MAKAUNIYAR KADDARA 63

dani, dan a tunaninta bansan komaiba game da dabaran. Babu wani ja’inja na nuna mata hakan shine dai-dai, tare da sake kawo mata dalilaina nima. Sai ko aka
dace ta yarda dan nayi amfani da inda ke mata ƙaiƙayi. Amincewar tatace ta zama ginshiƙin tushen aikinmu na biyu, sai dai a wannan karon cikin bayin gidanmu
na ɗakko, kuma da amincewarta dana iyayenta, ana kuma gamawa na maidota gidana ina kula da duk motsinta har ALLAH tasa ciki ya zauna ya kai wata biyu da
wasu kwanaki sannan Mammah tazo da kanta ta tafi da ita Morocco. Zuwa sannan kuma Abdul-Mutallab da wasu a cikin danginmu sunsan Farah nada ciki, sai dai
mun gargaɗi Abdul-Mutallab da sanarma danginsa zancen ciki har sai Farah ta haihu saji hakan zaisa sufi murna ya kuma musu surprise. Ya amince da hakan kuwa
sai dai bamusan dalilinsaba. Sai dai ashe kana nakane ALLAH na nashi, dan randa Farah ta baro london da nufin zuwa tai goyon ciki a Morocco wanda tursasawar
Mammah yasa Abdul-Mutallab yarda washe gari yarinyar tayi barinsa. Ranar ba Farah kawai ba hatta ni da Mammah sai da mukai kuka wlhy, Abdul-Mutallab kuwa a
ranar ya baro london zuwa Morocco hankali a tashe. Shima har kukan yayi saboda ya ƙwallafama cikin nan rai kamar mi. Bayan gama wannan taraddadin bawai na
haƙura bane akan ƙudirina. Na cigaba da zungurar Farah da Mammah suna zillewa. Dan kai tsaye Farah tace min alhakin Abdul-Mutallab ne yasa cikinma ya zube.
Faɗa mukaita mata a lokacin, amma taƙi saurarenmu. Mun tattara mun ƙyaleta a lokacin danta huta dan naga itama Mammah na neman fara zamemin. Taimakon da
ALLAH ya sakemin shine takurawar Abdul-Mutallab ya ƙara aure daga hajiya iya, wanda har takai ga ya ɗauke kafarsa da Nigeria, sukuma suka tura masa ƙaninsa.
Tun daga nan na fahimci hankalin Farah baya tare da ita, dan duk wani abinda ya faru tsakaninta da Abdul-Mutallab sai ta kira ta sanarmina lokacin. Abinda
na fahimta shine kishin zancen ƙara aurensa na cinta har take ganin kasancewar wani nasa tare da shi zai sa danginsa suci galaba a kansa. Na biyu kuma
tashin hankalin Mammah itama na kada Abdul-Mutallab ya komawa danginsa yasa take goyama Farah baya.”
Takai ƙarshen zancenta tana share hawayen da tun ɗazun basu gajiya wajen kwaranya ba daga kumatunta, dan muryarta har dashewa takeyi dan kuka.
Tsitt falon yayi motsima kowa ya kasa dan al’ajabi, wane irin masifa ne wannan da haɗa boom. dan wannan al’amari na Zakiyya yayi kama da haɗa boom.
Dan kawai kinason ƴar uwarki sai ki ƙulla abinda zaki cutama rayuwar wasu.
Kallonta kawai AK yace cike da tsana da takaici. idanunsa sun kaɗa sunyi jajur, hakama jijiyoyin kansa sunyi ruɗu-ruɗu. Hakama Farah kuka take tamkar
ranta zai fita, dan tasan dai komai Zakiyya tayine dominta, gashi tun ba’aje ko’ina ba komai ya ƙwaɓe. Kishiyar da take tsoro kuma an mata ta sanadinsu.
Mammah ma kanta duƙe a ƙasa dan tama rasa mi zatace dan tashin hankali da baƙin cikin kanta da kanta, tayaya ta zurma haka da yawa yarinya ƙarama
ta ɗana boom ɗin da a ƙarshe yake neman tashi da ita? Tayaya idonta ya rufe haka da yawa ne akan abinda yana a hannunta amma gashi sakacinta ya ta miƙashi
ga mai shi?…….
Cikin ƙunar Zuciya AK ya katse tunanin kowannensu ta hanyar faɗin, “Shima cikin da take dashi yanzu na ƙaryane kenan? Randa mukaje asibiti da nufin
sake duba lafiyata kune kuka ƙulla?.”
