MAKAUNIYAR KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAUNIYAR KADDARA 64

da matan Baffah suka shirya musu, suka kuma sake tattaunawa a tsakaninsu na maza. Kamar yanda anan cikin gida suma su Granny basu gaji da sake tattauna 

zantukanba a tsakaninsu. Mahma taja su Zakiyya gefe tana musu faɗa akan ƙin neman gafarar kowa da sukayi. Ta zazzagesu tas tai gaba ta barsu batare da kowa 

ya sani ba.

      AK kam bayajin daɗin jikinsa, dauriya kawai yakeyi, hakama Zinneerah tana gadon Granny ƙudunsune dan zazzaɓi na neman dawo mata sabo ga ciwon kai na 

kukan data sha. Tanason zuwa ta gaisa da Baba ma ta kasa.

   Zuwa la’asar su maimartaba suka fara tafiya bayan ya tasa su Farah dake faman kuka gaba ya wuce dasu masarauta, harda Baba dan yanason ya shiga har 

ƙauyen Danya yayma baba rakkiya ya kuma gana da dagacin garin danya ta silar baba. Hakan yama Zinneerah data fito suka gaisa da ƙyar daɗi, yau ga babanta ga 

maimartaba wata hikima sai UBANGIJI. Shima kansa AK hakan da maimartaba yayi ya masa daɗi sosai.

    Bayan wucewarsu suma su mmn sadiq suka wuce, suma hajji Lanti tafiya sukai bayan sun sake gurfana neman gafara ga Zinneerah da AK dama su Hajiya iya 

baki ɗaya.

        Da wannan damar Mammah ta samu suka sake zama ita da Mahma dasu Baffah ta ƙara neman gafararsu da sake tattauna duk abinda ya faru. AK dai bai 

zaunaba ɗakinsa ma ya shige yay kwanciyarsa dan bayajin daɗi, ya tabbatar yau jininsa yayi ƙololuwar hawa tabbas.

     Hajiya iya ce ta hana su Mammah komawa gidan mijin Zakiyya. Tace Khalipha zaije ya ɗakko musu kayansu suyi zamansu anan har randa za’aje ga yarinyar 

datake rainon cikin a Morocco. 

    Zinneerah ma dai magani Granny ta bata tasha ta kwanta.

________________________

      *_DANYA_*

  Su baba sun iso danya da tawagar maimartaba. Inda tsabar ruɗewar da maigari yayi kai kace zai kife ƙasa. Maimartaba da kansa yau a ƙauyensa, bayan ko’a 

labari bai taɓa jin ko kusada wajen hakimi yaje ba sai dai ya aiko wakili idanma wani abune ya taso. Ai baima san ya gurfana yana kwasar gaisuwa ba. Hakama 

garin danya cikin ƙanƙanin lokaci labarin zuwan maimartaba da baba a tare ya shiga kunnen kowa harsu Inna da ke kwance rijib cikin ciwo. Dan tun zancen 

cikin Tinene dajin uwar sata da Karima ta kima na sarƙar zinarin wata hajiya da har yay silar Babawo yimata dukan mutuwa ya korota gida ta yanke jiki ta 

faɗi aketa fama har yanzun. Dan saki uku Babawo yayma Karima. Ga kuma aike daga kotu cewar Karima zata biya naira dubu ɗari huɗu na sarƙar mata bayan tara 

kuma da zaman kaso na wata shidda bayan ta yaye ɗiyarta. Ga zancen cikin Tinene ya baje ko ina na garin danya da kewaye har ƴammata sun dasa mata waƙar 

dandali. Matan aure kuwa da biyu suke zuwa barkar ƴan biyun amaryar baba dansu sake tabbatar da zancen ciki da halin da Inna ke ciki na samun ciwon ɓarin 

jiki a silar faɗuwar da tayi.

       Ga ƴan uwan amaryar baba sun cika gida daga jiya zuwa yau dan ana haihuwa baba ya kirasu ya sanar musu. A safiyar jiya saiga kusan mutane shidda 

sunzo, sauran kuwa sai daren suna. Duk abinda ke faruwa kuwa akan idonsune sai mamaki sukeyi kamar almara ko hikayoyin marubuta.

         

     Cikin ƙanƙanin lokaci ƙofar gidan maigari ya cika taf da jama’ar gari saboda kiranye da aka saka sanƙira yayi musu. Ciki kuwa har dasu Sa’a a ƴan 

kallon zuwa ganin maimartaba. Sai da guri ya nutsa sannan maimartaba ya fito. A take waje ya ruɗe yau gasu ga maimartaba. Farin ciki duk ya bayyana a 

fuskokinsu kamar shima yanda yaji daɗin yanda suka amshesa duk da basu da wani cigaban kirki a garin, zaima iya cewa baisan da zamansuba saita wannan silar. 

Sai yaji zuciyarsa ta ƙara rauni da karaya akan nauyin al’umma dake kansa.

          Bayan Matawalle ya isar da saƙon gaisuwar sarki a garesu ya gabatar da hajji lanti a gabansu tai bayani akan silar ɗaukar Zinneerah zuwa birnin 

katsina. Itama Hajiya Haule tayi bayani kamar yanda tayi a kano. Kafin Zakiyya ma da takejin tamjar ranta zai fashe tai nata bayanin akan gaskiyar dasama 

Zinneerah ciki da sukai ba ta hanyar iskanci ta samosa ba.

        Take gurin ya ƙara ruɗewa da al’ajab da mamaki. Ɗunbin tausayi da nadamar cin kashin da suka dinga ma yarinya ya ringa dawo musu a rai harda masu 

kuka. Kafin wani dogon lokaci labari ya ƙara kaiwa ga mata dake cikin gida da jama’ar sauran ƙauyukan gefensu da duk sukasan da labarin cikin na Zinneerah. 

Abinka kuma da ƙananun gari babu wanda ya manta musamman daya kasance ba’a jima da zuwa akai bikin Zinneerah ɗin ba. Bakajin komai sai ALLAH wadarai ga Inna 

asabe dasu Zakiyya. Dan su maimartaba kan sun tafi sunbar abin faɗa ga mutane. Musamman daya kasance yanzu ALLAH ya bama Zinneerah cigaban rayuwa. Ga kuma 

samakon nan a jikin Tinene da ita kanta Innar dake kwance rijif ita ba gawaba ba kuma rayayya ba.

     Ita kanta da labarin yaje mata sai gata tana hawaye zuciyarta na ƙara hauhawar zafi. Daga ƙarshe jikintane ya ruɗe sai da aka kwasheta zuwa asibitin 

cikin kusada…………..✍        

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button