MAKAUNIYAR KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAUNIYAR KADDARA 66

 *Page 66*

…………Washe gari da yammaci jirginsu ya ɗaga zuwa Birtaniya. Inda al’amari yaso ƙwaɓema Zinneerah. Dan tamkar jira jirginsu na ɗagawa amai ya ringa 

taso mata. Ganin yanda taketa rintse ido da yamutse fuska yasa AK taɓata. Ido ta buɗe da ƙyar tana dubansa. “Lafiya dai?”. Ya tambaya cikin kulawa.

      “Yayanmu amai nakeji wlhy”. Ta faɗa da ƙyar tana danne bakinta da hannu. Cikin mamaki yace, “Amai kuma?”. Kanta ta ɗaga masa tana miƙewa da sauri 

domin zuwa toilet. Dole shima ya miƙe yabi bayanta, Hajiya Iya na tambayarsu ko lafiya ma basu jitaba.

       Sosai ta jigatu wajen yin aman, sai da ya taimaka matama sannan suka fito. Ganin yanda duk ta jigata hajiya iya ta shiga salati. “Inno baki da 

lafiyane dama aka ƙirƙiri wannan tafiyar dake haka?”.

       Kanta taɗan jujjuya mata da ƙyar, murya a sanyaye tace, “A’a Granny lafiyata lau, kawai yanzu ne dai na dinga jin aman”.

        Khalipha dake mata kallon tsaf ya ɗauke kansa yana murmushi da gyarama little dake jikinsa yana barci zama. Hajiya iyama kallon tsaf takema 

Zinneerah ɗin har wasu mintuna. Kafin tai murmushi da faɗin, “To ALLAH ya rabaku lafiya, ya inganta kuma”.

       “Amin” Khalipha ya amsa mata. AK da duk bai fahimcesu ba ya kalli hajiya iyan sai dai baice komaiba. Harara ta zuba masa tana mita. “Ka wani tsareni 

da ido minaci ban bakaba to?”.

      Ƙara tsuke fuskarsa yay yana ɗauke kai gefe batare daya tanka mataba. Sai dai har cikin ransa waswasin maganar tata yakeyi. Ya kwantar da Zinneerah 

jikin kafaɗarsa yana gyara mata mayafinta. Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga barci yay awan gaba da ita. Itace bata farkaba sai gab da zasu sauka.

     Abin mamaki sai ga Mammah tazo da kanta ɗaukarsu. Cikin girmamawa kuma ta gaida Hajiya iya tare da rungume Zinneerah da duk alamun rashin lafiya ya 

bayyana gareta. Khalipha ma cike da kulawa ta amsa masa gaisuwarsa tana dungure kan little da yaƙi zuwa wajenta ya maƙale Khalipha ɗin.

        Har cikin rai AK yaji daɗin canjawar mahaifiyar tasa. Sai dai bai nunaba ko’a fuska. Tunda ya gaishetama sai ya ɗauke kansa ya maida ga waya.

        Sun iso gidansu da suka samu ƙal an gyara, ya kuma san aikin Mammah ne da Mahma. Nanma yaji daɗi. Hajiya iya ɗakin data zauna wancan karon ta sauka. 

Khalipha ɗakinsa. AK da Zinneerah ɗakinsa. Dan ɗakin Farah ma a rufe yake bai kuma nuna alamun son a buɗeba.

       Wanka ya taimakawa Zinneerah tayi ta kwanta dan zazzaɓi ne rijif a jikinta. Ga yunwa na cinta dan bataci komai a jirgi ba. Hakan yasa AK tsareta taci 

abincin da Mammah ɗin ta kawo musu. Da ƙyar tai lauma uku, sai gata hanyar toilet da gudu. Duk binta sukai da kallon tausayi, AK idonsa ya kaɗa yay jajur, 

dan shi ya rasa wannan amai na minene?. Bayan ya taimaka mata ta fito ya kwantar da ita sannan yazo falo yana cema Khalipha yazo suje asibiti dan shi wannan 

amai ya rasa na miye ko wani abu taci ya bata mata ciki.

         Dariya ta kusa suɓucema Khalipha akan wannan zance, a ranaa yace, (Waken daka batane Yayanmu ya bayyana kansa) a fili kam sai yace, “Uhm ai Yayanmu 

bara dai na duba mata wani magani kozai taimaketa, amma wannan amai ai na farin cikine bana ɓacin ciki ba”.

       Fuska ya ɗaure tamau yana hararsa, “Shi aman har abin sone?”.

