MAKAUNIYAR KADDARA 66

ɗakin hajiya iya. Mamaki yasata jujjuya wayar tana kallo dason tunani yanda akai tazo London, london ɗinma ɗakin Yayansu.
“Malama miya kai idonki nan?”. Taji an faɗa a bayanta cikin dakakkiyar murya. Tasan Yayansu ne, dan haka ta juya fuska a ƙwaɓe tana kallonsa da
cigaba da juya wayar a hannunta. Takowa ya ƙarasa yi cikin ɗakin yasa hannu ya amshe wayar fuska a tamke. Ya ɗaga ƙafa zai juya ta riƙo hannunsa da faɗin,
“Wai Yayanmu dama kaine ka sacemin waya?”.
Harga ALLAH yanda tai maganarne yay matuƙar bashi dariya, duk yanda yaso cigaba da pretending ɗin mazuran nasa sai gashi ya saki murmushi da hararta.
Ya dungure mata kai yana cije lip ɗinsa na ƙasa.
“Yarinyarnan kin fara rainani ALLAH. Ni nema ɓarawo ko?”.
Hannu tasa ta rufe fuskarta tana murmushi. “Nidai bance dakai barawo ba. Amma idan ta gaskiya za’ sace wayarnan akai na nemeta na rasa”.
Cak ya ɗagata da ƙasa yay saman gado da ita yana faɗin, “To bara na nuna miki ba satar waya kaɗai na iyaba yarinya”. Ya ƙare maganar da tura hannu
cikin ƴar fingilar rigar jikinta da iyakarta cinya. dama ta sakatane dantayi aikin a sake babu takura. Dariya ta shiga ƙyalƙyalewa tana faɗin, “Na tuba wasa
nakeyi ALLAH”.
Kobi takanta baiyiba ya lula da ita duniyar kodumo, dama ita kam duk sanda ya taya tana maraba, inma bai kawo kansaba ita zataje.
Sai da suka samu nutsuwa aka koma firar waya. Babu kunya yake sanar mata ai tun randa Farah taje Nigeria lokacin da take bama su Mas’ood Number ta yay
ƙudirin rabata da wayar, sai dai bayaso yayi gatse-gatse su Granny su saka masa ido ko Khalipha ya fassara abun da wani abu daban. Shiyyasa yabi dare ya
sace batare da sanintaba. Dan tana gama waya dasu maman sadiq ta fita tarbosu ya ɗauke wayar yasa a aljihu, ya fito da nufin barin gidan yaci karo da fuskar
little.
Jikinsa ta faɗa ta rungumesa tana dariya. “Kai Yayanmu amma ranar harda tambayata ina take? Sannan duk yanda kaga ina zaune babu waya bakaji tausayina
ba”.
Hancinta yaja yana murmushi, “Uhmyim, salon na barki ki riƙe wani yaymin fashi da makami. Na tabbata Khalipha nema zai fara shiyyasa nai azamar yin
maganinku, dan bana haɗa takara da kowa nikam. Duk abinda zuciyata taji tana muradi nawane ni kaɗai insha ALLAH. Dan tun randa kikaimin ihu a ɗaki da kirana
aljani kikai wuff da tunanina da zuciyata, shiyyasa duk motsinki yazama akan idona”.
Ƙarara mamakin maganganinsa suka bayyana a fuskar Zinneerah, sai ga hawaye na cika mata ido, batama san ta ɗane jikinsa da haɗe bakinsu waje gudaba
dan daɗi.
Soyayyar Zinneerah da AK abin sha’awa. Gwargwadon iko yana bata kulawa. kuma yana so da kaunarta. Sai dai soyayyarta sam bata rufe idonsa ya manta
da Farah ba. Tana nan maƙale a ransa yana kuma son kayarsa. Babban fatansa ALLAH ya shiryeta ta gane gaskiya a duk sanda zata sake dawowa rayuwarsa ta dawo
a Farah dinta da suka shinfiɗa ƙyaƙyƙyawar rayuwa a baya. Ya kuma yafe mata daga ita har Mammah da Zakiyya, dan koba komai sun zama silar mallakar Zinneerah
a rayuwarsa, tare da kusantashi da ahalinsa. Da kuma samun dai-daito tsakanin Mahaifinsa guda biyu, abinda tayta fata a tsahon shekaru amma ya gagara.
