MAKAUNIYAR KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAUNIYAR KADDARA 61

       Sai da AK yaji fitar motarsu daga gidan sannan ya kalli Farah da Zinneerah ɗin. “Kuma kuje ku shirya zamu bisu”.

       Jiki a sanyaye Zinneerah ta kaɗa masa kanta, sashenta ta nufa zuciyarta duk babu daɗi da abinda ya faru. Duk da dai tasan ita mai laifice kodan 

gudowar da tai bada sanin hajiya ba batai tunanin abin zaiyi girman haka ba tunda da ya wuce kusan shekara huɗu fa kenan.

     Zinneerah na shigewa Farah tai saurin bin bayan AK, kusan a tare suka shiga falonsa. babu zaton tana biye da shi yaji ta rungumesa ta baya tana sakin 

kuka. Shiru yay kawai yana saurarenta dan yasan kukan mi takeyi, shi shaidane akan kishin Farah, amma yana ƙara hauhawane bisa karatun Mammah da Zakiyya. 

         Dalilin dayasa kuwa ta dawo gidan a yau Mahma ta sanar masa jiya ta zaunar da ita tai mata nasiha mai ratsa jiki, tare da tuna mata abubuwa masu 

yawan gaske waɗanda suka tada mata hankali, tun a daren tace zata taho nan gidan shine aunty Zakiyya ta rufeta da masifa. Ta ringa zaginta ta uwa ta uba 

daya kai har Farah kiran Abbansu ta sanar masa. Shine ya buƙaci ta haɗashi da Mahma suyi magana. Itako Mahma bata ɓoye masa komai dake faruwaba harma wanda 

su su Farah basu san ta saniba. Ya nuna matuƙar tashin hankali saboda shi mutumne nagartacce, ko zaman Farah a hannunsu dan anfi karfinsane kawai, amma duk 

sauran yayunta suna tare da shi sai dai irinsu Zakiyya da sukai aure. A yanzu hakama soyake yay murabus a ɗora babban yayansu Farah ɗin a karagar mulki. 

Zantukan da Mahma ta sanar masa ɗinne ya sashi sanar dasu yau zaizo kano, Farah kuma ta tabbatar ya sameta a gidan mijinta inba hakaba wlhy sai ya saka AK 

ya saketa saki uku, kuma ta dawo zaman Nigeria cikin masarauta.

    Itako a duniya ta tsani zaman masarautarsu saboda yanda ake komai a takure, ga matan babansu sam basa ƙaunarsu saboda son da baban ke nuna musu a 

dalilin rashin mahaifiya. Dama can kuma yaso mahaifiyarsu sosai dan tunkan tabar duniya matan sun mugun tsanarta itama. Abu na biyu maganar sakin da yace 

zaisa AK ya mata. Tasan Abbansu sarai, wlhy zai iya sakawa AK ɗin ya saketa dan kaɗan daga aikinsa. Shima murɗaɗɗen mutumne mai tsayawa akan gaskiya duk 

ɗacinta.

         A hankali AK ya janyeta daga jikinsa yana zagayo da ita gabansa. Ƙyawawan idanunsa masu cikar kamala da kwarjini ya zuba mata hannayenta duka biyu 

riƙe a cikin nasa. Sake fashe masa da kuka tayi kishinsa mai tsanani yana taso mata, amma tanata ƙoƙarin ganin ta danne dan duk runtsi bata iya rabuwa da 

shiba saboda tana sonshi.

     Karan farko AK ya saki murmushi da kai hannu ya share mata hawayen dake sauka a fuskarta. “Nifa kinsan banason kuka ko?”. Ya faɗa yana rungumota 

jikinsa dan shima yanason kayarsa.

        Ƙanƙamesa tai tana sake fashewa da wani kukan, “Dan ALLAH Yah Abdul-Mutallab kayi haƙuri wlhy Abbah zai iya rabamu, ka taimakeni karka faɗa masa na 

tuba”. 

          “Toni dama miya haɗamu da har zan sanar masa?”. Ya faɗa yana ɗago fuskarta. Cigaba yay da faɗin, “Kece kike biyema su Mammah ai dama, suna amfani 

dake wajen biyan buƙatunsu batare da kin fahimtaba. Sannan kina barin kishinki na rinjayar tunaninki bayan kinsan ina sonki. Sokike ne na dinga binki kamar 

wani sakarai dan kawai ki tabbatar ina sonki? Ko sokike nabar mahaifina da ƴan uwana dan kawai ina sonki Farah? Wannan abun shina dinga tsoratar miki dama. 

Randa zan iya ƙosawa da halayarki na fara tunanin ƙara aure. Iyayena da baki ragamawa suma su bani goyon bayan yin. Amma sai kika kasa fahimta, ke ga mai 

Mammah da aunty Zakiyya ko?. Gashi nan duk yanda nake ɓoyema Maimartaba halayyarki sai da takai kin tonama kanki asiri da kanki”.

          “Na tuba wlhy, dan ALLAH ka taimaka karka faɗa masa yanzuma, dan wlhy yace yana hanyar zuwa kano. Na rantse yana tambayarka ka faɗa masa sai ya 

raba aurenmu kasan halinsa”.

        “Idan kinmin alƙawarin zaki nutsu, ki komamin Farah dana sani a baya, mai tattalina da ƙaunata bazan faɗa masaba. Sannan duk abinda za’a tattauna a 

gidanmu yanzu zaki faɗi gaskiyar abinda kika sani bazan taɓa yarda a rabamuba koda kuwa zan hukuntaki da laifinki ne”.

       Batare data nutsu ta tace zantukansa ba tace, “Na amince wlhy Yah Mutallab”.

          Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe a kanta, tare da sunbatar goshinta da laɓɓanta. A dai-dai lokacin da Zinneerah ta shigo falon da sallama, hannunta 

ɗauke da basket ɗin da Khalipha ya kawo musu breakfast. Dan harta fito saita tuna ko karyawa basuyiba. Shine tai tunanin kawo masa koshi zaici dan ita kam 

bazata iya shan ko shayi ba.

     Wani irin bugawa ƙirjinta yayi, tai saurin ja da baya jikinta na rawa, dan shigowar tata yayi dai-dai da ɗaura lips ɗinsa akan na Farah, itako ta cafke 

tana kara rungumesa kamar yanda shima ya sake rungume abarsa.

        Jin basket ɗin hannunta zai faɗi ya sakata saurin ajiyewa a ƙasa ta juya da sauri ta fita dama a farkon shigowa take……………..✍ 

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button