MAKAUNIYAR KADDARA 62

Zinneerah kam mutuwar zaune tayi tanabin kowa da kallo kawai tamkar butun-butumi, dan harga ALLAH suna neman rikitar mata da tunani. Ita kanta burinta
kawai aunty Zakiyya tayi magana.
Mai martaba da zuciyarsa har wani tafasa take ya kafe Zakiyya da kallo yana kuma duban Farah dake kuka itama wiwi. A zafafe yace, “To dan uban daya
haiheki sai kimana bayani muji lalatacciyar yarinya kawai. Wannan wane irin kafurcine kuma daga ina kika samosa ko kuka samosa tunda dai babu yanda za’ai
dashe masu ƙwai basu saniba. Shi ƙwan na wanene? Kuma yaya akai?”.
Ƙasa ta zamo ta dirƙushe jikinta na rawa, dan tafi kowa sanin wanene mahaifinsu. Inhar kuma tai gigin faɗar abinda ba haka bane lallai zai mata
abinda gwamma ta faɗi gaskiyar.
Kafin tace komai Farah da tsoro ke neman gigitata na tsawar mahaifin nasu ta fara rawar jiki da faɗin, “Wlhy Abbah babu ruwana nidai, duk aunty
Zakiyya ce ta tsara komai, itace tasa muyi wlhy badan inaso ba……”
Hankali tashe itama Zakiyyan ta fara magana, “Dan girman ALLAH Abbah ka gafarceni. dan ALLAH kar kayi fushi dani, Baba wambai ka bashi haƙuri dan
ALLAH”.
Aminin mai martaba da suke kira da baba Wambai ya gyara zamansa cikin kasaitar mulki da dattako yace, “Zakiyya kafin azo ga neman gafara ai nakega
ya dace musan yaya akai ko? Kinsan mai martaba bayason jayayya, dan haka ki buɗe baki kiyi bayani tamkar yanda suma waɗanan mata sukayi, inaga shine zaifi
sauƙi kamar kafin muzo ga gaɓar da kike so”.
Kanta ta jinjina masa tana sharce hawaye.
“Kowa yasan Farah dai autarmu ce da tausayinta yasa duk muka ɗauka son duniya muka aza mata, musamman ma ni daya kasance itace kawai ƴar uwata
mace, sauran ukun duk maza ne. Farah a Morocco ta rayu hannun kakarmu data baro london, bayan rasuwarta Mammah yayar mahaifiyarmu ta amsheta ta koma da ita
london. Tausayin da kowa yakema Farah a cikin dangi shi Abdul-Mutallab ke mata shima. Hakan yasa yafi kowa nuna jin daɗinsa da komawar Farah garesu. Kamar
yanda take samun gata daga Mammah haka shima take samu a garesa, ta sanadin hakan shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, daga karshema ta juye soyayya. Kowa
yaji daɗin hakan a dangi, dan babu wani ja’inja aka yanke zancen aurensu. Bayan bikin su da kusan shekar biyu babu wani labari koda na ɓatan wata daga
wajensu, babu kuma wanda ya damu da hakan sai ni dana farajin damuwa. A wani zuwa da tayi Nigeria na takura mata mukaje Doctor ya dubata, inda mukaci karo
da mummunan labarin daya nema zautani, dan ita koma a jikinta saboda ƙuruciya na ɗawainiya da ita a lokacin. Doctor ya tabbatar mana akwai wani tsiro daya
toshe bakin mahaifar Farah gaba ɗayanta. Yanda da wahala ace ciki ya shiga, kodama ya shigan bazai zaunaba. Na bukaci ai mata aiki a ciresa idan zai yuwu,
sai ya tabbatar mana taɓashi babbar matsalace, dan zata iya rasa ranta, sannan basu da wani maganin da zai iya gusar da shi a yanzu haka dai. Naci kuka
sosai na kuma shiga damuwa da tunanin neman mafita ma yar uwata. Da farko dai son ganin jinin autarmu yasani damuwar, amma dalilin shigowar wasu maƙudan
kuɗi ga Abdul-Mutallab da zantukan danginsa na ya ƙara aure ya far canja alkiblar tunanina, zuciyata ta fara rayamin idanfa ƴar uwata ta haihu da shi komi
ya tara mallakintane ita da ɗiyanta. Idan kuma nayi sakacin hakan suka aura masa wata akwai matsala tunda likita ya tabbatar mana akwai matsala game da
mahaifarta ita. Wannan tunanin ya sani ɗaukarta a wani zuwa london da nayi muka fara bin likitoci ba tare da sanin Abdul-Mutallab kosu Mammah ba. Sai dai
duk inda mukaje amsar dayace mahaifarta nada matsala, kuma irin bayanin wancan likitan suma suke mana dai. Hankalina ya ƙara tashi haka itama nata, dan
haushin rashin damuwarta yasani zama na fahimtar da ita. Nasha takaici ganin daga baya ta nuna ita fa ba komai bane, tunda Abdul-Mutallab na sonta tana
sonshi ko bata haihuba babu damuwa, ballema bata fidda ran a gaba su samuba dan bata yarda da maganar likitocinba ALLAH ne maiyi. Duk da gatan da mukema
Farah na tsiya nasan tanada zurfin tunani da aiki da hankalinta matuƙa, sai dai banyi zaton zata kasa fahimtataba musamman dana san tanada kishi mai zafi
irin namu musamman akan Abdul-Mutallab. Lokacin da suke cika shekaru uku da aure kakarsa ta ƙara bijiro masa da zancen aure a time ɗin sunzo Nigeria tare,
hankalin Fara ya tashi matuƙa, dan tanada tsananin kishi”………..✍
[ad_2]