MAKAUNIYAR KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAUNIYAR KADDARA 63

 

*Page 63*

…………“A wannan gaɓar saboda yanda ta nuna tashin hankalinta matuƙa sai nayi amfani da damar wajen sake zaunar da ita na nuna mata muhimmanci 

haihuwarta. Tare da kawo mata zancen dashen ciki. Ta razana matuƙa, ta kuma ce ita dai gaskiya tanajin tsoro, dan tasan Abdul-Mutallab ma ba yarda zaiba. 

Dan haka kawai mubar zancen na tayata da addu’a dan bazata iya zama da kishiya ba zata iya halaka kanta. Wannan furuci nata ya kuma ɗagan hankali matuƙa, 

dan nasan zata iya aikata abinda ta faɗan, na kuma tabbatar auren Abdul-Mutallab bazai fasu ba inba danginsa sunga ta haihu ba. Ta kuma nunamin su Mammah ma 

ba yarda zasuyiba dan abune da kowa yasan malamai na nuna illarsa a addinance dama lafiya ta wani fannin. Ban gusaba wajen zaman cigaba da nusar da ita, 

tare da kawo mata dabarun da zamuyi maganin kowacce matsala. Na farko karmu bari AK ya sani, ayi komai a ɓoye harta wadda za’a sama cikin ta haihu ace itace 

ta haihu. Ta tambayeni taya za’ai hakan ta kasance bayan koyaushe tana tare da AK. Na ce mata ta bari zanyi tunani. Bayan kwana biyu dayin maganar na samo 

mafita a wajen Doctor ɗin da zaiyi aikin, idan an dasama wadda zata raini ciki ita zata fara pretending like pregnant, bayan yakai kamar 3months zata koma 

zama a Morocco ta hanyar wasu dabaru namu na mata har mai ciki ta haihu a bata ɗanta ta shayar ita da kanta. Cikin tsoro tace amma tayaya hakan zata faru 

bada yardar su Mammah ba. Niko nace mata Mahma ce kawai za’a ɓoyema gaskiyar zance, amma Mammah da ita za’ai komai. Tacemin ta yaya Mammah zata yarda da 

hakan?. Nace mata ta hanyar yin amfani da ita akan so da kishin da takema mahaifin Abdul-Mutallab da ganin laifin danginsa da take na rabuwarsu, da kuma ƙin 

son rabata da ƴaƴanta da shine babbar barazanarta a rayuwa. A lokacin Farah bata bani goyon bayaba, dan tace bata yarda a cutar da kowa ba, musamman ma 

Mammah da ta ɗauketa daidai da nata ƴaƴan saboda ƙaunar da takema mahaifiyarmu. Sosai na mata masifa ni da Muktar a lokacin, dan shine ya taimaka mana da 

likutan da zaiyi aikin ma. Da dai mukaga taƙi tanƙwaruwa ta sauki sai itama nabi da ita ta hanyar razanarwa da kshiya har tai laushi ta amince. Tun daga 

lokacin itama Mammah na fara aiki a kanta, sannan Doctor ya tsarama Farah yanda zamu sami sparm ɗin Abdul-Mutallab cikin sauƙi”.

               Babu wanda mamaki bai nema kashewa a falonba, musamman ma Mammah datai mutuwar zaune akan wannan labari na Zakiyya. Zakiyya ta cigaba da 

faɗin,

        “Bayan wani lokaci na tunkari Mammah da batun ya kamata musan halin da Farah da Abdul-Mutallab ke a ciki game da haihuwa, kar muyi sakacin da dangin 

mahaifinsa zasu aura masa wata zasu rabamu da shine kawai ya koma hannunsu. Na tabbata wannan kalma ta tada hankalinta matuƙa, dan babu abinda tafi tsana 

arayuwa kamar ace yaranta zasu koma hannun mahaifinsu. Bayan munyi wannan maganar washe gari taima Abdul-Mutallab maganar a gabana, amma sai ya nuna ɗan 

ɓacin ransa akan duka shekararsu nawa da auren da har za’a fara nuna damuwa basu haihuba, shi wannn maganar dan ALLAH a barta ALLAH ne mai badawa kuma zai 

basu lokacin da yaso. Da wannan furucin yabar gidan a zuciye. Hankalina ya tashi, dan gashi saura kwana biyu na baro london ɗin, dan haka na sake sabon 

zaman fanfa Mammah da kawo mata dalilai kala-kala da suka dinga ruɗa mata tunani itama tana ruɗashi. Tashin hankalin data nema sakashi a ciki ya sashi 

tattaro Farah suka gudo Nigeria a lokacin bamu sani ba. Sai da sukaje ta kira take sanar mini. Naji daɗin hakan, dan nima a gareni wata dama ce. Dan haka na 

sake buɗe wutar data harzuƙa Mammah harta kirasa ta tabbatar masa da inhar bai yarda da batuntaba wlhy zata iya tsine masa. Sosai Abdul-Mutallab na gudun 

