MAKAUNIYAR KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAUNIYAR KADDARA 59

sashi kallon cinyoyin, idanu ya ɗan lumshe da sake buɗesu a kansu, kafin ya cije lip ɗinsa muryarsa na canja amo yace, “Karfa kisa nai miki wani sabon

aika-aikan ALLAH. Muje ki shirya ga abinci har 2 tana neman yi. Kinyi salla ko?”.
          Kanta a ƙasa ta daga masa kawai.
      “Magana da baki”.
Dole ta buɗe baki tace, “Eh nayi tunma dana tashi naga lokaci yayi”.
     “Good. kije ki shirya to, ko na shiryaki ne?”.
       Babu shiri ta waro masa idanunta da har yau ke a ɗan kumbure. Shima waro mata nasa yayi sosai. Hakan sai ya sata jin kunya tai saurin saka tafukan

hannaunta ta rufe fuska murmushi na suɓuce mata.
        Wannan salon nata na nuna yawan jin kunya na kayatar dashi, dan haka ya rungumeta gaba ɗaya a jikinsa yana faɗin, “Ina son wannan salon naki baby.

Da gaske fa kina neman shigama Farah hanci, idan kuma ta tashi fyatoki zakiji jiki”.
     Gaban Zinneerah ne ya faɗi dan itakam sai an amfaci sunan aunty Farah take tunawa da ita, tare da tuna cewa Yay Abdull-Mutallab bafa nata bane ita

kaɗai, akwai wadda ta fita tsananin sonsa da kishinsa, komai kuma zata iya aikatawa akansa. lallai tana cikin lukutin yanayi duk randa aunty Farah tazo

Nigeria (dan itafa batasan suna nan ba har Mammah).
      Ganin yanda ta koma saboda ambaton Farah da yayi sai ya ɗauketa cak domin gusar mata da tunanin, saman gadon ya ɗorata yana ƙoƙarin kwance towel ɗin

jikin nata ta riƙe gam idanunta na firfitowa waje da jera masa roƙon haƙuri jikinta har rawa yake.
     Duk yanda yaso ya danne sai ya kasa sai da ya dara. Ya ɗan dungure mata kai da faɗin, “Matsoraciya kawai. Tashi ki shirya kici abinci inason fita”.
     Yana gama faɗa ya nufi hanyar fita dan ya bata damar da zata kimtsa tunda ya fahimci a takure take matuƙa.

     Koda ya fita ɗakinta ya nufa, babu jimawa sai gashi da kayanta ya ɗakko mata. Less ne zani da riga kalar milk da kwalliyar coffee. Sai B&F ɗinta daya

tuno masa randa ya far ganinta a gidan Granny. Haka kawai ya shiga sakin murmushi shi kaɗai tun a ɗakinta. Tana gyar gashinta ya shigo, ganin duk ta daburce

sai baiyi magana ba ya ajiye mata kayan kawai a gado ya fice abinsa zuwa falo.
        Ajiyar zuciya ta sauke tare da juyowa ta kalla kayan nata. Har cikin ranta tanajin daɗin wannan kulawar tasa na yimata hidima batare da duba cewar

ya girme mataba. Sannan inda wani ya bata labarin zata iya samunsa haka da sauƙin kai bazata yardaba. Musamman idan tai dubi da halayyarsa da kowa ke

kallonsa da ita na rashin sakewa da barazana da rashin ɗaukar raini. Shiyyasa akace karka yankema mutum hukunci har sai ka zauna da shi sannan. Dan wani ɗan

adam ɗin ba’a taɓa karantar shi wanene sai an rayu da shi. Ashe wannan damar Farah ta samu daga garesa take yanda ta gadama. A binda kuma ta fahinta da shi

adalcine kawai da sanin darajar mace da son mutuntata ya sashi zama mai sauƙi ga iyalansa badan anfi karginsa bane ko bazai iya motsa ƙwanji ba. Jitai wani

natsuwa da kaunarsa na sake saukar mata a rai da bargo, har tana jerama UBANGIJI kalaman godiya da samunsa matsayin abokin rayuwarta batare da yayi shawara

da itaba ko dubi da cewar AK ɗin ya ɗarata a komai na darajojin duniya, a lahiran kuma tana fata da addu’ar su kasance a muhalli ɗaya a gurbin gidan aljanna

insha ALLAHU rabbi..
     Da wannan tunanin ta kammala shiryawa a gurgurguje duk tunaninta su Granny na’a gidan basu tafi ba………….✍

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button