanka tayo hakan bai hana tasirin fitar kamshin mayun khurah ɗinta

ba. Ya ƙara tura hancinsa cikin wuyan duk da laimar ruwan dake naso a jikinta. Tare da zagayo duka hannayensa akan cikinta.
      Cikin rawar murya kamar mai shirin fasa kuka tace, “Yayanmu su Granny”.
         “Su Granny mi? Ba suna falo ba muko muna nan abunmu a ɗakin sirrinmu”.
         “Amma zasu ce…..”
Ta kasa ƙarawa saboda nauyin maganar.
       Yana cigaba da shin-shinar wuyan nata dake tada mata tsigar jiki yace, “Zasuce ina lalube amaryana?. To ai suma sunsan tunda suka bani komaima zanyi

baby girl”.
       Zinneerah da kunya ke neman kasheta da mamakinsa, tai saurin cewa “Nifa ba hakaba Yayanmu”.
      “To yaya ne?”. Ya faɗa yana ɗagowa da birkitota suna fuskantar juna. Kafafu ta shiga matsewa saboda kunyar cinyoyinta dake waje. Yanda take ɗinne ya

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button