MAKAUNIYAR KADDARA 69

Naci Zinneerah ta cigaba da masa akan dawowar Farah ɗin yana basar da ita har sai da ta ƙara wata uku akan shekara biyun mai martaba sannan yace mata
zaije. Amma babu rana.
Wannan maganar tasata tunkarar hajiya iya da batun da Baffah a karo na farko. Albarka suka dinga saka mata. Uncle Ahmad yace insha ALLAH da kansa zaije
ya ɗakko Farah ɗin.
★__________★
Aiko kamar yanda Uncle Ahmad yay alƙawari bayan sati guda da wannan zance batare da sanin AK ba sai gashi tare da Farah. Lokacin suna a barandar gidan
su duka da yammaci iskar la’asar na kaɗasu. Boss na zaune yana harkar business ɗinsa a lap-top duk da ma su Anam na hanashi, dan sai hawa masa jiki suke
suna ƙirniya. Zinneerah na gefensa tana koyama Little homework.
Duban Zinneerah yay yana nuna mata Anam data haye masa dokin wuya. “Mami kizo ki ɗauke kakarnan taki kona jehota ƙasa ta isheni ALLAH, ta hanani
aiki”.
Dariya Zinneerah tai saboda yanda yay maganar a marairaice tana kallon uban da ƴar. Tace, “Idan ka jeho Granny ƙasa aiko ka koma Morocco da ƙafa dan
takwararta ba ɗaga maka ƙafa zatai ba”.
Murmushi yay yana sauke Anam ɗin da faɗin, “Madam rikici ba, ai saita saukemin Nigeria a kaina wlhy. Inaga dai bara na haƙura da aikin nan kawai dan ba
barina zasuyi ba, shi baffah ma neman rikitamin system ɗin yake”.
Little daketa tunzura baki gaba ya gaji da homework ɗin yace, “Daddy na ɗakko ball muyi?”.
“Kokuma kakan ball ɗin ba”. Zinneerah ta faɗa tana nuna masa littafin gabansa. sake tunzura bakin yay yana kallon AK kamar zai kuka. Yanda yay ɗin ya
bama AK dariya. Shima sai ya duba zinneerah yana marairaicewa kamar yanda little yayi. “Mami a tausaya mana a barmu mu huta. Itafa bokon nan iyakarta
duniya, kuma mu ba dangin mango park ba”.
Ta buɗe baki zata bashi amsa motar Uncle Ahmad dake tare da Khalipha da Farah ta shigo gidan. Shi AK da farko ma ya zata ko Suhail ne babban ɗan
Uncle Ahmad ɗin dan nan ɗin gidan zuwansa ne sosai tunda ya baro Turkey. Dan haka yayma Zinneerah nuni da hijjab ɗinta dake gefe dama ajiye. Sai da yaga
Khalipha ya fito da Uncle Ahmad ɗin ya sashi miƙewa tsaye babu shiri. Yana ƙoƙarin nufarsu Farah ta fito a motar. Ta rame sosai ta canja tamkar ba itaba. A
take fara’ar fuskar AK ta ɓace ɓat. Sai dai babu damar magana saboda Uncle Ahmad.
Sannu da zuwa Zinneerah taketa musu fuskarta ɗauke da murmushi. Uncle Ahmad ya ɗauka little yana faɗin, “Uhm babana zoka samin albarka”.
Shima Khalipha sai ya ɗauka Amaan yace, “Nima taho samin tawa albarkar babana tunda abin hakane”. Dariya aka sanya musamman da Anam taje jikin AK itama
ta maƙale. Shi dai ko murmushi baiyiba.
Ita dai Zinneerah nufar Farah dake kallonsu tamkar tana hawayema tayi tana mata sannu da zuwa cikin fara’a. Yanda ta amsa mata kamar a kunyace sai ta
bata mamaki, ta kama hannunta sukabi bayan su AK ɗin da har sun shige ciki.
Sashen AK suka nufa, sai da ta raka Farah sannan ta dawo ta koma sashenta tasa Saliha haɗa abin sha da motsa baki takai musu, ita kuma ta ɗauka
abincinsu na dare da aka girka gaba ɗaya ta nufi sashen nasa. Ta iske Khalipha nata tsokanar Saliha dan mutuniyarsa ce sosai. Bayan ta gama zata wuce ta
kirata tazo ta tattara yaran suje. Ɗaukar Anam tayi da tisa ƙeyar little da Amaan suka fita. Itama ta gama shirya abincin a dining zata fita Uncle Ahmad ya
dakatar da ita.