       Mammah da itama dariya ke cinta tace, “Barma yarona mazurai malam, ai gaskiya ya faɗa wannan amai abin so ne, dan kuwa dai na rabone sai dai muyi 

fatan ALLAH ya sauketa kafiya”.

       Karon farko AK ya ƙwalalo idanu waje yana kallon Hajiya Iya da Mammah dake dariya, ya maida ga Khalipha daketa ƙoƙarin ɓoye tashi. “Nikam ku fiddani 

a duhu, kuna nufin ciki ne da ita komi?”.

       “Tabbas hakane Yayanmu, Congratulations”. 

    Kasa motsi AK yayi dan alja’ab ko ruɗani zai ce. Sai gani kawai sukai yakai gwiyawunsa ƙasa yay sujuda ga UBANGIJIN talikai mai badawa ga wanda yaso a 

kuma lokacin da yaso, kafin ya koma gaban Hajiya iya ya rungumeta, ya saketa itama Mammah ya rungumeta, kafin ya koma kan Khalipha.

     Yana sakinsa ɗakinsa ya nufa cikin sassarfa, cikin barci Zinneerah taji an mata wata lafiyayyar runguma ana sakar mata kissis tako ina a jikinta. Ta 

buɗe idanu da ƙyar tana kallonsa. Jin godiya da kirarin da yake jerama UBANGIJI tare da addu’ar ALLAH ya sauketa lafiya ya sata fahimtar lallai zancem su 

Yaya gajeje ya tabbata cikine da ita, hawayene suka silalo mata na jin daɗi da tausayin kai. Tayi farin ciki dan tasan koba komai mutane da yawa zasuyi 

farin ciki ta silar wannan cikin, sannan ta tausayama kanta dan tasan da wahala karatunta bai salwantaba.

       Aman daya taso matane ya sakata samu AK ya saketa ta nufi toilet da gudu. Wani irin tausayinta da ƙaunartane ya kamashi ya dafe kansa yana mai jin 

kamar inama ace zai iya rage mata wani yanki na raɗaɗin da takeji.

             Khalipha ne ya fita dole ya samoma Zinneerah maganin dazai taimaketa ta ɗan huta da aman duk da dai yasan baizama lallai ta daina duka ba. 

Cikin amincin ALLAH kuwa tana sha sai barci. Daga haka suka cigaba da farin cikinsu, yayinda labari har ya kaima ƴan Nigeria.

        Zo kaga murna wajensu Meenal da dariyar mugunta wai su Zinneerah an cika zalama, daga shiga harta ƙumso. Sunji inama zasu iya samun wayarta su 

baɗaɗeta da sheri.

    Mammah ma cikin farin ciki ta komawa Mahma da wannan daddaɗan labari. Sosai itama tai farin ciki da shiga jerama Zinneerah addu’ar lafiya mai inganci. 

ta sake ɗorawa da yima Mammah nasiha kamar yanda takeyi kullum yanzu tunda suka dawo. Hakkanne ma ya ƙara sakama Mammah nutsuwar zuciya da sake duƙufa neman 

gafarar ALLAH.

       

      Sabon tattali Zinneerah ta fara gani a london hannun AK da mahaifiyarsa da Mahma. Hajiya iyama duk da tana ƙarƙashin kulawar likita tana binta da 

addu’a da dabarunsu na tsoffi. Dama little tun kwana biyu da zuwansu ya koma gidansu Mammah ɗan gata. Hakan yasa AK samun damar baje sharafin soyayyarsa a 

cikin gidannan. Dan Khalipha na musu kawaici da basu fili yaje yay zamansa wajen Hajiya iya susha hira.

     Ita kanta Zinneerah ɗin shegen ƙwaɗayin da cikin yazo mata da shi yasata sake nanuƙema AK, dan babu abinda tafi ƙauna daso kamar ƙamshin turarensa da 

kasancewa dashi. Randa tai waya dasu Bahijja tasha Sheri, hakama su Sa’a nata tsokanarta.

    Ita dai babu baki dan ya mutu murus. Suna cikin sati na uku da zuwa jikinta yay ɗan mata ƙarfi irin na mai ciki, yau lafiya gobe jangal. Gyaran ɗakin 

nasa ko nace nasu tai ƙoƙarin yi, tanayi tana ɗan hutawa harta ga yay mata ƙal. Tana cikin gyaran ne sai ga idonta takai kan tsohuwar wayarta da aka sace a 

1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button