MAKAUNIYAR KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAUNIYAR KADDARA 65

     Kwana biyu dayin wannan maganar Zinneerah ta kira taima Baba barka da tashin baƙi dajin yaya jikin Inna yake sanar mata ai jiya AK ya aika Khalipha 

danya. Yanzu haka Inna na asibitin katsina yau da safe aka wuce da ita. Ya kuma biya kuɗin sarƙar Karima ɗin.

     Wannan zance ya saka Zinneerah matuƙar farin ciki dajin ƙaunar mijinta kuma Yayanta. Yana shigowa gidan tai masa ƙyaƙyƙyawar tarbar da bai taɓa samu 

daga garetaba. Dan yau fidda kunya tai abinta ta manne bakinta da nashi ta shiga masa salo akan karatun da yay mata. Wannan al’amari ya gigita AK musamman 

daya kasance ta cuɗe jikinta da turarukan dake neman zauta masa tunani. Yako zage wajen bata haɗin kai har sai da ta koma masa raki. 

     Sai da ya kai boader ya koma mata dariya da tambayarta wai minene sirrin?. Baki ta dinga tura masa tana zuba masa shagwaɓa. Sai da suka tsaftace 

jikinsu ta zaman masa godiya. Nuna mata yay shi baima san anyi hakaba. Maybe Khalipha ne yayi kawai.

        Tasan sarai yayi hakane dan ya goce, bawai dan abinda ya faɗa gaskiya bane.

      Haka rayuwar waɗanan ma’aurata ta cigaba da tafiya cikin aminci da kwanciyar hankali, duk da dai wataran saɓani kan gifta musu har rai ya ɓaci. 

Musamman daya zamto halinsu na kamanceceniya da juna wajen miskilancun tsiya. Little kan leƙosu kwana ɗaya biyu ya tafi, wani lokacin yana gidansu Granny 

wani lokacin yana gidansu mmn sadiq. Khalipha kuma kanje Danya shi da Dr Mahmud daya fola Sa’a tun a wajen biki batare da sanin su AK ba.

         Sunata shirye-shiryen bikin ƴammatan gidan daketa gabatowa. Adilah ma na Nigeria bata komaba su Mammah ne kawai suka tafi. 

      Bukatar komawa ganin likitan Granny yasa AK shirya musu tafiya harda little. Dan yanason zuwa shima yaɗanyi wasu abubuwa acan kafin su dawo wajen biki 

kuma.

      Zinneerah batasan da wannan shiri nasaba sai ana saura kwana biyu ya ɗauketa suka nufi Danya shi da ita da little. Wani irin farin cikine ya baibayeta 

ganin inda suka nufa. Ta kwanto jikin hannunsa da faɗin, “Oh oh thanks you so much Yayanmu”.

     Murmushi ya ɗanyi yana sake maida hankalinsa ga tuƙi. Yace, “Yayansu dai, dan kekam kin gama gane Yaya ciki dabai yarinya”.

     Kunyace ta kamata, ta maida kanta gefe tana ƙyalƙyala dariya. Little dake baya yanata harkokinsa da game da Khalipha ya saya masa shima jin dariyarta 

ya sashi ƙyalƙyalewa da tasa. Dariya suka shigayi saboda yanda yay dariyar abin dariya.

      Tarbar data bama Zinneerah ɗunbin mamaki suka samu a garin Danya, dan bama ƴan gidansu ba hatta da maƙwafta shigowa suketayi. Itako cikin mutunci 

taketa gaida kowa. Suka dinga daukar little zukatansu fal mamakin yanda aka samar dashi. Tausayin Tinene ya kamata saboda itama ta ɗanɗana rainon cikin nan 

taji yanda yake musamman a irin wannan yanayin da mutane ke tsanarka da ƙinjin tausayinka. Dan Tinene dukta rame ta lalace cikin na bata wahala. Yayinda ta 

ɗauka ƴan biyun amaryar babansu kuwa sai daɗi ya kanainayeta ta dinga samusu albarka. Cikin tsokana amaryar Baba ke faɗin. “Ai saura ke ɗiyata, dan wannan 

ƙyawun da kika ƙara ai in kaji gangami da labari”.

        “Kai Mama ni ALLAH bani da komai, kawai dai idanunki ne”.

       Yaya Gajeje dake bama little abinci tace, “Haba Zinni ai duk wanda ya dubeki yasan kinada ciki, fatanmu dai ALLAH ya raba lafiya muje musha shagalin 

suna kamar na aure”.

