MAKAUNIYAR KADDARA 68

*Page 68*
……….Sai da Zinneerah ta fara gabatar da sallar magrib bayan fitowarta wanka sannan ta zauna ta tsara kwalliya ƴar gaske, tare da baje lungu da saƙo na
jikinta da ƙamshin mayun turarurrukan ta sabbin haɗi daga Hajiya Falmata. Ta ɗakko less da yaji ɗinki mai ƙyau da tsari ta saka tare da kashe kan ɗauri.
Awarwaraye da sarƙa ta zuba kai kace wani biki zata. Ta sake ɗorawa da wasu turarurrukan sannan tai zaman sallar isha’i. ALLAH ya sota ƴan biyu suna goye a
bayan Yaya Gajeje da Mama A’i.
Sauri-sauri ta kammala ganin har isha’i su AK basu shigoba. Koda ta fito su Yaya Gajeje wani ihun dariya suka ɗauka da yaba wannan wanka nata. Kunya
tasata jan mayafi ya rufe fuskarta.
Mama A’i da yake itama a ce, babu yawan magana sai lalata tace, “A’a wannan gayun bai kamata ki kaisa turaka ke kaɗai ba. Bara na ɗakkoma su Alhaji
ƙarami kaya a canja musu suma dasu za’a”.
“Wannan zance nakan hanaya Mma A’i”. Yaya Karima ta faɗa tana dariya. Zinneerah ta tura baki kaɗan tana faɗin, “Gaskiya nai dai a’a, salon su batamin
gayu”.
“Iyee, lallai Zinni binni ta buɗe miki ido da baki, a gabana babu kunya”. Cewar Yaya gajeje tana riƙe haɓa.
Dariya Zinneerah ta shiga kwasa. Ta faɗa ɗaki tanayi da faɗin, “Yi haƙuri Yaya gajeje na tuba”.
Suma dai dariyar suke tayata harta ɗakko kayan da za’a canjama ƴan biyu. Su Mama A’i suka shiryasu tsaf sannan Zinneerah ta kwashesu. Dan Yaya Gajeje
korata tai wai ta tafi can yazo ya sameta zaifi jin dadi. Su Yaya Gajeje tsoffin masoyane da sukasan takan maza da muhimmancin irin wannan ranar. Aiko
shawararsu Zinneerah ta bi. Dan dama itama akwai nata shirin a ƙasa.
AK bai shigo gidan ba sai wajen tara da rabi na dare. A gajiye yake matuƙa. Dan haka kai tsaye ya nufi sashem Zinneerah ɗauke da little dayay
barci. A falon farko ya samesu dan sunfi zama nan, kai shi baima taɓa samunsu a falon ciki ba dan daga shi sai Zinneerah ɗin ke shigarsa da bedroom dinta na
ciki, saiko little.
Mama A’i ta mike tana amsar little ɗin da masa sannu da zuwa. Suma su Yaya Gajeje sannun suke masa. Cike da mutuntawa yake amsa su yana baza idon ganin
ta inda Zinneerah zata ɓullo da twins nashi. Ganin dai babu alamarta ya sashi leƙa Inna sannan ya fice.
Gulmarsa su Yaya Karima suka shigayi suna dariya. Dan yanda yaketa kalle-kalle sunsan matarsa yake son gani, gashi su kuma sun yi gum bama su nuna sun
fahimcesaba.
Shiko harya ɗan shaƙa dan ya zata abinda ya faru tsakaninsu ɗazun da safe ne ya sata fushi. Sai da ya shigo sashensa ya shaki wani mayataccen ƙamshi
daya nema karar masa da man kai lokaci ɗaya sannan ya sauke ajiyar zuciya. Taku yake tamkar mara laka a jiki yana bin falon data sakama hasken wuta kaɗan da
kallo. Bukatar fara wanka ta sashi nufar bedroom ɗinsa ransa fal waswasin ina ta shiga.
A bedroom ɗinma ƙamshin da yafi na falo ɗaga masa hankali ya shaƙa. Kasancewar wutar ɗakin a kashe dindim ta sashi fara lalauben makunnar fitilar. Ɗan
zabura baya yayi lokacin da haske ya gauraye ko ina a ɗakin. Kyawawan idanunsa kuma sukai masa gani na musamman daya sakashi hangame baki. Zinneerah ce
zaune a tsakkiyar gadon lulluɓe tamkar sabuwar amaryar da aka kawo ɗakin miji yau. gefe da gefenta Amaan da Anam ne cikin showals suna barcinsu hankali
kwance suma cikin gayu.
