MAKAUNIYAR KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAUNIYAR KADDARA 65

kanta, ta kuma ɗakko masa kayan da zaisa wanda bazai takura ba. A gaɓar shiryawane dai kam ta kasa duk yanda yaso dole ya barta ya shirya da kansa.

     Falo suka fito a tare suka sami little, baiyi tunanin ita tai girkinba, sai dai ya masa daɗi, kaɗan yaci yau kam dan da gaske bayajin daɗi, yana gamawa 

ya koma falo ya kwanta cikin kujera saboda jiri, wayarsa yace ta ɗakko tai kiran Doctor Mahmud yazo ya dubashi, dan bama zai iya driving ba. Cikin damuwa ta 

ɗakko ta lalubo masa no ɗin Dr Mahmud ɗin, yana ɗagawa ta miƙa masa wayar yay magana da shi.

       Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga Doctor Mahmud da Khalipha tare. Bayan ta gaisa dasu ta bar musu sashen saboda kallon da AK ke mata na gargaɗi dan ko 

mayafi babu a jikinta yau. 

        Koda ta koma a can tai zaman karyawa itama. Bata sake leƙo sashenba sai da little yazo ya kirata. Hijjab ta zunbula dan hanyar lafiya a bita da 

shekara. Khalipha kawai ta samu tare da shi sai Huzaifa da batasan da zuwansaba. Ta gaisa da Huzaifa daketa tsokanarta da amarya amarya. Ita dai murmushi ne 

nata kawai babu bakin ramawa.

    Ta ɗan dubi AK da akema ƙarin ruwa idanunsa a lumshe. Sannu tai masa dan ta fahimci idonsa biyune, saboda riƙe yake da hannun little dake tsaye gaf da 

fuskarsa yana masa maganar da batasan kota micece ba. Khalipha ne ya sanar mata abinda zatayi, dan haka ta juya ta sake fita ta barsu.

           ★*********★

Abu kamar wasa sai ga AK yasha zazzaɓi kwana biyu, dan sai da takai har Baffah da Uncle Ahmad sai da sukazo dubashi, hakama su Mammah dake shirin komawa 

gobe idan ALLAH ya kaimu sunzo sun dubata da sake neman gafarar Zinneerah. Yanda Mammah taketa tattalin Little sai ta baka tausayi, gashi shi saima wani 

ƙiwan wulaƙanci yaketa faman mata. 

     Shima AK ɗin sun ƙara masa nasiha da nuna masa muhimmancin yarda da ƙaddara. Mammah ta sake neman gafararsa duk da ta fahimci fushi yake da ita. Nuna 

mata yay shifa komai ya wuce, amma ita tasan bai wuce ba tunda ya kasa sakin jiki da kowa sai ɗansa da matarsa.

        Yau Alhmdllh ya tashi jikin nasa da sauƙi sosai, dan har fita yay zuwa gidansu shi da little. Bayan sallar la’asar Zinneerah na falonta na biyu 

zaune tana cire ƙumba ya shigo da sallama. Gaidashi tai da masa sannu da dawowa. Ya amsa mata yana kaiwa zaune. Ita kuma ta miƙe dan kawo masa ruwa. Amma 

sai jitai ya ruƙota. Duk yanda taso zamewa ya hanata damar hakan. Cikin wani irin kasalalliyar murya yake mata magana a kunne. “Wace irin amaryace wannan 

mai rowan tsiya nikam?”.

        Ɗan dubansa tai dan bata fahimci ina ya dosaba, ya ɗage giransa ɗaya yana kasheta da kallonsa mai sakata nutsuwa. Itama dai yau tayi dauriya da 

jarumtar kallon nasa cikin idon, da wannan damar yay amfani wajen ɗora lips ɗinsa kan tausasan nata. Sukaja numfashi a tare da lumshe idanunsu. Sai gata 

luff ta nutsu tana amsa saƙonsa. Sai da labarin ya fara canja salo kuma ta nema raina kanta. Ko saurarenta baiyiba ya ɗauketa cak yay cikin bedroom ɗinta da 

ita. Ganinfa irin na ranar yake son maimaitawa tuni ta fara tsuma da neman roƙomsa shikam baima jinta ya antaya duniyar kodumo.

      Duk yanda taso daurewa yau ma dai kasawa tai, sai da ta kaita da masa kuka, dan wannan yayan nasu bana wasan yara bane, baisan sauƙi ko sassauci ba 

har sai ya kai boader.