ɓacin ran mahaifiyarsa. Dan haka furucinta ya tada masa hankali yace ya amince zasuje idan sun koma london. Still nice dai na sake bama Mammah shawarar suga 

Doctor Hannafi dake nan Nigeria shima kwararrene a wanna fanin kuma a can london ɗinma yay karatunsa da aiki harna tsahon shekara bakwai. Batare da wani 

jayayyaba ta kirasa da tura masa address da phone Number ɗin Doctor Hannafi dana bata nima kuma na tattaro na dawo Nigeria neman yarinyar da za’aima dashen. 

Ta farko bataiminba, dan tanada wayo kuma idonta a buɗe yake, hakan yasa nasa hajiya haule canjamin ita.”

         “Biyayyar da Abdul-Mutallab yake ma Mammah ya sashi ɗaukar ƙafa sukaje ga Doctor Hannafi, wanda dama mun gama tsara komai. Dan haka kawai abinda ya 

buƙata a garesu shine sparm ɗin sa, ita kuma Farah yay mata wasu gwaje-gwaje kamar gaske. Domin kawai bin umarni Abdul-Mutallab ya yarda ya bama Dr Hannafi 

Sparm ɗin nan, wanda da shine aka haɗa da ƙwan Farah akaima ita Zinneerah dashen bayan mun tabbatar zata iya. Dan ita bata kai waccan girma da wayo ba, amma 

yanayinta kawai zaka kalla bama zaka ɗauka a ƙauye ta fitoba dan ƙyakyawa ce. Da wannan karancin shekarun nata mukai amfani wajen yin komai na dashen batare 

da ita ta fahimci komaiba, dan ALLAH ya taimakemu sanda aka kawo min ita tana cikin halin zazzaɓi sai komai ya ƙara zuwa mana dai-dai muka tafiyar da ita 

akan treating ɗin zazzaɓin nata. Sai dai kuma bayan dashen muna fata da addu’ar ALLAH yasa ya zauna da kwana uku muka nemeta muka rasa. Hankalina ya tashi 

matuƙa a wannan lokacin, nama kasa sanarma Farah yanda akai sam. Sai dai munta tararrabin mu da neman yarinya ni da Muktar da Dr Hannafi. Gashi Hajiya Haule 

ta wuce saudia kuma bani da contact ɗinta nacan balle mu binciki garin da ta ɗakkota. Dr Hannafi ne ya kwantar min da hankali ta hanyar sanar min da 

wahalama cikin ya zauna, dan bai kai kwanakin da ake buƙatar nutsuwarta a waje guda ba, kawai yanzu dabarar da zamuyi a karasa AK ya bada sparm ɗin nasa 

kafin su wuce sai a sake yima wata dashen, wannan kuma mu ɗaukama bazai zauna ba kawai, musamman da ko magungunan daya kamata tasha sau daya ta shasu. Na 

ɗanji sanyi da wannan shawarar tasa, akanta kuma na yanke hukuncin tun karar Mammah da batun dashen cikin. A ranar na kirata, na sanar mata Dr Hannafi ya 

tabbatar mana AK nada matsalar bama mace ciki, amma za’a iya yin amfani da sparm ɗinsa ai dashe, sai dai matsalar itama Farah nada tata matsalar a mahaifa 

kuma”.

          “Hankalinta ya tashi, harta buƙaci na haɗata da Dr Hannafi ɗin, na kuma haɗata dashi ya sake mata bayanin daya kamata akan dashen da tsarin da 

za’ayi. Ta tabbatar masa da zata iya yarda ayin kodan a samu ɗan danginsa su daina harar mata yaro dason mallakesa. sai dai babbar matsalarta shine Abdul-

Mutallab, tasan bazai taɓa yarda da hakanba koda zata tursasashi a wannan gaɓar. Cikin dabara Dr Hannafi ya shigar mata da shawararmu na yanda tsarin zai 

kasance batare da Abdul-Mutallab da kowama sun fahimci hakanba bayan mu. Tace ya bata dama zatai tunani da shawara. Cikin amincin ALLAH sai tai shawara 

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button