Kasa magana Farah da Zakiyya sukayi. sai Mammah ce cikin kuka tace, “Kayi haƙuri Abdul-Mutallab, tabbas wannan duk laifinane, da ace ban bata
goyen bayaba babu yanda za’ai hakan ta kasance. Nayi nadamar saninki Zakiyya, wannan wane irin haline haka da kika nema jefamu a ciki. Har takai na saka
hannu wajen cutama gudan jinina ta hanyar makircinki”.
“Dama shi son zuciya ai ɓacin zuciya ne, daga lokacin da kake ganin wayonka ko dabararka zai baka abu to lallai a lokacin ka ɗaura ɗammara da ɗambar
rasashi, dan koka samu sai ya suɓuce maka. Kin biyema yara ƙanana saboda wani shirmen banza da wofi Hindatu, yanzu da ALLAH bai ƙaddara yarinyarnan ta faɗo
cikinmu ba yaya kenan? Duk da dai sanda sukayi na farko basu sanar miki ba, amma na biyun da’an haifesa fa? Shikam kinada kamasho a ciki ai”. Uncle Ahmad ne
ke magana cikin ƙunar zuciya.
Kauda kai AK yayi yana rumtse idanunsa saboda zafi da ƙirjinsa ke masa. ga kansa sai juya masa yakeyi alamar hawan jininsa na neman motsawa. Cikin
harɗewar harshe yace, “Uncle idan wancan ya salwanta aiga waninan ma sun sake dasawa. Tunda sunce tanada ciki kuma likitoci sun tabbatarmin babu wani ciki
tare da Farah”.
Yanzu kam duk yanda mai martaba da mukarrabansa sukaso daurewa sun ƙasa. Cikin kaushin murya yace, “ALLAH zai sakamin ɓatamin suna da kukayi. musamman
ke Zakiyya dan kece kika ƙulla komai, kece kika ɗora ƴar uwarki akan abinda sam babu shi a ranta, ni yanzu bamma san mizance mukuba wlhy, dan yanda nakejin
raina zanma iya tsine muku. Amma inason sanin gaskiyar zancen shi cikin da akace tana dashi yanzu, dan nikam kotun musulinci zan kaiku a yanke muku hukunci
dai-dai da laifinku”.
Sosai Farah ta fashe da kuka. Ta rarrafo gaban mai martaba ta kama ƙafafunsa da fashewa da kuka. “Dan ALLAH Abba kayi haƙuri, nidai wlhy bazan sakeba,
wannan ma kota haufa banaso zanyi haƙuri ALLAH ya bani nawa. Na tuba Abbah dan ALLAH na tuba”.
Banza yay mata yama ɗauke kansa ya maida ga Zakiyya da itama kukan take. “Wai bada Zakiyya nake maganarnan ba?!”
Zabura ta ɗanyi saboda yanda yay maganar a tsawace, ta shiga jinjina kanta da faɗin, “Abba hakane, shima dasawar akai, amma wannan ƴar Morocco ce, kuma
da amincewarta itama wlhy”.
Sake ɗaukar sallalamu falon yay gaba ɗaya, hajiya iya dake sharar ƙwalla tace, “Gaskiya baku ƙyautaba, wannan zaluncine wlhy dason zuciya. A barshima
mutum shi ya yarda yay muku wannan aikin da sauƙi ai, amma kamar yarinyarnan aikun zalunceta. Inda ALLAH bai ƙaddara tamu bace kamar yanda Ahmad ya faɗa
harta mutu baza’a daina mata kallon wannan tabon ba. Yaya zakuyi da alhakin wannan yarinyar kawai ma balle na sauran suma, sai dai idan da yardarsu kukayi
sukam. Nikam dai ina bayan mahaifinku a kaiku kotun musulinci a bin kadin jikata na rainon cikin da tayi. kuma wlhy ko sama da ƙas zata haɗe ɗannan ya zama
nata har gaban abada marasa mutunci”.
A take su waziri suka shiga goyama hajiya iya baya, kowa na tofa albarkacin bakinsa. Mmn sadiq, Abba, baba sune dai basuce komaiba, sai dai duk
sai da sukai ƙwallar tausayin Zinneerah harma da AK da little. Sai da ƙyar Baba ya fara magana ganin kowa ya yarda da zuwa kotin.
“Ranka ya daɗe nikam kuyi haƙuri zance wani abu”.