MAKAUNIYAR KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAUNIYAR KADDARA 69

*Page 69*

………..Rayuwa ta cigaba da tafiya cikin farin ciki gasu Zinneerah, babu abinda zatacema ALLAH dasu Hajiya iya sai godiya, dan itakam sun bata ƙyauta da 

har abadan bazata daina alfahari da tutuiya dasu ba. Kwananta goma dayin arba’i su yaya Gajeje suka shirya komawa Danya, duk da dai Inna bata warke bane 

sarai Alhmdllh jikinta yayi sauƙi sosai, dan kullum sai Dr Mahmud yazo safe da dare ya sake dubata. Tana ɗan magana da motsa jikinta, tafiya ce dai babu kam 

kafafun zuwa gidan malamai sun mutu.

     A ɗan zaman nan gidan Zinneerah babu fashi kullum sai tayi kuka. Musamman idan AK ya shiga ya gaisheta ko aka kawo wani lafiyayyen abinci aka bata, ko 

Zinneerah ta shiga da yaranta abin sha’awa gaisheta. Balle ta zauna dan su ɗanyi hira ta dinga haɗiyar zuciya kenan kamar budiddigin ƙwaɗo. Little kam baya 

minti goma bai shiga ɗakin ba inhar yana gida. Dole kuma take kulashi saboda shi babu ruwansa haye mata jiki yake, sai ma idan Zinneerah ta ganine taita 

masa faɗan karya ƙarisa mata uwa, daya faki ido kuma zai sake komawa, ko ganinta a zaunen ne shike ɗaukar masa hankali oho????..

           A dalilin zaman Inna maman sadiq kuma tazo gidan sau kusan uku dubata ita da mmn halima. Na kusan ƙarshene sukazo harda mmn sakina da matar 

naziru da ayanzu suketa zuminci da Khalipha, dan sun zama abokai tunda ba wani girman Khalipha ɗin yayba shima auren gata ne Abba dama yay masa.

    Shatara ta arziƙi AK da Dr Mahmud suka haɗa musu, sannan kuma suka tafi gaba ɗayansu musu rakkiya harda AK da Dr Mahmud dan sunason zuwa su gaida Baba 

duk da baima jima da zuwa ya dubata ba shi da ƴan uwansa, sai su Meenal da suka maƙale. Tarba suka samu mai ban mamaki daga amaryar baba da dangi, kowa yana 

sambarka da ƴan biyun Zinneerah dan hada yawon arba’in duk ta haɗa tazo. Ga Sa’a ma na fama da nata laulayin cikin sai fatan sauka lafiya.

      Anan su AK suka barsu zasu kwana biyu, ya juya shi dasu Jamal da Dr Mahmud kowa na kewar matarsa. Da farko little ya maƙale binsu zaiyi, mi kuma ya 

gani harya shiga motar tama ɗakko masa kayansa sai cayay kuma zai zauna wajan su Anam indai badasu za’a koma Kano ba.

        

      Kwanansu huɗu a Danya Zinneerah da Sa’a suka shiga lungu da saƙo gaida ƴan uwa da abokan arziƙi, duk inda suka gitta sha’awarsu ake ana san barka dan 

sun zama abin kwatance ga kowa. Alkairi kam duk inda suka shiga sukan ajiye gwargwadon ƙarfinsu su wuce ana saka musu albarka. Baba kansa yana cikin farin 

ciki da kasancewar ƴaƴansa cikin kwanciyar hankali. Mutane nata zuwa ganin Inna ana yadda mata habaici akan ga wadda ta tsana da gallazamawa nan ta zama 

silar samun lafiyarta ai.

      Babu bakin magana ga Inna Asabe danya musu murus, sai kukan zuci da haɗiyar zuciya kawai. 

    Randa suka cika kwanaki huɗu babu daɗi babu ƙari sai ga Moos’ab yazo kwasarsu. Zinneerah bataso hakaba dan catake zaiyi haƙuri sukai 1week ɗin data 

roƙa. Amma hakanma sun gode dan batai zaton zai bari ba. Aiko data dawo tasha mitar shi an barsa shi kaɗai a gida kamar mara gata.

