MAKAUNIYAR KADDARA 66

gidan Gwaggo laritu harta haihu, dan an ajiye magana randa ta haihu za’a ɗaura mata aure damai cikin tunda ya amsa nasane.
Daga kai kuɗi baba yace shikam dai baimaga wani abun jeka ka dawo ba a ɗaura aure kawai a huta. Zuwa wani satin ta tare ɗakinta taje tai haƙuri tamkar
kowa. Hakan yama Dr Mahmud daɗi, hakama su Baffah da suka kai kuɗin. Nanko take aka zarge igiya uku tsakanin Sa’adatu Sulaiman Danya da Dr Mahmud Dawood.
Zokaga baki wajen ango. Aiko AK ya dinga masa sherin kurame yana ramawa shima kamar yanda yay masa. Dan bazai fito kai tsaye yay maganaba sai dai yayi a
fisge ya tsuke baki cikin basarwa tamkar bashine yayi ba.
Cike da farin ciki suka dawo kano da wannan labari, Zinneerah kam tafi kowa murnar wannan al’amari dan har kukan daɗi tayi.
Cikin amincin ALLAH sati na zagayowa akai tariyar Sa’a. sai dai Zinneerah bataje Danya ba dan batajin daɗin jikinta kam, Khalipha ma tasa amaryar ta
tare a nasa gida da aka kammala. Yanzu kam sai dai mu cigaba dabin kowa da fatan alkairi.
Tun bayan tariyar Sa’a komai ya sake lafawa, Khalipha ya koma London shi kaɗai domin karasa karatunsa. Zinneerah ma cikin ƙarfin hali AK ya sata
zana exam na November/December. Tasha wahala saboda laulayin dake damunta, amma babu laifi tayi ƙoƙari Alhmdllh, sai fata da addu’ar fitowar ƙyaƙyƙyawan
result.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Zinneerah na rainon cikinta dake ƙara fitowa yana wahal da ita, duk ta rame sai haske data ƙara kam masha ALLAH.
Yanda wahalar tai mata yawa ne ga aikin gida ga little ya fara makaranta, dan yanzu yafi zama anan fiye da ko ina, yawonsa sai weekend, ga gida shiru ita
kaɗai yasa Hajiya iya cemasa ya maidota nan gidan sai ta haihu.
Babu wani ɓoye-ɓoye ya ɓata ransa. Dan shi dai yafison su cigaba da lallaɓawa a hakan har ALLAH ya sauketa lafiya. Tunda dai bawai kwance take rijif
ba. Aikin gida da lalurarsa girki da sauransu duk tanayi. Fitace kawai bata cika sonyi ba dan wahala take sha sosai koda kuwa zuwa gidan su Granny ne kawai
tayi ko gidan mmn sadiq. Shiyyasama ta tattara kowanne yawo ta ajiye.
“Ikon ALLAH, wai ka cika baki da iska! Bazaka maidotan bane komi kake nufi moddibo?”.
Shiru yay mata kamar bazai tanka ba, sai da yaja wasu sakanni ya dubeta yana ajiye wayar hannunsa. “Granny ki fahimta mana dan ALLAH, taya yarinya na
gidan mijinta ace ta taso ta baro. Wazai kula damu ni da Abdul-Mutallab to?”.
“Owoo, sai ta zauna zaman kula da ku ita kuma ta kashe kanta. Kana ganin yanda duk jikinta ya koma ko abincin kirki bataci sai yame-yame”.
“Granny duk nasan da waɗanan matsalolin kuma suna damuna wlhy nima, ina kuma yin iya bakin ƙoƙarina na ganin na bata kulawa nima, kuma Alhmdllh jikin
natama ya fara sauƙi. Kawai dai idan kin yarda a samo wata ta zauna da ita ni ko nawane zan biya. Kokuma ke ki koma can dan ALLAH ”.
“Wa? Kama kanka. Kawai sai naje ƙososo na zauna muku a gida raba kanka malam”.
Murmushi yayi a ransa yana faɗin, ‘Ai wlhy ke zan lallaɓa kije madam, nasan maganinki ai’. A fili kam sai yay mata shiru, daga ƙarshe ma ya miƙe yana
faɗin, “Bara naje na ɗauka Abdul-Mutallab a makaranta”.
“ALLAH ya kiyaye ka gaishesu”.
