MAKAUNIYAR KADDARA 61

Kanta kawai ta jinjina masa. shi kuma ya juya zuwa sashen sa inda ta fara gyarowa duk da ba wani datti baneba.
Tana kammalawa bedroom ta koma tai wanka. Kammala shiryawarta kenan little ya farka. Wankan shima tai masa, ta shafa masa mai tana tunanin yanda za’ayi
akan kayan da zaisa.. A dai-dai lokacin ta jiyo ƙarar doorbell. Little ɗin ta sauke daga kujerar mirror da yake a tsaye tana faɗin. “Ka jirani, idan wani
abuna yay motsi anan kaima saina motsa maka jikinka da duka”. Daga haka ta ɗauka gyale ta fice.
Khalipha ne da kansa ɗauke da kayan little da breakfast ɗinsu. Ta matsa ta bashi hanya tana gaishesa. Cike da fara’a ya amsa mata idonsa akan
little da batasan ya biyo bayantaba. “Uhm my boy ashe anan ka kwana?”. Ya faɗa yana mika mata basket ɗin ya ɗauka little daya nufosa baki a washe. Dan shi
indai mazane to baya jimawa yake sabo dasu. Shiyyasa ko a gidan da wuri ya gama haddace samarin gidan. Kai tsaye sashen AK ya nufa abinsa. Itama sai tai
ƙoƙarin juyawa nata sashen.
Kamar jira tana shiga aka sake danna doorbell ɗin. Sake dawowa tai zata buɗe taci karo da Khalipha ya fito shima. Barinsa tai ya ƙarasa ita kuma ta
tsaya jiran ganin wanene?.
Farah ce ta fara shigowa idanunta jajur alamar tasha kuka. Sai Aunty Zakiyya a bayanta, Mammah na biye dasu. Ba karamin bugawa zuciyar Zinneerah tayiba
da cin karo da Farah, tai wani diri-diri da ita dan koba komai dole taji hakan tunda ta aure mata miji. Jin muryar Mammah datai ya sata sake duban bayan
Farah ɗin duk da kuwa sau ɗaya ta taɓa ganin Mammah ɗin.
Wani irin mahaukacin bugu ƙirjin Zinneerah yayi ta zabura baya batare data saniba. Wani irin duban aunty Zakiyya da itama ɗin dai ita take kallo takeyi
baki a hangame.
Har abada bazata manta da wannan fuskarba. Koda shakara ashirin tai kuwa balle uku kacal. “H….h…hajiya?!”.
Zinneerah ta faɗa cikin rawar baki matuƙa. Wanda hakan yay dai-dai da fitowar AK da yasan da zuwan su Mammah ɗin a yanzu-yanzu da Mahma ta kirasa
take sanar masa nan suka taho batare da sanintaba. Yayi duk yanda zaiyi karya bari Zinneerah ta haɗu dasu. Sai dai kuma hakan bai yuwuba tunda aikin gama ya
gama.
Ba shi da Khalipha ba, hatta Mammah da Farah kallon Zakiyya suke da mamaki ganin yanda tai wani diri-diri tana kallon Zinneerah ɗin itama. Dan da
hasashe kawai take, amma muryar Zinneerah ɗin ta tabbatar mata da eh lallai itace duk da ta ƙara girma ta kuma canja sosai.
“Kin santa ne?”.
AK ya faɗa idonsa akan Zinneerah. Kanta ta shiga jinjina masa, kafin tace, “Itace Hajiyar nan ta katsina da aka kaini gidanta”.
“What!!” AK ya faɗa duk da kuwa dama aunty Zakiyya suke zargi.
Mammah da abun ya harzuƙata ta dakama Zinneerah tsawa. “K!! Shashasha daga ganinmu sai kice wani itace hajiyar da aka kaiki katsina wajenta. To aka
kaiki kikai ubanmi acan?”.
Kafin Zinneerah tace wani abu AK yace, “Mammah kwantar da hankalinki Please. Inaga ai magana ta ƙare kawai. Khalipha kira Faisal kace ya kai matan
nan gidan Baffah gamu nan zamu samesu acan”.
“Abdul-Mutallab banson iskanci, ya ana wata maganar kana ɗakko wata kuma?”.