         Dariya ta dinga masa da bashi haƙuri. daga ƙarshe tabi hanyar data dace wajen lallashin abinta. Gaba ɗaya gidan yanzu sai take jinsa wani iri da 

duk suka tafi, sauƙinma ta taho da ɗiyar Yaya gajeje zata ɗan mata hutu mai suna Saliha. Yarinya ce ƙyaƙyƙyawa kuma nutsatstsiya, shekaranta goma kwata-

kwata. Tarbiyan yarinyar yasa ta shiga ran AK yace makaranta zai nema mata dan tazo kenan bazata komaba. Sosai Zinneerah taji daɗin hakan kuwa taita masa 

godiya.

         Bayan sati uku da dawowarsu daga Danya da ƙyar ya barta taje Minna wajen Gwaggo Maryama. Aiko taji daɗin wannan zuwa harda ƴar ƙwallarta. Kwanansu 

biyu acan suka dawo, Hajiya iya ta sake jajubarta suka tafi bauchi. AK nata fushi batabi takansaba tace yawan arba’in Zinneerah keyi dana aure daya hanata 

yi. 

                Yama zai yi da tsohuwarnan inba yay gum da bakinsaba. Dan yana tankawa zatama iya ƙwaƙulo wasu dangin a wani garin tace Zinneerah taje. 

Satinsu ɗaya a can suka dawo. Shima kuma sai ya fara musu shirin zuwa Morocco daga can zasu wuce London su ɗan huta tunda little sun sami hutu. Fatansa kuma 

ya tarkato su Mammah su dawo a maida aurenta da baffah tunda yaga sun sakko an daina faɗan masoya saita waya idan sun kira juna da nufin gaisuwa. Mahma kuwa 

gida zai saya mata tai zamanta kusa dasu.

  *_MOROCCO_*

   Wannan shine karon farko na zuwan Zinneerah dangin kakarsu AK, tako sami tarba ta mutunci ga mutanen har taita mamaki, yaranta kowa yana nuna musu so da 

ƙauna abin birgewa. Yaran Mahma kuwa kamar sun santa dama can, dan janta suka dingayi a jiki ita dasu little. Magana kuwa sai da turanci, waɗanda basaji sai 

larabci sai dai ake musu tafinta da Zinneerah dan ita dai ba iyawa taiba sai abinda ba’a rasaba na islamiyya, wanda bai wuce gaisuwa ba da kalmomi.

     Satinsu ɗaya cif suka wuce london cike da kewarsu, inda acanma suka sami tarba ga Mahma da Mammah. Kwanansu biyu da isowa Adilah da Huzaifa suka iso 

suma. Ai fa sai gida ya kacame da farin ciki bakin Mammah tamkar zai yage dan farin ciki. dan itama Adilah fama take da ciki harya fito abinsa.

    Sunsha hutu da soyayyarsu a london kafin su tattaro kuma su dawo gida dansu little sun koma school. Satinsu biyu da dawowa aka maida auren Mammah da 

Baffah.

        Zo kaga farin ciki wajen yaran gidan, dan koba komai AK ya cancanci su girmama mahaifiyarsa su kuma sota dan shima yana girmama nasu. Ba’a wani 

tsaya ja’inja ba Mammah ta tarkato kayanta ta dawo Nigeria gidan masoyinta bisa rakkiyar dangin mahaifinsu.  

           Aiko sai ga baffah da mammah an ƙara shimfiɗa sabuwar soyayya, ita da abokan zamanta kuwa sai dai sambarka. Dan tana ƙoƙarin danne kishinta kamar 

yanda suma suke danne nasu kodan yara da nasihar da hajiya iya ke musu kullum babu gajiyawa. Dan babu abinda zatace da UBANGIJI sai godiya na sake haɗe mata 

kan family ɗinta da yayi, bayan gwagarmaya da jarabawar data sha a shekarun baya wajen ganin ta haɗesu waje guda hakan bai samuba sai da iyaka tazo.

    Mahma kuma AK ya saya mata gida anan kusa dasu, da yake mutumce maison jama’a saita tarkato ƴaƴan dangi daga kaita dansu tayata zama.

★★★

        Daga haka rayuwa ta cigaba da turawa Zinneerah na cigaba dama AK naci akan dawowar Farah. Duk da yana ɓata mata rai haka take sake dawowa ta ƙara 

masa maganar.

     Sai gashi a wasa-wasa dai sai da Farah da Zakiyya suka cika shekaru biyu cif da maimartaba ya basu. Zuwa lokacin ƴan biyu babu inda basa zuwa da 

kafafunsu, yara sunyi ɓul dasu masha ALLAH ga wayo dan sun hau karatun little.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button