MAKAUNIYAR KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAUNIYAR KADDARA 62

       Waziri ne ya gabatar musu da addu’a. Kafin hajiya iya ta fara magana.

        “Zan fara da sunan ALLAH mai rahama mai jinƙai, dan shine yay sanadi da silar taramu anan ta dalilin wani saka mai sarƙaƙiya da duk ta sarƙe 

zukatanmu kafin shi wannan zaman. Anan mu dukanmu iyayene kuma kakannine, dan haka ina fatan zamu bada haɗin kai wajen nutsuwa mu fahimci abinda ya taramu, 

sannan duk wanda al’amarin ya shafa dan ALLAH ina mai roƙonsa dayaji tsoron ALLAH mai zartar ga hukunci a sanda yaso ga wanda yaso ya faɗi gaskiyar abinda 

ya sani. Mun cire hukuma ne a wannan zancen saboda wasu dalilai. Ba kuma hakan na nufin bazamu iya maida komai garesu bane duk da mun kasance a ƙarƙashin 

inuwar zumunta ta dalilin aure da sauransu. Wannan yarinya da kuke gani…..”

     Ta nuna Zinneerah da kanta ke a durƙe tamkar Farah.

      “Sunanta Zinneerah. Malam Sulaiman gashi nan zaune shine mahaifinta. Wannan kuma Hauwa’u ɗiyar ƙanwata itace mahaifiyarta. Waɗan nan iyaye sun rabu 

sanadin ƙaddara data saka Zinneerah zama a hannun matar uba bayan barin Hauwa’u gidansu. Inda ita wannan matar uba nata ta raineta cikin gallazawa da son 

zuciya, a ƙarshe kuma ta miƙata aikatau bada sanin mahaifintaba. Sanadin wannan aikatau ta dawo musu da ciki da suka rasa daga ina ta samosa. Aka turketa da 

tambayar duniya da barazana tace ita bata aikata komaiba kuma batasan mai ciki ba. An turza iya turzawa tace bata saniba. To a yanzu dai wannan yaro dake 

jikin Alhaji Abubakar shine ɗan data haifa. Nasan kuma duk wanda ya kallesa zaiyi mamaki da ruɗani akan kamanninsa da Moddibo. Kuma komi za’a faɗa bazai 

yardaba zai dangantashi da shi a matsayin mahaifinsa kamar yanda muma mukaitayi. Bazan kaiku da nisaba, ga dai wadda ta kai Zinneerah aikatau birni, zamu 

fara ji daga gareta yaya aka haihu a ragaya. Hajiya Lanti bismillah”.

    Hajiya iya ta ƙare zancenta da kallon Hajji lanti dake zaune ita da hajiya Haule da kallo ɗaya zakai mata ka tabbatar a gigice take tun zuwansu gidan.

        Zama hajji lanti ta gyara. Kanta tsaye ta fara magana da iya gaskiyarta. “Ni Lantana nayi alƙawarin faɗar gaskiya kamar yadda Hajiya mama ta buƙata, 

zanyi hakanne kuma domin na fita har a wajen UBANGIJI na. Wannan sunanta hajiya Haule. a garin katsina take zaune. Na santane dalilin wata ƙawata ƴar kankia 

da muke zuwa sarin kayan koli kano, itace ta haɗani da ita akan na dinga kai mata yara masu aikatau. Zuminci ya ƙullu a tsakaninmu mai ƙarfi saboda kai mata 

yara da nakeyi akai-akai. Har ALLAH yasa Zinneerah ta shiga sahunsu a dalilin matar mahaifinta Asabe. Labarin kuɗin da ake samu a dalilin aikatau yasa Asabe 

ɗaukar Zinni ta bani saboda ta mallake babanta ga shinan bai iya ce mata bai iya musata. Na ɗauka Zinni na kaita garin katsina aikatau tare da wasu yara, 

washe gari na juyo da nufin komawa gida ƴan doka suka kamani a tsaranci dalilin wata yarinya. Kusan shekarata biyu a gidan kaso, na fito shine naci karo da 

mummunan labarin Zinni ta dawo da ciki. Wlhy, wlhy, wlhy, wannan shine kawai abinda na sani, amma bansan komai game da cikin Zinni ba”.

        Kowa ya gamsu da zancenta, dan haka suka maida dubansu ga Hajiya Haule dake sharar zufa.