Zinneerah na falon farko na sashenta a kwance cikin kujera barci ya ɗan fara figarta daga charting dasu Meenal suka shigo. Kamar yanda Little ya saba duk
da kuwa yanzu ya ƙara girma da wayo ga shegen miskilanci kamar sunyi kaki sun ajiye ya nufeta da gudu. Yana ƙoƙarin faɗa mata a jiki AK ya ɗagashi sama dan
yanayinta ya nuna masa batajin daɗin jikin. Kuma lafiya lau ya fita ya barta.
Itama ajiyar zuciya ta sauke ganin ya hana little ɗin faɗa mata a jiki. Ta yunƙura ta tashi zaune tana musu sannu da zuwa. Amsawa yay idonsa a kanta
yana kaiwa zaune kusa da ita little a jikinsa.
“Jikin ne kuma?”.
Fuska Zinneerah taɗan yamutse tana kamo hannun little ɗin. “Kawai dai banajin ƙarfi ne amma babu inda kemin ciwo, garama tashin zuciya daketa damuna tun
cin kifin nan na jiya da naci”.
Tausayintane ya sake kamashi, musamman daya tuna yanda taita damunsa da maganar kifin. harma ya dawo gida jiya da nufin bazai sake fitaba ta takura
sai da ya fita kusan goma na dare ya nemo mata kifin, gashi kuma taci ta kasa zaman lafiya.
“Sannu ALLAH yay miki albarka ya saukeki lafiya. Bara na taɓa Mahmud naji kozaki iya shan wani abu dazai baki nutsuwa”.
“Yayanmu kama barshi zai bari dan kansa. Dan nayi waya da Yaya gajeje tace na samu ɗan kanwa kaɗan nasa a ruwa na sha zai faɗa min”.
Kafin yace wani abu little da yay kamar ba saurarensu yakeba yace, “Aunty sorry, idan kika haifa mana babynmu zan kaiki makka”.
Dariya zancen nasa ya basu, dan haka suka murmusa AK na shafa kansa. “ALLAH ya tabbatar ɗan albarka. Yanzu ka muje na maka wanka kaga aunty yau babu
kanta”.
Kansa ya ɗaga masa. Zinneerah tace, “Kama barshi zan iya masa. Bara kaima na haɗama ruwan wankan ga abinci nan na shirya”.
“Kina fama da kanki kika wani kama abinci? Nace miki duk randa baƙyajin daɗi basai kinyi ba tunda ga gidan Granny sai a kawo daga can”.
Murmushi ta ɗanyi da kama hannunsa dan ta tura little ɗaki ya kai kayan sa. Ta kwanto jikin hannunsa tana duban ƙyaƙyƙyawan fuskarsa. “Yayanmu nace
makafa bawani ciwo nakejiba ALLAH. Kuma idan ban motsa jikin ai sai wani kuma ciwon ya taso”.
Kanta ya shafa yana rungumota da ƙyau jikinsa. Ya sumbaci laɓɓanta da goshinta yana jera mata addu’a. Itama hannunsa ta sumbata ranta fes ƙaunarsa na
ƙara shigarta jini da ɓargo.
Kwana biyu dayin haka sai ga Mahma daga london. AK yaji matuƙar daɗin wannan zuwa nata, dan dama lokacin bikin su Adilah ta tabbatar masa da cikin
Zinneerah ya shiga watanni bakwai insha ALLAH zatazo Nigeria. To shikam ya ƙudiri tunda tazo riƙeta zaiyi har sai matarsa ta haihu.
Sosai Zinneerah ma ta nuna farin cikinta sosai na zuwan Mahma. Dan-danan ta gyara mata ɗayan ɗakinta na falon farko duk da dama fes yake. Bakuma wani
amfani take da shiba garama da ƴan Danya sukazo tariyarar Yaya Sa’a sun kwana a ciki.
Itama Mahma taji daɗin yanda suka tarbetan, tare da ɗunbin tausayin Zinneerah daketa fama, dan ga cikin nata yayi girma sosai Alhmdllh kamar ba ɗan
wata bakwai ba. Kasama haƙuri tayi sai da tace, “Anya cikin nan ba ƴan biyu bane kuwa a cikinsa?”.
Cike da kunya Zinneerah tai ƙasa da kai tana murmushi kawai. Sai AK dake saurarensune yace, “Ƴan biyu kuma Mahma?”.