MAKAUNIYAR KADDARA 65

*Page 65*
…………Ganin dare ya fara yasa Hajiya Iya tada Zinneerah, shima AK taje ta tasoshi akan suzo su wuce gida haka nan. Badan Zinneerah taso hakanba ta
miƙe, shima AK ɗin ya fito yana faman dafe kai. Kowa bai kallaba a falon yay ficewarsa duk da yasan akwai su Mammah zaune. A waje ya samu su Haneef da
little a hannu, aiko ya maƙale masa. Amsarsa yay suka shiga motar da Khalipha zai jasu dan shi bazai iya tuƙinba. Zinneerah ma da Hajiya iya ta rakota dasu
Meenal ta shiga baya.
Koda suka iso Khalipha ne ya buɗe musu ƙofar falon, daga haka ya juya yana musu sai da safe. AK ya ɗauka Little suka wuce sashensa batare daya kula
Zinneerah ba. Itama ɗin ba kulashi taiba ta shige nata sashen. (Faɗan masoya hutu????????).
Ko wanka kasa zamanyi Zinneerah tayi, tana shiga gado ta faɗa tai kwanciyarta dan barcin tafi bukata. Musamman daya kasance maganin da Granny ta
bata yana saka barci.
Shima a ɓangaren AK kwantar da little dayay barci tun a mota yayi, ya samu yaɗan watsa ruwan yasha tea dan yanajin yunwa, duk yinin yau ya gagara sakama
cikinsa abinci, basket ɗin abincin da suka bari a gidan tunna safe ya ɗauka ya bubbuɗe. jin babu abinda abincin yayi ya sashi ɗauka ya fita dashi ya kaima
maigadi yace ya badashi kar ai asararsa. Daga haka ya dawo shima yay kwanciyarsa bayan yaɗan leƙa Zinneerah yaga harma ta kwanta.
*_WASHE GARI_*
Da safe sun tashi Alhmdllh, musamman Zinneerah batajin ciwon komai a jikinta. garama AK dai jikin nasa sam baya masa daɗi. dan ko sallar asuba a gida
yayi abunsa ya koma ya kwanta. Sai kusan ƙarfe bakwai da little ya farka yana damunsa ya miƙe da ƙyar ya ɗakkosa gaba ɗaya yayo sashen Zinneerah da shi. A
lokacin tana cikin saka turaren wuta dan ta gama gyaran ko ina.
Sanye take cikin wando da riga na kayan barci farare tas, yanda suke da santsi yasa suka manne mata a jiki sosai, gashi ko bra babu a jikinta. Kallo
ɗaya yay mata ya kauda idanunsa, itama cike dajin kunyar yanda ya sameta dan batai zaton shigowarsaba takai ƙasa tana gaidashi cikin girmamawa batare da ta
yarda sun haɗa ido ba.
Amsa mata yay a daƙile yana dire little kusa da ita dan haushinta yakeji, har itace zata buɗe baki tace zata barsa saboda wasu. Wannan magana tai masa
ciwo, tanama cikin masa ciwon. Juyawarsa yay ya fice ta bishi da kallo zuciyarta na raya mata yana fushine saboda matarsa da aka wuce da ita. Haka kawai sai
taji ranta ya sosu. Ta ɗan taɓe baki tana miƙewa da ɗaukar little ɗin dake mata ƙorafin shi tea zaisha.
“Dalla yima mutane shiru abinda ka iya kenan sai cin tsiya kamar ubanka”.
Kuka ya sanya mata saboda dungure kansa da tayi. “Malam yimin shiru ALLAH kona huce a kanka”. Daga haka ta ɗaukesa suka nufi ciki dan ta masa wanka
sannan tazo tanadar musu abinda zasuci dan tacema Granny abar kawo musu abinci zata fara girki.
Wanka tayi masa itama tayi sannan, tura little tayi wajen AK ya amso kayansa, ita kuma tai ƙoƙarin shiryawa a gurguje ta fito. Sai da ta haɗa ma
little tea ta fara nema musu abinda zasuci yanda bazata takura ba. Harta gama bataji ɗuriyar little mai kukan yunwaba, hakan bai dametaba dan tasan wani
abun ya samu acan.