“Nace ki kwantar da hankalinki Mammah, kumuje can gidan kawai, dan akan wannan sanin junan da sukai akwai magana”.
“Magana!?” Mammah ta faɗa tana kallon aunty Zakiyya da sai yanzu ta samu bakin cewa wani abu.
A firgice tace, “Magana! Dawa za’ai maganar?. Dan kawai ta kirani da hajiya sai kace wani akwai magana. Ke dan ubanki a inama kika sanni dazaki
wani kirani da hajiya?”.
Mamaki ƙarara a fuskar Zinneerah tace, “Hajiya kin manta dani? Nicefa wadda wata hajiya Haule mai jiki ta taɓa kai miki har bani da lafiya kikaita
kaini asibiti ana dubani, nikuma tsoro ya sani gudowa bayan na warke dan canake gidan yankan kai kika kaini”.
Zinneerah ta kara maganar kanta a ƙasa tana tuno komai a ranta tamkar yanzu yake faruwa.
Baki Zakiyya ta buɗe zata sake magana AK ya dakatar da ita. “Please kunga ya isa haka, kumuje can gidan tunda dama ai akwai maganar da akace za’ai
bayan gama taron nan”.
Mammah ta kallesa, dan harga ALLAH ita tama kasa fahimtar ina suka dosa kai tsaye. Ta buɗe baki zatai magana sai ga Mahma data biyo bayansu, sallamar
da tayi ya sakasu juyawa su duka suna kallonta.
Ganin yanda sukai cirko-cirko yasa Mahma faɗin, “Lafiya? Mike faruwa anan?”.
Mammah da dama magana ke bakinta tace, “Wlhy Addah nima da nake tare dasu anan na kasa fahimta, waifa muna shihowa gidan nan sai yarinyarnan mara
kunya take kiran Zakiyya wai da hajiyar da aka kaita gidanta a katsina”. Tai maganar tana nuna Zinneerah da al’amarin masu ya ɗaurema kai itama. Dan harga
ALLAH ita bataga wani abun tada jijiyar wuya anan ba. Daga ta nuna ta santa ai bai kai ya zama tashin hankaliba…..
Mahma data ɗauke kanta daga kallon Zinneerah da Mammah ke nuna mata ta maida ga AK, kai ya jinjina mata kawai. Hakan ya sata fara maganar data katsema
Zinneerah tunanin da tatafi.
“Kunga duk a ajiye wannan shirmen nake ga. kuzo muje can gidan dama Kabeer ne ya kirani wai yanason magana damu akan Adilah”.
Tuni Mammah ta saki batun aunty Zakiyya da Zinneerah ta maida hankalinta ga Mahma wajen faɗin, “What!. Mi kuma yake nufi da zancen Adilah? To wlhy
Addah wannan karon duk abinda zanyi karki tsayar dani, dan dama yau-yau ɗinnan nai niyyar zuwa har gidan na tarkatota itama gobe zamu wuce Morocco”.
Mahma ma nuna ɓacin ranta tai ta hanyar cewa, “Nima ai shiyyasa na biyoku nan ɗin, dan a wannan karon ba ɗagama Kabeer ƙafa zanyiba kuwa koda na
mintuna ɗaya ne. Ku muje can, idan an gama mazo ayi wannan batun nasu Zakiyya ɗin”.
Kafinma Mahma ta rufe baki Mammah takai ƙofar fita, aunty Zakiyya da gaba ɗaya take a harmutse tai saurin fara magana cikin borin kunya. “Kuje, ni dai
zan wuce katsina idan kun gama kwa sameni acan”.
AK daya saki wani murmushin mugunta yace, “Ai hardake za’aje hajjaju, dan maganace data shafi family, idan kuma kin fidda kanki a cikinmu sai muji”.
Wani shegen kallo ta bisa da shi mai kama da ruɗani da tsana, ta buɗe baki zatai magana Mahma ta katseta. “Kunga nifa banason wannan fitinar taku,
ke Zakiyya wuce muje, da an gama maganar ai baki ɗaya zamu wuce komai dare”.
Badan Zakiyya taso ba tabisu, Farah dai ko motsi bataiba dan da ido AK yay mata gargaɗin tsayawa. Khalipha kuwa dama tuni ya fice shi da Little.