     Sai da ya ga ya samu kansa ya koma tsokanarta da suna ragguwa. Ita ko ta dinga tura baki har a wajen wanka da ya taimaka mata ta kuma gasa jikinta 

yanda zataji daɗi. Suna fitowa ya gudu sashensa dan kiran sallar magrib ake tayi.

      Bata sake ganin ƙeyarsa ba sai bayan sallar isha’i, ta fito domin nema musu abinci shi kuma ya shigo hannunsa ɗauke da leda alamar ya biya ta ɗakinsa 

kafin yazo nan. Zama yay da kiran sunanta, dan haka ta nufosa zata zauna ƙasa ya nuna mata gefensa. Sai da takai zaune sannan ya miƙa mata ledar. Amsa tai 

tai godiya duk da batasan minene a cikiba, tana buɗewa taci karo da waya mai ƙyau. Ai tuni jin daɗi yasa ta manta da Yayansu ne fa. Ta miƙe ta ɗane masa 

jiki tana murna.

           Murmushi yalwace da fuskarsa ya karɓe abinsa yana cusa kansa a wuyanta. “Yanzu kin ɗaneni, da an taɓaki kuma ki hau yima mutane raki”.

     Kanta ta cusa a ƙirjinsa tana dariya da faɗin “ALLAH akwai wuya Yayanmu, kai dan baka sani bane”.

     Dariya ta basa, amma sai baiyiba ya cigaba da murmushinsa yana cusa hannunsa cikin gashinta, “Ni kuma gashi ba wasa zan tsayaba ƙannen little nakeso da 

wuri, dan naga shikam ba barmana zasuyiba haka zai ringa yawo tsakanin danya, gidan Abba, gidan Baffah, london. Kinga saiki sama mana namu muma”.

      Ƙwaɓe fuska tai cikin marairaicewa. “Yayanmu ba yanzuba akwai wahala wlhy”.

     Kansa ya ɗan girgiza mata da sumbatar lips ɗinta. “Haba my Neerat ai ke jarumace tunda kika haifo Abdul-Mutallab tun kinada shekaru sha huɗu, yanzu kam 

ko ƴan huɗu ne zaki iya ai”.

       “Sai dai in zaka tayani”. 

Ta faɗa tana ɓoye fuskarta a jikinsa. Sosai yanzu kam ya ƙyalƙyale da dariya. “Mizai hana na tayaki nikam Mrs Shira, ai tare zamuyi rainon cikin muyi naƙuda 

abunmu mukuma rainesa idan ya fito”.

    Dariya sosai Zinneerah keyi itama mamaki fal ranta na Yayansu. Ashe haka yake da sauƙin kai da sakin jiki, amma yayta musu mazurai a gida.

        Washe gari suna kammala breakfast yabar gidan zuwa jigawa. Da wannan damar ta samu zaman gyara gidan sannan tai zaman kiran ƴan uwa da abokan arziƙi 

data samu nombobin wasu a wajensa. Wanda bata da shi mmn sadiq ta tura mata da su hajiya iya. Ƴan danya ne ƙarshen kira. Inda tai farin ciki matuƙa dajin 

muryar babanta. 

      A wayar tasune yake sanar mata shagalin suna da za’ai gobe idan ALLAH ya kaimu. tare da abinda ke faruwa akan Karima na zancen sarƙa data sata acan 

Kaduna aka kaita kotu, a yanzu kuma babu sarƙar babu kuɗin ga Babawo ya saketa saki har uku. Ya ɗora da faɗa mata halin da Inna take a ciki da zancen cikin 

Tinene. Harma da wanketan da mai martaba yaje yayi har danya bayan sun bar kano tare.

       Zinneerah tayi kukan daɗi tayi na damuwa tayi na baƙin ciki a wannan yinin. dan har AK ya dawo daga jigawa a jigace ya isketa. A kallo ɗaya ya 

fahimci damuwar dake tare da ita. Baice mata komaiba harta taimaka masa yay wanka yay zaman cin abinci, sai da ya kammala yaje sallar magrib da isha’i ya 

dawo sunyi zaman kallon labaran dare ya tambayeta. Da farko tata noƙewa akan ƙin faɗa ya nuna ɓacin ransa. 

       Kuka ta fashe masa da shi ta shiga basa labarin abinda duk ya faru. Shima yaji daɗin abinda maimartaba yayi. yakuma taya baba murnar samun ƙaruwa. 

Tare da jajanta abinda ke faruwa ga Inna da ƴaƴanta. Sannan ya ɗaura da lallashin matarsa ta hanyar daya dace.

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button