MAKAUNIYAR KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAUNIYAR KADDARA 67

      Iskeshi tai yana zuba abincin da kansa. Batai maganaba ta matsar da little kusa da shi ta zauna, “Ina waje. ciwon Alhaji?”. Ta faɗa tana kamo ƙafar 

little. Nuna mata yayi, ta buɗe man zafin ta shafa masa yana wani shii da baki da yarfar da hannu. “Daddy kace tayi a hankali zafi”.

       “Oh ALLAH, ALLAH yaron nan saika kashe auren da babu soyayya, yanzu shafa maganinne da zafi?”.

          Zancen nata ya bama AK dariya amma sai ya gimtse bai yiba. Yadai kamo hannun little ɗin yana bata amsa a daƙile. “Dama can babu soyayyar ne ai”.

     Tasan da biyu ya faɗa, dan haka taja bakinta tai shiru. Sai dai ta cigaba da kallonsu yanacin abincin yana bama yaronsa har suka kammala.

      Bai wani jima da gamawarba ya mike yana kallon agogo. “Saifudden zai kawo muku cefane. Dan bazan dawo ba sai dare”.

     Mikewa itama Zinneerah tayi da faɗin, “ALLAH ya saka da alkairi ya kara buɗi, miza’a dafa maka da daren”.

      Kallonta yay cikin ido sonta da buƙatarta na ɗawainiya da shi, yaja numfashi da duban inda little yake. Ganin hankalinsama ba’a kansu yakeba sai ya 

sake kallonta. “Abinda nakeso a dafamin kam ai ba bani za’aiba. Sai dai nayi manage da tuwo”.

     Murmushi tayi tana maida kanta gefe dan tasan ina ya dosa, ta hau tattara kwanikan, “Uhm ni Yayanmu ALLAH fitina kake ƙarowa kullum, na kawo mafita 

kuma kaji haushina”.

       “Ke dai kika sani” ya faɗa yana nufar ƙofa.

      Murmushi kawai tayi ta cigaba da abinda take. Sai da ta kammala ta tisa ƙeyar little da baima lura da fitar Daddyn nasaba ta rufo sashen. A sashenta 

ta samesa zaune suna gaisawa dasu Yaya Gajeje ƴan biyu duka na’a jikinsa yana kallonsu zuciyarsa fes da farin ciki. Inda yake little ya nufa ita kuma ta 

nema waje ta zauna. Ya ɗan jima a falon suna maganar jikin Inna daya fara lekawa tana barci dasu Yaya Gajeje kafin ya basu yaran da musu sallama ya fice, 

bayan ya jefeta da wani kallon duk randa na kamaki. Murmushi mai sanyi kawai tai masa da rakashi da addu’a.

      Shima daga nan sashen Farah ya shiga inda ya samu su Mammah na karyawa. Sun gaisa nanma yaɗan zauna suka taɓa hira sannan yay musu sallama yabar 

little anan ya fice.

       ★★★

Daga ranar Zinneerah bata sake masa zancen Farah ba har ALLAH yasa sukai arba’in. A randa tai arba’in ɗin kuma su Mammah ke shirin tafiya katsina duba su 

Farah daga can su wuce london. 

         Gaba ɗaya Zinneerah sai ta shiga damuwa. Dan zamansu a gidan ba ƙaramar shaƙuwace ta shiga tsakaninsu ba. Ganin shine zai kaisu katsinar ta sake 

daurewar masa zancen dawowar Farah sai ya balbaleta da faɗa, duk da tasan bayason wargi bata taɓa ganin fushinsa irin yau ba. Ita kuma yanda yake mata ihu 

akai yasata fara kuka.

      Suna haka Mammah ta shigo falon. Saurin share hawaye Zinneerah tayi tana ƙaƙaro murmushi da yima Mammah ɗin dake binsu da kallo sannu. Daga haka ta 

zame ta gudu ta barsu, dan tasan tunda Mammah din ta shigo nan da kanta magana zatayi da shi.

      Da kallo tabi Zinneerah harta fice kafin ta maida ga AK dake ta wani bata fuska. “Abdul-Mutallab mi kaima yarinyarnan?”.

       Guntun tsaki yaja yana murza goshinsa. “Mizan mata kuwa Mammah, itace da neman fitina kawai”. 