“Dawo ki zauna Inno ai maganar ta shafeki kema”. Dawowa tai babu musu ta zauna.
Bayan Uncle Ahmad ya buɗe taron da addu’a ya fara musu da nasiha mai ratsa jiki, kafin ya duba AK da yay kicin-kicin da rai. “Abdul-Mutallab ayi
haƙuri, a cigaba da haƙuri a ƙara haƙuri. Ita ƙaddara haka take babu abinda ya isa tsaidata ga bawa. UBANGIJI ya riga ya hukunta faruwar hakan a garemu
tilas. Hakan jarabawa ce. Maganar tone-tone bama ta tasoba tunda anyi komai ya wuce sai ayi haƙuri kuma a sake kafa sabuwar rayuwa. Ga Farah nan ta dawo
cikin iyalinka. Ina fatan zaku manta da komai ku ringumi junanku kuyi haƙuri. Darajar haƙurin da zakuyi sai ALLAH ya ƙara muku kwanciyar hankali da farin
ciki kaji”.
Kan AK a ƙasa yace, “Dady taya zan zauna da wadda bata amshi laifinta ba, girman kai ya hanata neman yafiya ga wadda suka zalunta duk da rawar gani
data taka wajen hana katsewar igiyar aurenta”.
Shashshekar kukan Farah ne ya fito, tace, “Wlhy ba girman kai ya hanani neman gafarar Zinneerah ba kunya ce kawai da nauyin girman laifin da aka aikata
mata, duk da ALLAH shine shaidata ban sanma wadda aka sakama ciki ba. Amma inajin nadama da kaico da kawunanmu saboda son zuciya. Zinneerah ki yafe mana
domin ALLAH badan halinmu ba. Duk da nasan munzo a makare ga neman gafarar taki. Amma dan girman ALLAH ki gafarcemu, gwiyawunmu bisa ƙasa……..”
Sauron katseta Zinneerah tai da faɗin, “Haba aunty Farah, wlhy ni ban rikeku ba tun a waccan ranar komai ya wuce a gareni. Sai dai muyi fatan ALLAH ya
yafe mana baki ɗaya. Ya kuma bamu zaman lafiya da haƙuri da juna”.
Da amin duk suka amsa. Yayin da AK ya ballama Zinneerah harara. Murmushi kawai tayi ta ɗauke kanta. Shima AK ɗin gafararsa Farah ta nema, duk da dai
bai kulataba bai kumace uffanba. Uncle Ahmad dai ya ɗora musu da sabuwar nasiha data ƙara sanyaya jikinsu.
Da ga ƙarshe ya rufe taron da addu’a suka tattara suka tafi aka bar Farah anan.
Tashi Zinneerah tai zata barsu AK ya dakatar da ita wai ta haɗa masa ruwan wanka. Kafinma ta nufi ɗakin shi ya shige. sai taji duk babu daɗi ga Farah
zaune ko kallonta baiyiba.
Tayi tunanin Farah zata ɓata rai, sai taga kawai ta bisa da kallo tana murmushi da share hawaye a kaikaice. Ta maido dubanta ga Zinneerah datai shiru
kanta a ƙasa ta kasa tashi. “Mamin Abdul kije karya ga kin ɓata masa lokaci, sai dai ki sake roƙamin shi gafara dan ALLAH, da kuma keys ɗin sashena”.
“Kiyi haƙuri dan ALLAH aunty Farah komai zai wuce. Kinsan dai halinsa kinma fini sani. Keys kuma suna wajena ma bara na ɗauka miki”. Tai maganar tana
nufar hanyar ƙofar fita. Da sauri Farah ta dakatar da ita tana miƙewa. “A’a kinga jeki ki cika umarninsa zanje na jiraki a general falo”.
Kai Zinneerah ta kaɗa mata kawai cike dajin nauyi ta nufi ɗakin nasa. A cike fam ta iske AK da haushi. Kamar jira yake tana shigowa ya balbaleta da
masifa wai ta wulakantasa bayan ya faɗa mata bukatarsa. Hankalintane ya tashi dan faɗa sosai yakeyi.
Ganin abin karya juye mata yasata faɗawa jikinsa ta manne bakinsu waje guda ta shiga lallashi ta hanyar da yafi buƙata. Ai ko saigashi yay bulum