MAKAUNIYAR KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAUNIYAR KADDARA 68

     “Yayanmu ga abinci fa a falo kar dare ya ƙara zurfi”.

    Lumsassun idanunsa ya buɗe a kanta. Akan laɓɓansa da ƙyar ya furta, “Ke kaɗai kin wadatar dani”.

    Dariya zancen nasa ya bata dan tasan dai shi da abinci sai ta ALLAH. Ta miƙe tana fadin, “Nidai daka daure kaci bara na kai su Anam ai musu shirin 

barci. Uffan bai iya ce mataba harta fice a ɗakin. Bai kuma iya motsawa ba yana a inda ta barsa har kusan mintuna talatin sai gata ta shigo ɗauke da tea. 

Ajiye masa tai tana faɗin, “Ga tea nanto Yayanmu bara na ɗakkosu.”

    Bai motsaba bai kumayi magana ba harta sake ficewa yanzu ma. Bata jimaba yanzu ta dawo ɗauke da ɗan gadon su Amaan. Ta ajiye ta koma falonsa inda Mama 

A’i ta rakota da yaran ta amso su sannan tai mata sai da safe dan tama su Yaya Karima sallama.

       Jin ta dawo tana kwantar dasu ya sashi miƙewa da ƙyar zaune. Kofin tea ɗin ya ɗauka ya hau sha dan da gaske yanajin yunwar ma. Sai dai duk inda tai 

yana binta da kallo harta gama hidimar yaran tai musu addu’a. Dan ma sanye take da zumbulelen hijjabi a saman kayan barcinta.

    Sai da ya kammala yaje yay brush itama taje tayo dan ta kimtso kanta daga can, alwala kawai tayo da brush ɗin ta fito. Tsugunne gaban gadon su Anam ta 

samesa yana musu addu’a fuskarsa ɗauke da murmushi yana faman shafa kawunan yaran. Ta zare hijjab ɗin nata tana nufar falo ɗakko ruwa duk da ta tabbatar sai 

yaci abincin nan ko zuwa anjima ne.

    Da kallo ya bita harta fice. Ya sauke ajiyar zuciya yana mikewa daga wajen su Amaan ɗin.

    Tsaye ta samesa gaban mirror yana saka turare. Tana ajiye ruwan ta juyo da nufin masa magana taji anyi cak da ita sai gado. A tare ya faɗa da su yana 

magana cikin kuneneta. “Wai sokike dai sai na miki kuka yarinyarnan. Sai wani ƙwalele kikemin ni da kayana”.

    Siririyar dariyar data nema zautashi ta saki tana cusa kanta a wuyansa da shaƙar ƙamshinsa itama. Babu shiri ya lalubo bakinta dake ƙamshin strawberry 

freshener ya manna nasa a ciki. A zalame yake, dan haka cikin zalamar ya shiga sarrafata shima, itama kuma tana amsarsa da zalamar dan koba komai tayi kewa.

     Sai da tafiya tai nisa sosai ta gama shagala a hannunsa da salonsa sai ga idon madam ya raina fata ta koma raki daga karshe. Inama AK ke wani jinta shi 

a wannan yanayin. Sai da ya more duk ƙwalelen kwanakin da akai masa shima sannan ya koma lallashi yana mata dariyan mugunta.

    Kamar yanda tai hasashe kuwa suna kimtsa jikinsu sai da yaci abinci waishi duk ta sakashi jin yunwa. Murmushi kawai ta dingayi dan dai al’amarin nasa 

yakanfi ƙarfinta wani lokacin, babu abinda ya damesa ɓaro mata zance yake kansa tsaye kamar ba yayansun nan sarkin mazurai da tsare gida ba. A yanzu haka 

idan su Jamal na tsogumi akansa sai taita dariya kawai dan tasan dai mazuran iya na waje ne. Itama dai sai da tacin danya tsiyayeta tas ga yaransa a gefe da 

nasu suma.

      A tsakanin dare zuwa safiya dai sai da Zinneerah ta raina kanta a hannun AK, dan babu kunya ya hanata komawa sashenta yinin ranar shima kuma bai fita 

ko inaba sai massallaci. Sai dai taje ta ɗauka abu a sashenta ta dawo, su ƴan biyu kam ko ƙofar ɗaki basu jeba suna nane da shi harda little da tunda gari 

ya waye shima ya taho nan ya tare. Sai da zai wuce islamiyya.

