MAKAUNIYAR KADDARA 70

*Page 70 End????????????*
………..Iya ƙokari Zinneerah yi take akan ganin zaman AK da Farah ya dai-daita, dan sai faman fushi yake har yanzu. Itama idan tai maganar sai ya hau
fushin da ita. Ya hana taje ɗakinsa balle ta amshi girki. Gudun shiga haƙƙinta yasa Zinneerah riƙa ƙin zuwa ɗakinsa duk bayan kwana biyu, zatai girki ta
kuma gyara masa sashinsa amma bata yarda ta kwana ba duk iya masifar da zaiyi. Dan har cikin ransa haushin Farah da yakeji akan al’amarin nan yaƙi barinsa.
Randa ya fahimci take-taken Zinneerah yayi mata faɗa kamar zai cinyeta, uffa batace da shiba saima kuka da taci. Washe gari sai ya tsiri tafiya Lagos.
Kwanansa biyu ya dawo ran girkinta.
Duk da taji haushin hakan da yayi saita sharesa ta amshesa kamar yanda ta saba daya dawo. Takumabi hanyoyin daya dace ta bashi haƙuri da ƙara roƙonsa
akan ya mance komai. A lokacin tana lafe jikinsa.
Cikin lallashi tace, “Yayanmu nasan daga ni har kai duk an mana laifi, amma idan mukai haƙuri muka mance da komai sai ALLAH muma ya yafe mana
kurakuranmu. Shi riƙo baida amfani, sai dai ya dinga zafafa zuciyar mutun da ƙuntata ta. Dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy nasan itama tayi nadama. Ka duba fa
yanda aunty Farah ta canja tamkar ba itaba, tayi laushi fiye da zaton duk wanda ya santa”.
Guntun tsaki yaja da yunƙurawa zai tashi tai saurin riƙosa ta sake naɗe masa a jiki. “Yayanmu Please mana, i beg you”. Ta faɗa cikin tsananin raunin
murya.
Dafe kansa yay da ɗan cije baki yana wani luu da idanu, aɗan hasale yace, “Wai ke miyasa bakison kiga mutum yana hutawarsa ne? Sai kin takura masa da
silly zantukanki?. Idan ke zaki iya haƙura kamar bakisan ciwon kanki ba, ni bazan haƙuraba. Ban kasance mazinaci ba amma kullum ana haɗa kai da matata ana
min rarraba da sperm a jikin wasu matan dama bansan su ba. Wannan wane irin son zuciya ne da yahudanci?”.
“Duk nasan ba’a ƙyautaba My Heartbeat, amma Please kayi haƙuri tunda sun amsa laifinsu kuma sunyi nadama. Kodan rahamomi da UBANGIJI yay maka
kashi-kashi ciki harda yinka musulmi mai imani daya yarda da ƙaddara da jarabawa. Ya azurtaka da dukiya badan kafi saura ba, ya kuma baka ƙyaƙyƙyawar zuciya
da damar sarrafa dukiyar daya baka ta tsaftatattun hanyoyi da babu saɓon UBANGIJI a ciki, wannan ma ba dabaranka bace. Ya baka lafiya a jikinka baka kasance
gurgu ba, makaho, kurma ko wani abu daban ba. Zakaji sautin kiran salla, kaji na karatun alkur’ani, kaga ayoyin alkur’anin, ka taka kafarka kaje
massallaci,0cikin duniya babu fargaba. Ya baka nutsuwa da tarin hankali da mutunci ga duk wanda zai mu’amulanceka koda ya fika a shekaru. Ya azurtaka da
mata har biyu da ƴaƴa a lokacin da bakai zato ko tsammani ba. Ya bama Baffah da Mammah da Granny tsahon rai kanata ganinsu kanajin farin ciki. Yayanmu duk
waɗanan tarin ni’imomin basu isa susa ka yafema duk wanda yay maka kuskure ba koda yakai girman duniya? Haba Yayanmu kaifa shugabane a garemu kuma uba, duk
abinda kayi dashi zamuyi koyi muda ƴaƴanmu. Wlhy aunty Farah tanada ƙyawawan halaye kawai anyi amfani da wani raunintane wajen ɗaurata akan hakan. Kai mata
afuwa muma sai ALLAH yayi mana. Ka haɗamu ka runguma domin gidanka ya zama tsintsiya ɗaya maɗauri ɗaya. Kagafa yanda take jan su Anam jikinta da soyayya
irin ta uwa da ƴaƴa batare da nuna damuwa ba. Ina kishinta dan nima mace ce kuma inason mijina, amma wlhy ina sonta tunda har taso jinina”.
