MAKAUNIYAR KADDARA 69

harma yana neman zurmawa. Da ƙyar ta ƙwace kanta ta na masa dariya. Ƙwafa yay da fadin, “Zan kamaki ne ai, zakimin bayani dalla-dalla tunda na fara zama
abokin wasanki”.
Ita dai shigewa toilet tai tana masa dariya.
Da taimakon su Saliha Farah ta gyara sashenta, Zinneerah takai mata abinci da kanta tana sake mata sannu da zuwa. Dan harda yara taje mata. Jawosu
Farah tai jikinta ta rungume ƙwalla na cika mata ido. Little kam daga jikin Zinneerah ya makale yana gaisheta. Duk yanda taso yazo gareta yaƙi dole ta
haƙura. Anan ta bar mata Amaan da Anam suka fita ita da little tana masa faɗa.
Buɗar bakin yaron nan sai cewa yay, “Mami ni bana sonta…”. Baima rufe bakiba ta make bakin har yana fashewa. Ta shiga masa masifar da ta kai har
AK dake falonsa fitowa dan suna a general falo ne tsaye.
Kallon yanda bakin little din ke jini yana kuka yayi. “Lafiya? miya miki haka harda fasa baki?”.
Ranta a ɓace tace, “Idanma ya sake maimaita abinda ya faɗa wlhy haƙwaran zan zubar ƙasa. Dalla matsamin na wuce mara mutunci”. Ta faɗa tana turesa
tai shigewarta sashenta.
Da kallo AK ya bita ransa a ɓace, dan ya tsani ana dukar masa yara itama kuma ta sani, yakance ko laifi sukai ta zaunar dasu ta musu nasiha bawai
dukaba dan baya magani. Hannun little ɗin ya kama suka shige sashensa yana tambayarsa miyayi mata?.
Abinka ga yaro saiya maimaita abinda ya fadama Farah ɗin. Faɗa shima yay masa da nasiha akan karya sake itama Momy ce. Yaron sai yace bazai sakeba ya
kuma bashi haƙuri. Tare da cewa bara yaje itama Mami ya bata haƙuri.
Cayay ya barta idan sun dawo salla saiya rakashi ya bata.
Haka kuwa akai bayan sun dawo salla sashen Zinneerah ɗin suka shiga shi da little. Acan ɗakinta na ƙurya suka sameta ita da Saliha suna magana. Saliha ta
gaishesa ta fice. Zama yay bakin gado little kuma yaje gabanta ya durƙusa. “Mami kiyi haƙuri bazan sakeba dan ALLAH”.
Shiru tai masa tamkar batajiba sai da AK ɗin yace tunda ya baki haƙuri ba kuma sai ya wuce ba.
“Yayanmu so kake na haƙura gobe ya sake kenan? Shi ɗan karamin nan dashi har yasan wani cewa baya son mutum?”.
Kuka little yasa mata yana ƙara bata haƙuri hannayensa riƙe da kunnuwansa. Nanma dai baki AK ɗin yasa harta haƙura. Little ya fita ya barsu a ɗakin
saboda aikansa da tayi wajen Saliha.
Mikewa tai tana ninke abin sallar da take kai zaune, AK dake binta da kallo yace, “Kemafa masifanki yayi yawa”.
Baki ta kumbura gaba amma batace komai ba. Hakan yasa AK kamota ta faɗo jikinsa. Lips ɗinta ya ɗalla da yatsunsa yana faɗin, “Dan wulakancin kin
fasamin bakin yaro harda jini”.
Murmushi tayi tana cusa kanta a ƙirjinsa da faɗin, “Kaga gobe idan zaima wani rashin kunya sai ya tuna da wannan ai”.
“Uhmyim, to ai ba ƙyaleki zanyiba sai na rama masa”. Yay maganar yana ɗaura lips ɗinsa kan nata. Daga hukunci aka zarce soyayya. Daga karshe dai sai
da aka kai gayin wanka………..✍
*_Dan ALLAH ku saka ɗan uwana addu’oinki na yinin yau, ya ɓata an rasa inda yake kuma babu labarinsa. ALLAH ya bayyanashi, ya karama mahaifiyarsa damu
nutsuwa. Ya kuma tsaresa a duk inda yake. Ya bashi kariya daga abokan banza ko miyagun mutane. Tare da sauran al’ummar musulmi baki ɗaya_*????????????
[ad_2]