Jiyay gaba ɗaya yana neman daburcewa da salon nata. Ya shiga takawa a hankali zuwa gaban gadon jininsa na tsinkewa tamkar manjan da yaji zafin wuta.
الْحَمْدُ للهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ .
*_Alhamdu lillahil-lazee bini’imatihi tatimmus-salihat._*
_Godiya ta tabbata ga ALLAH wanda saboda ni’imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika._
اَلْحَمْدُ ِللهِ عَلَى كُلِّ حَالٍ.
*_Alhamdu lillahi ala kulli halin_*
_Godiya ta tabbata ga ALLAH a cikin kowane hali._
Ya faɗa lokacin da yake kaiwa zaune bakin gadon. “Dan ALLAH ki zauna a haka karki motsa harna fito a wanka, dan wannan sirrin ya wuce na gani da ido
kawai ko fatar baki”.
Zinneerah da duk take jinsa tai murmushi batare datayi ko tari ba balle ta motsa. Bai damuba shima dan mikewa kawai yay ya nufi toilet.
A yanda ya barta ɗin kuwa haka yazo ya sameta. Tsane jikinsa yake amma ya kasa daina kallonta ita da yaran daga inda yake. Turarurruka ya cuɗe jikinsa
da shi da ɗaukar wando fari ƙal iya cinya ya saka da ƙaramar riga armless ya haura gadon
Zama yay a gabanta ya tanƙwashe kafafunsa suna fuskantar juna. Yasa hannayensa biyu ya kamo bakin mayafinta ya ɗaga sama ƙyaƙyƙyawan fuskarta na bayyana
garesa tana neman zautashi da wani sassanyan murmushi.
Da ƙyar ya iya fisgar numfashin dake neman ƙwace masa yana wani mar-mar da idanunsa dake neman zubowa jikinta. Luuu ta ɗanyi da idanun tasa tafukan
hannunta ta rufe fuskarta. Hakan da tai ya bashi damar yin tozali da ƙyaƙyƙyawan ƙunshinta.
“My Neerat zaki halakani wlhy”. Ya faɗa a wani irin sassanyan sauti da ita kanta sai da tsigar jikinta ta tashi. Hannayensa duka ya ɗaura akan nata
yana janyewa daga fuskarta. Cikin idanunta ya zuba birkitattun nasa yana faɗin, “Ina ƙaunarki da yawan yawa My Neerat, zaki zautan ɗan Shira da salonki”.
Zinneerah dake amsar saƙwanninsa ta cikin idanunsa itama da wata irin muryar da batasan tanada shi bace, “أَحَبَّكَ الَّذِي أَحْبَبْتَنِي لَهُ.
*_Ahabbakal lazi ahbabtani lahu._*
_Wanda ka so ni saboda Shi, kai ma Ya so ka Yayanmu. Kuma nima ina ƙaunarka”_.
Gaba dayanta ya cacumo jikinsa ya rungumeta tamkar zai cusata a fata da ɓargon jikin nasa gaba ɗaya. Cikin fisgar numfashi ya shiga laluben bakinta
ya manne a cikin nashi jikinsa na wani irin tsuma na zalamar son kasancewa da ita. Bata iya ta hanashi ba. Sai ma haɗin kai data shiga bashi.
Sai da labarin ya nema yin nisa kuma tsoro ya kamata, dan gasu Anam a gadon karsu taushesu. cikin taimakon da ALLAH yay mata sai Amaan ya farka da kuka.
Da ƙyar AK ya iya sakinta yana cizar lip. Itama ta mike da ƙyar daga jikinsa dan tunaninta kar hayesa sukai. Ganin babu abinda ya samesa ya sakata sauke
ajiyar zuciya da hararsa. “Ɗan ɗagwai na zatama hayeka akai”.
Idanu Ak ya buɗe da ƙyar yana duban inda Amaan ɗin yake. Kafin ya yunƙura da ƙyar ya matsa garesa yana dungure masa kai. “Haka kawai ka ɓatamin wasa.
Shiyyasama bana Baffan da kai yaro”.
Murmushi Zinneerah dake kallonsu tayi, ta sauka ƙasa gaba ɗaya tana kai hannu ta ɗaukesa dan tasan yunwa yakeji. Komawa AK yayi ya kwanta dan cikinsa ya
ƙulle tamau. Har Zinneerah ta gama shayar da Amaan ta maidashi ta kwantar sannan ta dubesa.