Ta ƙare maganar hawaye na silalo mata. Sake matseta yay a jikinsa yana bata wasu hot kissis data ƙara tabbatar da yes itama takai mace kuma abinso ga
mijinta kuma ɗan uwanta uban ƴaƴanta. Cikin jin daɗin hakan ta sake bashi haɗin kai ya kuma tabbatar mata da ita ɗin mai darajace ta gaske a garesa.
Koda suka kimtsa jikinsu baice da ita komaiba itama batace da shi ba. Dan tasan idan miskilancin yay miskilanci toshi baya magana da baki sai dai a
aikace. Murzar da yay mata yanzu kuma itace amsar komai da furucin bakinsa gareta. Itama hakan ya wadatar da ita dan maimaita maganar bashi da wani amfani
ko alfanu sai maida hannun agogo baya.
Tun daga ranar ta tattara zancen shirinsa da Farah ta watsar da su gefe kamar bata fahimtar komai. Daga ƙarshe ma cemasa tai ita Danya ma take son
zuwa sake duba jikin inna dan duk ƙarshen wata sai sunje dama har da shi da yaran.
Banza yay mata akan hakan tamkar baijiba har tsahon kwanaki da sukai ɗanyi shariya da juna ita da shi itama. Sai kuma suka koma dai-dai.
Bata sake masa maganar Farah ba ta zuba musu na mujiya. Tun suna fishe-fishesu har dai takai sun shirya batare dama ta saniba. Sai ganinsu tai ana
shimfiɗa shika-shikan soyayya ko kunya babu. Duk da tanajin kishi a ranta haka ta danne ta kauda ido dan karatunta na islamiyya data koma cinye mata kaso
mafi yawa na zaman gidan da rana yanzu, ga kuma su Saliha da mama A’i na ɗebe mata kewa sosai.. Dama tunda Farah ta dawo gidan ta canja salon girkin gidan
kwana bibbiyu, randa taƙi zuwa garesa yay masifar yay faɗan sai dai ta bashi haƙuri kawai tace ga aunty Farah nan.
Sai gashi tsakanin miji da mata sai ALLAH sun ɗinke abinsu batare data saniba. Duk da tanajin kishin mijinta haka ta cigaba da ƙoƙarin ganin ta
danne kamar yanda itama Farah ke ƙoƙarin dannewa a yanzu, suna kuma girmamawa da mutunta junansu duk da ta girmeta nesa ba kusaba.
Ya zaunar dasu ya musu nasiha sosai da shimfiɗa sabbin dokoki masu tsauri a garesu. Dukansu sun amsa masa da alƙawarin kiyayewa insha ALLAH.
Tun daga nan zaman gidan ya canja salo, duk da sunajin kishin junansu haka suketa dannewa kowacce tana nuna bajintarta akan kulawa da shi da saka
shaƙuwa tsakaninsu. Ashe Farah har girki ta iya iskanci ke hanata yi ko a baya. Sai gashi yanzu ta zage tanayi, tarema suke haɗuwa suyi dan haka baka iya
banbance girkin wance ne inba ka ganta a turaka ba.
AK ya ɗaukesu zuwa Family house Farah ta ƙara neman gafarar su Hajiya iya. Inda acanma dai nasihar aka sake musu daɗi kamar ya halaka Mammah. Gata
ta dawo gidan aurenta ga ƴaƴanta duk suna cikin kwanciyar hankali a gidan nasu auren, ga kuma ƴan jikokinta dan Adilah ma ta haihu. Itama har nasiha tai
musu mai ratsa jiki da roƙonsu su haɗa kansu kar taji karta gani, su duka ƴaƴantane bazata fifita wata akan wataba.
Sunji daɗin hakan sun kuma mata godiya.
Ya kuma kaisu gidan mmn sadiq data nuna jin daɗinta sosai itama da dawowar Farah ɗin. Dan dama kullum itace ke ƙara ɗora Zinneerah a kan taita
lallaɓasa har matarsa ta dawo su haɗa kai su zauna lafiya. Karta yarda ya guji matarsa akan laifinta itama wataran idan tai masa kuskure koda ba irin wannan