MAKAUNIYAR KADDARA 64

abinda suka aikata ɗin ya zama tsanin nasara ga gudan jinina. Shiyyasa akace idan kaga UBANGIJI ya jarabceka da wani al’amari ka nutsu wajen kwatanta haƙuri
dan zata iya yuwuwa wani tsanin zuwa ga nasara ne. Na yafe musu. ALLAH ya yafe mana baki ɗaya”.
A take aka shiga amsawa da amin duk cikin farin ciki. Maman sadiq da batace komaiba tun zamanta a wajen, tace, “Tabbas abubuwa da yawa sun faru an
maimaita wasu anan amma wasu bazasu maimaituba. Ni shaidace daga wahalhalun cikin nan da yarinyarnan tasha wanda da da ƙarar kwana ranar haihuwarsa da ta
bar duniya. Amma Alhmdllh, nagodama UBANGIJIN daya rayata, ya kuma kaimu ga ganin wannan ranar tunda gata a ɗakin mijinta cikin mutinci, kuma gaskiya ta
buɗe a garemu ALLAH ya wanketa tun anan dunuya. Da yaso sai ya barmu muyita kallonta da laifin har ranar tashin alƙiyama. Nima na yafe muku domin ALLAH da
wasu dalilai da Gwaggo ce silarsu (Hajiya iya) ALLAH ya yafe mana baki ɗaya ya kuma kiyaye na gaba”.
Itama godiya suka shiga mata da amsawa da amin. Kafin Hajiya iya ta fara magana.
“Tabbas dolene nima nace a yafemin ɗin bisa wani dalili, dan ƙila daban matsama Moddibo da ƙara aure ba da tunaninsu bai karkata ga hakan ba. Ni kuma ba
komaine ya sani damuwarba sai ganin yanda matarsa bata ɗaukemi da darajaba. Hakama Hindatu. dan duk da Kabeer ya fita ƙarfin faɗa aji akan yarannan tana
nuna masa iko a kansu, ko zancen auren yarinyarnan bamusan komai ba saida yazo gab. Koda yake duk ta wani tone-tone ya wuce, Moddibo ka yafemin kai da
matarka dan zan iya saka kaina matsayin silar faruwar komai”.
“Bake bace sila Granny, dan koda kikace na ƙara aure baki tursasaniba, sannan tsarin da sukazo muku dashi ya sakaki wannan tunanin kema. Dan haka
nikam kima daina neman gafarata bakimin komaiba why”. AK ne ya faɗa cikin dauriyar abinda yakeji game da jikinsa.
Mammah ta karɓe da faɗin, “Tabbar Inna ba laifinki bane, nice da wannan laifin, dan daban zurfafa da yawaba akan yaran nan da Zakiyya bataci galaba a
kainaba har nakai ga bata goyon bayaba, dan ALLAH Adnan ka yafe min kaji, ajizancine na ɗan adam da son zuciya da tsoron rasaku tamkar yanda gangancina ya
kaini ga rasa kabeer. Kishi ba hauka bane, kuma halas ne. Amma irin namu yayi muni da yawa dan muna zafafawa, da nayi haƙuri da hukuncinsa a wancan lokacin
da duk haka bata faruba na tabbata. Dan ALLAH ku gafarceni baki ɗaya. Ɗiyata Zinneerah kema dan ALLAH ki yafemin kinji, wlhy bazan ɓoye mukuba tun randa na
diro ƙasarnan naga yaron nan da kika haifa ƙaunarki data yaron ta kamani, duk abinda kukaga inayi borin kunyane kawai, amma har cikin raina son ɗanki dake
kanki ya shigeni, koda nake cewa kar Adnan ya taɓaki ya sakeki inason na gwada yanda yake sonkine kawai ba wani abuba, kuma koda ya gama tsarani bawai ban
fahimci tsaranin yayba. Sarai na san bazai iya sakinkiba wlhy, nima kuma bama zan yarda yay wannan taɓargazarba. Ki yafemin na ƙara roƙonki……”
Da sauri Zinneerah ta shiga girgiza mata kai, “Mammah dan ALLAH ki daina roƙona. Wlhy ni bakimin komaiba sai tarin alkairi kodan zama mahaifiya ga
Yayanmu da kikayi. Kuma ni kallon uwa nake miki daman, har abada kuma zan cigaba da kallonki da wannan kimar da darajar. Dan haka ki ɗauka bakimin komaiba.
Idanma kinmin na yafe miki wlhy”.
Tasowa Mammah tayi ta rungume zinneerah tana saka mata albarka. Kamar yanda zancen nata ya saka kowa dake falon murmushi, duk da ƙarancin shekarunta
ALLAH ya bata baiwar shirya lafuza masu taushi ga nagaba da ita duk da kuwa ko ba’a faɗa da gaske an tauye mata haƙinta.