       Babu abinda suke zubawa sai zallar soyayya da nunama juna tsantsar ƙauna a wannan yini. Duk wani motsinta idonsa na kanta. kamar yanda itama dai ta 

murje nata idon take masa komai dai-dai da buƙatarsa. Sai ta gama ta koma sinne kai wai ita kunya. Hakan na birgesa da sakashi a nishaɗi, dan ji yake tamkar 

yayi gamo da sabuwar budurwa a haɗuwar farko.

            Washe gari ma duk da ayyukan dake a gabansa tari-tari haka ya lalace wajenta sai bayan azhar ya shirya ya fita. Magribar fari sai gashi ya dawo. 

Sakawa yay ta shirya ita da yara ya fita dasu wani haɗaɗen joint ɗin cin ƙwalam da maƙulashe, suka shawo ice-creem. Yana ɗauke da Anam tana ɗauke da Amaan. 

Little na riƙe da ɗayan hannunsa abin sha’awa. Mutane sai kallonsu suke abin birgewa, dan shi kam rashin zamansa a ƙasar sosai yasa bawani saninsa akai a 

fuskaba da yawa. Sunansa yafi fuskarsa fita ga kunnuwan jama’a. Ganin yanda ake kallon nasu sai kishi ya kamasa ya kuma dinga ɓata fuska. Itama kuma madam 

ɗin nasa sai kishin ya rufeta ruf saboda yanda ƴan matan wajen ke rawar kai gaban samari dama irinsu AK ɗin duk da suna ganinsu tare da iyalansu (Ƴammata a 

yi haƙuri inaji daku????????????????????). Haka dai suka kasance a daddafe a wajen danma vip suke zaune. 

      Daga nan wajen wasan yara suka kai Little dan duk akwai a wajen duk da dare ne. Ya ɗan hau abubuwa yana maijin nishaɗi harda rigimarsa ta aɗora su 

Anam. Zinneerah tace wlhy bata yardaba. Bata gama dawowa daga maganin naƙudaba ba’a sata kuka.

       Maganarnan ta bama AK dariya. Ya dubeta fuska ɗauke da murmushi har haƙwaransa na bayyana yace, “Haba karki bada mata mana madam, ni har ina murna na 

sake jefa ƙwallo tsakanin jiya da yau”.

      Cikin ƙwaɓe fuska tace, “Wayyo ALLAH Yayanmu dan ALLAH daina min fatan nan ka tausaya min”.

        Nanma ƴar dariya yayi da sumbatar goshin Anam dake a hannunsa. “My Sweetheart kinji Mamin ku zata mana buƙulun gambo ko? Ku faɗa mata ku kuna son 

ƙani da wuri Mammah da Mahma, badan kar ace na cika son kai ba sai nace a haɗo da Uncle Ahmad duk lokaci ɗaya, daga baya sai a bani Mommy na da Gwaggo da 

Baba suma, sai Abbah kuma ya zama auta”.

         Yanda tai sagade tana kallonsa baki a hangame ya sashi dungure mata kai. “Kallon fa?”.

       Kai tsaye tace, “Na tsoro da al’ajabi ne ai. Ƴaƴa bakwai fa kake lissafi daga gama arba’in Daddyn Little”.

        “Oh kinma ɗauka ni na wasane kenan. Yarinya shirya da ƙyau Shirawa yawa suke son ƙarawa, mu babu ruwanmu da wani tsarin iyali”.

       “Aiko na rantse yaji zanzo nayi, danya zan tafi sai nayi wata uku acan”.

       Dariya sosai yakeyi yanzu kam. Yace, “Ai wlhy Baba koromin ke zaiyi, kije wajen Granny kuma kin kai kanki, dan ba ɗaga ƙafa zanba harcan zan biki, 

gara-garama wajen gwaggo, zanji kunya. Amm nasan itama koroki zatai”.

        A ranta tace, (Zaka iya wlhy Yayanmu) a fili kam cewa tai, “Wannan zance yafi ƙarfina karka lalatani da ƙarancin shekaruna gaskiya”.

        “Lalacewa kuma ta yaushe yarinya, tunda ga ƴan biyuna a hannu ina kallonsu inajin daɗin raina su da babban Yaya takwaran Daddynsa. Zaki gane kuranki 

bara mu koma gida”.

      Jin haka ya sata yin ɓam da bakinta. Shiko ya samu na tsokana har suka bar wajen bayan yama su Yaya Gajeje takeaway ɗin tasu tsaraban na kayan 

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button