     Shiru Mammah tai tana kallonsa cike da nazari, sai kuma taɗan girgiza kanta da cewa, “Fitina kamar ya? Ai kowa Yasan Zinneerah bata da kwaramniya, dan 

nidai a zamanmu gidan nan banga wani abun ashsha daga garetaba sai dai ajizanci irin na ɗan adama kawai. Amma yarinya mai kawaici da kunya ga haƙuri. Sai 

dai idan kai ne da laifin tunda sarai na san halinka bawai baƙona bane. Miya haɗaku?”.. 

         “Nifa Mammah babu abinda nai mata. Kawai ta isheni da zancen Farah ne”.

      Kallonsa kawai Mammah keyi dan maganar yanayintane da faɗa sosai. Ta sauke numfashi da gyara zamanta. “Abdul-Mutallab nasan Farah mai laifine tabbas, 

amma karka manta harda gudunmawarmu, kuma maganarta da yarinyarnan take maka tasan kantane. Dan wannan haline irin na mutanen ƙwarai da sake tabbatar maka 

ita mai tarbiyyace da hangen nesa. Ni bazance dole ka dawo da Farah gidankaba, amma zan baka shawarar ka daina ƙuntata yarinyarnan akan abinda ba laifinta 

bane saima alkairi da takeson ɗoraka akai. Ita rayuwa komai ɗan haƙuri ne ai. idan akai haƙurin sai komai ya zama labari wataran”.

       Shi dai kansa na ƙasa baice mata komaiba harta gama zancen Farah da Zinneerah ta ɗakko abinda ya shafesu sannan ya tsoma baki.

    Duk da Zinneerah tasan su Mahma basu rasa komai na rayuwaba sai da ta shirya musu tsaraba domin girmamawa. Musamman turarurrukan khumrah dana wuta da a 

koda yaushe suke yaba kamshin a jikinta da gidanta. Hakan yasa tasa Hajiya Falmata ta haɗa musu na musamman akai musu packaging nashi. 

    Sai gata harda ƙwalla da zasu wuce. Bama ita ba hatta su Yaya Gajeje sunji babu daɗi. Inna ma da take ɗan magana yanzu kuma takan ɗan motsa jikinta 

tafiyace dai batayi sai da ta nuna alhinin tafiyar tasu, dan kullum sai sun shiga sun gaidata sau uku a rana babu fashi.

       Duk yanda Zinneerah ke share hawaye AK na kallonta ta mirror. Yay ɗan murmushi yana cizar lip ɗinsa dan yau kam yasan ango yake tunda Mahma ta ɗaure 

mata ƙugu sai da tai arba’in duk da ba haihuwa tayi da kanta ba. 

      Baisan Mahma ta masa wayo bane tanata gyare masa Zinneerah ɗin a ɓoye. Ga gyaran Hajiya Falmata datake ɗorata a layi, hakama Hajiya Iya kullum cikin 

faɗa mata dabaru takeyi. Ita kanta tasan idan taje hannun boss din nata sai ta yabama aya zaƙinta. Shiyyasa yau duk take a tsure.

   Kasancewar da little ya tafi suna wucewa mai ƙunshin da zatai mata tana isowa. Ƙunshi akai mata na gani na faɗa na jan lalle da baƙi, Yaya Karima ta 

yarfa mata kitso kananu da ya fiddo mata ƙyawunta sosai musamman yanzu data yi wani bulɓul da ita tamkar ba itace tasha fama da rama lokacin cikin ƴan biyu 

ba.

        Kasancewar basu zauna wasaba kamar wasa kafin la’asar suka kammala komai tai fes da ita. Dama tunda ta fara zaman jegon nan take dilke jikinta da 

kayan gyaran fata na musamman da Hajiya Falmata ta haɗa mata ga kuma na Mahma. A gurguje ta shiga gyaran sashe. AK duk da bawani ƙura yayi ba. Sai da ta 

tsaftace komai yay mata yanda takeso ta baje kalolin ƙamshinta masu rikitashi. Sanda ta dawo sashenta ma su Mama A’i sun gyare ko ina sai ƙamshi yake. 

       Waya tai zamanyi da AK ɗin taji kosun taho. amma yace mata yana dai shirin tahowar. Taji daɗin haka dan ta samu damar shiga kitchen kenan ta haɗa 

abinci da kanta. Dan tunda ta fara zaman jegon nan kullum cikin ƙorafi yake akan abinci, idan kaji baiyi maganaba Mahma ce tai girki da kanta saboda shi.

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button