______________
Haka rayuwar London ta cigaba da tafiya cikin jin daɗi da farin ciki, sai dai wataran saɓani da ɓacin rai kanɗan gitta tamkar yanda akasan kowanne
gidan ma’aurata. Amma lallai bazasu taɓa iya mantawa da rayuwar london ba dan rayuwace mai tsayawa azuciya garesu. Anci soyayya kamar babu gobe.
Sunada wata ɗaya a london matar dake ɗauke da cikin da aka dasa mata ta Morocco ta haihu, sai dai abin ƙaddara ta haifi yarinya mace babu rai, abinda
yasa zancenta baiyi tsaho ba ta tabbatar ma su Baffah cewar da amincewarta su Zakiyya sukai komai, ko yanzu suka shirya kuma zata ƙara ɗauka musu wani cikin
tunda wannan batazo da rai ba. Godiya kawai sukai mata da bata wasu kuɗaɗe suka barota.
Duk da kuwa AK yaji baƙin cikin ta yanda aka samar da ɗiyar itama sai da yay hawayen rasuwarta lokacin da aka turo masa hotonta a waya abin sha’awa.
Ya sunbaci wayar da jerama UBANGIJI kirari da addu’a a gareta da sauran al’ummar musulmi baki ɗaya. Zinneerah kanta sai taji yarinyar ta shiga ranta. Hakama
Hajiya iya dasu Mammah. To amma yaya za’ai da hukuncin ALLAH sai haƙuri.
Watansu biyu cif suka dawo gida Nigeria domin halartar bikin ƴaƴa bakwai daga zuri’ar Abdul-Mutallab Shira. A lokacin cikin Zinneerah nada watanni
huɗu cif. Ya ɗan turo abinsa duk mai lura zai iya ganinsa.
Aiko sai ta dinga ƙunshe-ƙunshe musamman da taje gidan mmn Sadiq. aiko su Meenal suka dinga mata dariya. Taso zuwa duba Inna kafin a shiga hidimar
bikin amma AK ya hana, acewarsa ta bari a gama biki sai suje dan akwai maganar Dr Mahmud ma da Sa’a a ƙasa.
Kamar yanda ya umarceta da haƙurin haka ta haƙura aka shiga shagalin bikin su Abidah da aka shiryama bidi’oi kala-kala, danma AK ya zaftare wasu a
ciki yanata faɗa.
Ranar ɗaurin aure a bazata sai ga sunan Khalipha a cikin anguna. An zarga masa igiya uku da ɗiyar Uncle Ahmad Raheenat (Noor). Kowa kam yayi farin ciki
da wannan haɗi musamman ma Uncle Ahmad. Shima dai ango da gaske yanaso dan ƙiri-ƙiri ya nuna farin cikinsa. Abin sauƙin ma shima yanada gidansa dama da yake
gini, ƴan abubuwane kawai suka rage a ƙarasa dan haka aka hau sauran aiki babuji babu gani. Matar Uncle Ahmad tayi baƙin cikin wannan haɗi itakam, sai dai
babu yanda zatai dole ta haƙura. Dan dama taƙi sakin jiki da matan gidan sam. Suko da yake ba kanwar lasa bane duk sai suka watsar da ita suma suka cigaba
da sabgogin gabansu.
A bikin nan dauriya kawai Zinneerah keyi dan batajin daɗin jikinta, hayaniyarma sam bataso, shiyyasa lokuta da dama zaka sameta can gefe a killace.
Hakan sai yayma AK daɗi dan bata halarci bidi’a ko daya ba da akai garama kamu da akayi anan cikin gidan. Ana saka kiɗa kuwa sai da tabar gidan saboda ciwon
kai mai tsanani. Can gidansu ta koma tai kwanciyarta ta hutama ranta.
Ansha shagalin biki harna kwanaki uku aka miƙa amare ɗakinsu. Adilah lagos, Safiyya Abuja. Sauran kuma Ni’ima da Abidah duk anan kano ne, sai Noor da
aka bari sai nan da kwanaki uku an kammala aikin gidan Khalipha.
(To amare da angwaye ALLAH ya sanya albarka ya kawo ƴan dugwi-dugwi iyalan baba).
Washe garin da aka shashshare daga bikin nan kuma aka kai kuɗin auren Sa’a danya. Inda baƙi suka sami tarba ta mutunci da girmamawa. Inna ga dama
ta samu amma babu halin damawa, sai hawayen zuci takeyi.
Dan tuni aka maidota gida. Sai dai a duk sanda ta kalli Tinene da tsohon ciki ranar sai ciwonta ya rikice. Hakan yasa suka yanke shawarar maida Tinene