      “Nima nayi alƙawarin zan faɗi gaskiyata ni Hajiya Haule, dan faɗan da yafi ƙarfinka masu iya magana sunce ka maidashi wasa. Kamar yanda Hajiya lantana 

ta faɗa duk anyi haka. Ta kawomin yara ciki harda wannan yarinya Zinneerah saboda dama muna irin wannan huɗɗar. Inda ni kuma na danƙata hannun Hajiya 

Zakiyya. Amma kafin ita Zinneerah dama akwai wata yarinya da na taɓa bama ita Hajiya Zakiyya ɗin. Wadda ta sanarmin zasuyi mata aikine kuma zata bani 

maƙudan kuɗaɗe harda iyayen yarinyar. Babu wani ja’inja na yarda duk da kuwa bata fito ta sanarmin da ainahin aikinba, amma jin kuɗi ya sani ruɗewa na 

amince mata. A tashin farko ta diremin dubu ɗari biyar, hakan yasa a haukace na kai mata wata yarinya da aka kawomin dan sama mata aiki. Sai dai kuma bansan 

yaya akaiba bayan kusan sati ɗaya ta dawomin da yarinyar akan na sama musu wata ita bazata iya aikin da suke buƙataba. Nasha mamaki saboda yarinyar dana 

basu babba ce, nasan kowane irin aiki aka sakata zata iya. Dan haka na kasa daurewa na tambayeta duk da inajin tsoro saboda girmanta da kasancewar wadda ta 

fito daga masarauta. A lokacin bata kulani ba. ta daice naje idan an samu tana jira. Haka na baro gidanta cike da wasiwasi amma bani da mai bani sani sai 

ALLAH. Anyi haka da kusan wata ɗaya sai ga Hajji Lanti da yara. Da farko dai ƙyawun ita wannan yarinya yasani jin sha’awar kai mata ita, dan nasan masu 

kuɗinnan dason ƴar aiki mai tsafta da ɗan fasali haka. Cikin amincewar UBANGIJI kuma tana ganinta sai tace tayi, ta kuma ɗauka cikon kuɗina har naira 

miliyan ɗaya ta bani, duk da dubu ɗari biyar ya kamata ta cikamin. dan munyi da itane akan miliyon ɗayan, nawa dubu ɗari biyu na iyayen yarinya dubu ɗari 

uku, na yarinya ɗari biyar, amma ban saniba ko jin daɗin samo yarinyar yasata bani ƙarin dubu ɗari biyar, bakuma tamin bayanin ta karanba sai da naje gida 

na kirata dan duk zatona ko bata kulaba ta bani. Amma sai tace min tana sane. Samun yarinyar dai-dai da ra’ayinsu yasata ƙara mana waɗanan kuɗi mu da iyayen 

yarinyar. Ta kuma ɗora da faɗamin zasuma yarinyar dashe ne na ciki, idan yakai wata biyu zasu ɗauketa zuwa ƙasar waje har saita haihu musu su sallamota da 

tagomashin arziƙi, amma wannan sirrine tsakaninmu, ko iyayen yarinyar bataso su sani kawai nace dasu ta tafi turai ne da yarinyar inda take zama da mijinta. 

Iya abinda ta sanar min kenan ta yanke wayarta. Harga ALLAH na girgiza da zancen sai dai inda aka fi ƙarfi nane bani da damar cewa komai. Kamar yanda ta 

buƙaci karna bar Nigeria sai aikinsu ya kankama na amince, dan dama kuɗin data bani so nake na koma ƙasar saudia inda dama can nake zaune a da. An yayonine 

an maidoni rashin kuɗi yasa ban komaba. Gaba ɗaya na mallake kuɗi har na iyayen yarinya dana yarinya da tace, ko Hajji Lanti data kawomin yarinya ban nema 

ba. Dan na shirya kamfinma ta dawo amsar kuɗaɗen yaran data kawo nabar ƙasar insha ALLAHU. Bayan anyi haka da sati uku inata shirina sai ga wayar hajiya 

Zakiyya, ta tabbatarmin aiki yayi zan iya tafiyata cikin murnarta. Nima naji daɗi sosai dan dama kayana a shirye suke, hakan yasa kwana biyu dayin magana da 

ita na wuce saudi-arebia da yara guda biyu. Daga haka ban sake sanin komaiba sai jiya da ƴan sanda sukazo har gida batun kamani. Wallahi tallahi ALLAH shine 

shaidata wannan shine abinda nima na sani, dan ALLAH ku gafarceni na tuba”. Ta kare maganar tana share hawaye.

        Gaba ɗaya falon ya ɗauka salati ana duban Zakiyya da tai ƙasa da kanta, daka ganta kasan a firgice take matuƙa. Hakama Mammah a ruɗan take amma duk 

tasan itama akwai sunanta a ciki so take taji ta bakin Zakiyya game da cikin Zinneerah da ita dai harga UBANGIJI batasan da zamansaba.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button