MAKAUNIYAR KADDARA 63

Duk hankalinsu suka maida garesa. Ya ɗan muskuta zamansa yana gyarama little dake a jikinsa kwanciya, dan shi yaune karon farko daya ga jikan nasa,
“Kuyi haƙuri nasan tabbas basu ƙyautaba, kuma zaluncine abinda sukayi dan yarinyarnan taga rayuwa mai zafi kala-kala a dalilin cikin nan. To amma Alhmdllh
ta wani gaɓar ya zamar mata alkairi. Dan a sanadin samunsa ta sadu da mahaifiyarta, ƙaddara ta ɗakkota ta kawota cikinku da har a yau ya zama sillar
bayyanar komai, bugu da ƙari yay mata ƙyauta da miji uban ɗan kuma saboda hikimarsa. Sannan a sanadinsa nima kaina nabar gida harna samu waraka daga kaidin
matata, na kuma ƙara aure a yanzu haka matata ta haifamin yara maza ƴan biyu guda biyu tun washe garin da suka koma gida. Waɗanan kaɗanne daga ni’imomin
UBANGIJI gagara misali daya lulluɓe Zinneerah dasu a sanadin cikin yaron nan da batajiba bata ganiba. Tabbas duk mai haƙuri zai dafa dutse harma yasha
romonsa. Su dai duk sun aikatane akan dalilai biyu zuwa uku. Mahaifiyarsa dalilinta kawai kar ya dawo hanun ubansa ne da rayuwa, sai kuma gashi ya dawo
cikin sauƙi. Ita wannan yarinya saboda kar mijinta ya ƙara aure ne, kuma gashi ya ƙara ɗin harma suna zaune a inuwa ɗaya. Ita wannan ƴar uwa tata kar wata
tazo ta haihu ba ƙanwartaba. Gashi kuma watan ta haihu ba kanwar tata ba. To idan mukai tsam a nazari zamu fahimci UBANGIJI ya bama kowa sakamako nan duniya
dai-dai da shi da tabbatar musu cewar wayo ko dabarar bawa bata kaisa da nasara. duk saurinka kuma saika jirayi zartar da ƙaddarar UBANGIJI gamai ita. Tunda
su duk sunyine a ɓoye domin bama kayinsu kariya akan abinda yake gaibu kuma dauɗar duniya amma daga ƙarshe gashi duk sun rasa, kuma wanda sokaso ƙwata daga
wajensu ALLAH ya maido musu. A ganina kuma miya rage banda mu barma UBANGIJI ikonsa ya ƙarasa zartar da hukuncinsa. Basai anje kotuba, dan mu dukanmu ALLAH
ya haɗamune a ƙarƙashin inuwar zumunci sai muyi haƙuri wajen haɗiye duk wani saɓani da zaizo a garemu duk da kuwa wannan ya banbanta ba abune mai saukiba.
Amma idan mun sauƙaƙashi a ranmu sai ya zame mana alkairi kamar yanda ya zamewa Zinneerah. Sai dai kuma su sauran yarenne bamuda hurumi a kansu inhar suma
tirsasu sukai ko yaudararsu. Abin na gaba shi annamimin likitan dake wannan aikin ya kamata a dakatar dashi, dan gwara ace ma’auratan dake buƙatar hakan da
kansu suka amince suka kai kansu bawai ta irin wannan hanyar dabita wagga ɗiya Zakiyya tabi ba. Wannan al’amarima malamai sunata nasiha akansa. barinsa yafi
alfanu fiye da yinsa. Dan UBANGIJI shine yasan miya gani har bai bakaba, zata iya yuwuwa rashin haihuwar sai yafi zame maka alkairi fiye da yinta. To mizai
hana bazaka dogara ga UBANGIJIN talikai harya baka ba kuma?. Sai kuma ina roƙon alfarmar ku taimaka kuje can garinmu ku wanke wannan yarinya agaban
al’ummarmu, dan inba hakaba harta mutu wannan tabon na biye da ita. Haka shima wannan yaron bazasu taɓa kallonsa da darajaba dan ɗan shege zasuke kallonsa
bayan ba haka bane. Ayi haƙuri da juna ayi sulhu dan ALLAH shine mafi alkairi a garemu fiye da mu tonama kammu asiri kodan kasancewar ku manyan mutane danmu
namu mai sauƙine iya garine kawai, idan yazu kuma mukace mun barsa zance ya ƙare. Kuko magauta sun sami abin faɗa a gareku kenan har takai shi yaron ana
goranta masa duk da kuwa ba alfasha aka aikata wajan samuwarsa ba kai tsaye”.
Harga ALLAH kowa maganar baba ta sanyaya masa ransa. Kuma kimarsa da darajarsa ta ƙaru a cikin idanunsu, hajiya iya ta shiga jera masa tagwayen addu’oi
shi da zuri’arsa kowa na amsawa da amin.
Sai da kowa ya natsa sannan mai martaba ya fara magana bayan yayi gyaran murya. “Ni a nawa hukuncin to Abdul-Mutallab da Sageer (mijin aunty Zakiyya)
duk ku saki waɗanan marasa mutuncin, kowacce ta koma masarauta sai sunyi zaman shekaru bibbiyu kafin na barsu su dawo gareku idanma kuna sha’awa kenan,
kokuma su sake auran wasu mazan suji, dan masu iya magana sunce idan kai nada tsoka taɓa naka kaji. hukunci na biyu koda na faɗa ko ban faɗaba musilinci ma
ya bama wannan yarinya yaro duk da dai malamai sunyi bayani kala-kala akan hakan, dan haka ko da wasa idan kuka ɗauka yaron nan kuka bama Farah matsayin
uwarsa ALLAH ya isa ban yafe mata ba idan ta amsa. Yaro na Zinneerah ne har abadan kuma itace zata cigaba da iko da shi matsayin mahaifiyarsa har ƙarshen
rayuwarta, kai bamma yarda koda wasa wani ya dangantashi da Farah ba zan ɗauka mataki mai tsauri koda kuwa Abdul-Mutallab ne yayi hakan. Koda alaƙa zata
shiga tsakaninta da shi sai dai ta zumunci ko matsar ubansa amma ba uwa ba. Hukunci na ƙarshe idan waɗancan da sukaima wannan ƙullalliyar yazam suma bada
saninsu bane to lallai zan kaisu kotu a bi musu kadin haƙƙinsu. Wannan shine hukuncina a matsayina na maihaifinsu”.
Kuka wiwi Farah da Zakiyya keyi musamman akan zancen sakin da mazajenau zasu musu dana haramta mata Little. Dan Farah a yau karo na farko ƙara ganin
little yasa ya shiga ranta dan kamar an ɗakko ƙaunrasa mai tsanani an dasa mata a ƙirji takeji.
Babu wanda ya iya jayayya da wanan hukuncin na mai martaba dan shine kawai zai iya zama darasi garesu. Sai dai yanda suke kuka dolene su baka matuƙar
tausayi…………..✍
[ad_2]