      Cikin shagwaɓa tace, “Kai Yaya Gajeje nifa banda komai”. Dariya suka sanya mata harda Karima da a yanzu take jin wani son Zinneerah ɗin, dan badan 

mijintaba lallai da yanzu tana birsin. Yanzu ɗinma a zuwansun nan sai da taje tai masa godiya ta musamman harda kukanta.

      AK yace karta damu, shi komai zai iya musu akan Zinneerah. Fatansa dai ALLAH ya kiyaye na gaba kuma. Baba ma ya masa godiya sosai. Sukaje kuma har 

gidan maigari ya gaishesa tare da su Baba Sabi’u.

       A firarta da Yaya Sa’a takejin batunta da Dr Mahmud. Taji daɗi tayi farin ciki. ta kuma taya Yaya Sa’a murna duk da Dr Mahmud nada mata da yara biyu. 

To amma tasan shi mutumin kirkine, dan haka ta taya ƴar uwarta farin ciki da wannan abun arziƙi.

     Inna na asibiti har yanzu tare da wata kanwarta dake jinyarta. Suma sai lokaci-lokaci suke zuwa su dubata su dawo. Zinneerah taso lallaɓa AK suje ta 

dubata itama amma tanajin tsoro, dan dataje kai masa abinci take roƙonsa ko zasu ƙarasa katsina su gaida Aunty Farah wani shegen harara daya kaɗa hanjin 

cikinta yay mata. Dole ta fito sim-sim tana dana sanin yin maganar. Itako tayine saboda sanin har yanzu Yayan nasu na ƙaunar matarsa. Yana dannewane kawai 

saboda fushin laifin da suka aikata masa. Amma Sometimes idan suna fira zakaji yakan sakkota koyin misali da wani abunta yace Farah kaza Farah kaza. Tanajin 

zafin hakan sabida kishi, amma bata ganin laifinsa. dan tasan soyayyar da yake nunawa ga aunty Farah itama ko aure ya ƙara zai iya nunawa gareta bazai 

wulakantataba. Dan tunda suke bai taɓa kushe Farah a gabantaba, bai kuma taɓa yimata wani zancen halinta mara ƙyau ba indai kaji zancen Farah a bakinsa to 

alkairintane.

         Yini guda sukai a Danya, dan basu tahoba sai gabannin magriba. Lokacin da suka shigo garin kano ana sallar isha’i.

    Washe gari kuwa nan ma da kansa ya kaita gidan Mmn Sadiq danta yini. Sunyi farin cikin ganin juna itada mamanta da yan uwanta matuƙa. Duk da kuwa a 

yanzu tana waya dasu a koda yaushe. Hakama mmn halima da Abbah tare da ƴan biyun mmn Halima da suka fara zama ƴan mata. Dan jira kawai suke a kauda Sakina 

da miji ya gagara samuwa suma su ƙara zabgewa. 

    Nanma yini tai zur dan sai dare ya aika Khalipha ya ɗakkota saboda shi ya tafi wata sabgar shi da Dr Mahmud. 

     A ranar da daddare yake sanar mata gobe idan ALLAH ya kaimu zasu wuce london su da Granny. Bazasu dawoba sai bikin su Safiyya daya gabato gab danma 

ɗagashi da akayi saboda na Adilah daya shiga ai da wannan watanne za’ayisa.

       Jin harda Granny za’a tafi yasata nuna jin daɗinta sosai. dan ita dai duk da Mammah ta nuna ƙaunarta daga baya tana shakkar matar har cikin ranta. 

Sai dai taso ace harda su Bahijja ma a wannan karon amma yaya zatai tunda aure take yanzu. Ga ssce exams ɗinsu zasu fara batasan yaya yake nufiba, amma dai 

bazatai maganaba tunda tasan ya fita sanin muhimmancin karatun ai. Suma kuma su Bahijjan zaman yaran Uncle Ahmad a gidan yanzu ya ɗebe musu kewarta sosai. 

Danfa Granny ta kafa ta tsare ta hanashi komawa. Dan kuwa dai bai shirya kara aure ba. Matarsa taci kuka harta gode ALLAH ta haƙura. Dan harma yaje ya 

tattaro musu duk abubuwansu masu muhimmanci da yoma yaransa transfer ɗin makaranta zuwa Nigeria. Manyan ne kawai dake jami’a zasu koma su 

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button