Kamarko ta sani dan AK na gama saka masa kaya tea ɗin ya haɗa masa da ruwan dispencer, ya haɗa masa da biscuits. Shima wankan yayi dan yanason yaje
asibiti kar abin yay masa nisa. Koda ya fito wankan rashin ƙarfin jikin ya sakashi sake komawa ya kwanta har takai barcin ya sake figarsa.
Lokacin da Zinneerah ta shigo falon da kayan abincin little kawai ta samu a falon ya barbaza filos ɗin kujera yayma falon kaca-kaca. “ALLAH ya
shiryeka” kawai ta iya cewa ta ajiye abincin a dining. Kayan shara ta ɗakko ta fara a tunaninta AK yana wani abunne a ciki. Waje ɗaya ta saka little zama
harta kammala kimtsa falon tasa turare. Ganin har lokacin shiru babu motsin dadynsa ga goma harta gota ya sata nufar bedroom ɗin a ɗarare danta sanar masa
ga abinci. Kusan sau uku tai sallama babu amsa. hakan ya sata tura ƙofar ta ɗan leƙa kanta a tunaninta koma dai baya gidan ne.
Zaune ta hangosa a bakin gado dan dai-dai ya tashi kenan saboda sallamarta. Hannunsa dafe da kansa dake masa tsananin ciwo. Jitai tamkar ta juya da
baya dan da ga shi sai boxer ne, amma ganin yanda ya dafe kansa yasata tunanin ba lafiya ba. tunda jiya dai ga a yanda suka dawo su duka, kuma tanaji sanda
yake sanarma Khalipha kansa na masa ciwo a jiyan.
Kanta a ƙasa ta ƙaraso cikin ɗakin, sai da tazo kusa da shi sannan ta rissina tana gaishesa batare data sake yarda ta kallesa ba. A yanda ya amsa
ɗin kuma sai tsoro ya sake kamata, cikin damuwa tace, “Yayanmu baka da lafiya ne?”.
Shiru kamar bazai amsaba har kusan mintuna biyu sannan ya ɗago idanunsa da sukai jajur yana dubanta. Kwalliyar tata tayi masa ƙyau, dan haka yaɗan
lumshe ido ya sake buɗewa a kanta da cewa, “Kaina ke ciwo. Haɗamin ruwan wanka inason naje asibiti”.
Sosai damuwa ta bayyana ƙarara a fuskarta. ta shiga jera masa sannu kamar zatai kuka. Shi dai kallonta kawai yake dan duk da yana cikin halin
ciwo yanda takeyi ɗin tada masa tsigar jiki take. Ga mayatattun turarurrukan ta da ƙamshinsu ke ɗaga masa hankali zuwa ga buƙatarta. Ya ɗan cije lips ɗinsa
yana komawa da baya a saman gadon ya ɗan kwanta kafin ta kammala haɗa ruwan.
Sai da ta tsaftace masa toilet ɗin duk da ba wani uban datti yay ba sannan ta haɗa ruwan, ta fito hanunta da tissue data warwaro daga can tana gogewa.
Da ƙyar ya iya yunƙurawa ya tashi zuwa bayin.
Ta ɗan sauke numfashi da fara ƙoƙarin gyara masa gadon, daga haka ta zarce da tsaftace ɗakin gaba ɗaya. Ɗan jimawa da yake a wanka yasa harta kammala
kafin ya fito, tana fesa fresheners take jiyo little na ƙwala mata kira daga falo. “Aunty! Aunty!!”.
“Oh ALLAH! Na’am”. Ta faɗa tana ajiye gwangwanin freshener ɗin. hakan kuma sai yay dai-dai da fitowar AK daga bayi. Bata yarda ta dubesaba, sai sake
amsama little kiran da yake mata tayi. Ta ɗaga ƙafa zata nufi hanyar fita taji an ruƙo mata hannu. cak ta tsaya dan tasan dai shine.
“Idan kin tafi wazai shiryani”. Ya faɗa a hankali yana jawota ta juyo tana fuskantarsa. Kasa kallonsa tai dan dagashi sai guntun towel. Ganin yanda
taketa sinne kai ya ɗago fuskar tata da ƙoƙarin saka idanunsa cikin nata. “Nazama surukinki ne?”.
“A’a” ta faɗa a hankali tana ɗan murmushi.
“Hum” ya faɗa da kama hannunta yajata suka ƙarasa gaban mirror ɗin. Duk yanda taso zamewa dole tabi umarnin sa. dan dolenta ta shafa masa mai da