Farah da Zakiyya dai babu wanda ya roƙa gafarar Zinneerah, babu kuma wanda yace dasu ƙala akan hakan, kai kowama basu roƙaba sai kuka da sukeyi
kawai. Dan haka mai martaba ya umarci AK da mijin Aunty Zakiyya da shima yana a wajen akan su basu saki. Babu wanda yace komai a falon, sai AK ne ya miƙa
hannu ya amshi takarda da biro daga hanun Baba Wambai. Haka shima mijin aunty Zakiyya.
Gani kawai sukai Zinneerah ta tashi da sauri taje gaban AK ta durƙusa. Biron daya dasa akan takardar ta riƙe da fashe masa da kuka tana girgiza kai.
Jajayen idanunsa ya ɗago yana kallonta. “Yayanmu dan ALLAH karka aikata, na roƙeka karka saketa. Kuma koba hakaba ka tausaya mata ba laifinta bane itama
tursata akayi”. Tai saurin juyawa ga mai martaba dake mata kallon mamaki hakama sauran jama’ar falon. “Abbah dan girmana ALLAH kayi haƙuri ka janye wannan
hukuncin naka koda kuwa sauran zasu tabbata. Gara komi za’a musu ai musu da igiyar aurensu kar’a rabasu da iyalansu na roƙeka Abbah. Dan ALLAH kodan
maraicinsu ai musu afuwa, wlhy na tsani naga an saki mace inajin ciwo. Granny, Baffah, Mahma, Babana dan ALLAH kusa baki, Abba dan ALLAH ku bama Abbah
haƙuri dasu Yayanmu karsu aikata”.
Yanda take kuka kamar ranta zai fita sai duk hankulansu suka tashi. Dan har suƙewa takeyi, ƙoƙarin son fisge pen ɗin AK yayi yana harararta ta sake
damƙesa da fashe masa da kuka. “Yayanmu dan ALLAH, kodan ƙyautar little da ALLAH ya azurtaka da shi ka taimaka karkayi, idan ka saketa ALLAH nima bazan
zauna da kai ba, zan ɗauke little na tafi inda bazaka sake ganinmuba wlhy”.
Kansa dake sara masa ya dafe, da wannan damar ta samu amshe takardar da biron, ta koma gaban Mai martaba ta gurfana tana cigaba da roƙonsa shi da su
baba wambai da su waziri. Sosai ta basu tausayi ta kuma sake birge kowa. dan haka hajiya iya tai ɗan murmushi da duban mai martaba ɗin da shi kansa yakejin
wani irin ƙaunar Zinneerah na shigarsa. Dan koda ƴaƴansa suka kasance masu laifi bazaiso mutuwar aurensuba ai. Sai dai kuma dolene ya yanke musu hukunci
domin yin gargaɗi.
“Inaga a amsa kukan Zinneerah dan ALLAH, za’a iyama su Farah hukunci bawai sai an katsa igiyoyin aurensu ba, dan koda abinda duk ya faru aka barsu
ya ishesu tunawa da ishara har ƙarshen rayuwa. Ayi haƙuri dan ALLAH”.
Ƙasa kawai mai martaba yayi da kansa dan yana ganin girman tsohuwar ainun, yanda yayi ɗin ne ya saka sauran ƴan falonma fara roƙonsa harma dasu AK
kansu. Ganin sun masa taron dangi ya sashi jan numfashi da dafa kan Zinneerah ya shiga jera mata addu’oi masu daraja da ake jifan mutum mai daraja dasu. Sai
da ya gama ana amsawa da amin sannan yace, “Shikenan zan janye maganar saki, amma kuma dolene sai sunje masarauta sunyi wancan zaman wlhy, sauran hukuncin
kuma tsakanina da sune. ALLAH yay miki albarka ke kuma, daga yau kema kin zama cikin jerin ƴaƴana”.
Kabbara aka ɗauka a take. Kowa na nuna jin daɗinsa da farin ciki. Daga haka Hajiya iya tai musu nasiha. Hakama baba wambai yayi musu sannan shima
maimartaba ya ɗaura tashi, daga ƙarshe aka rufe taro da addu’a saboda lokacin sallar zuhur yayi.
★★★
Ana idar da sallar azhar aka gabatar da ɗaurin auren Huzaifa da Adilah bisa alƙawarin Baffah, dan dama sun gama magana da mahaifin Huzaifa tun daren
jiya, ya kumace ya bashi wuƙa da nama dan zaman Huzaifa hakan ya ishesa dama. Shima dan baya Nigeria ne da dashi za’ai komai a yau.
Koda suka dawo cikin gida tuni labari yaje kunen kowa. Zokaga murna wajen ango da amarya dan dama sun folama juna tuni. Daga haka sukai zaman cin abincin