MAKAUNIYAR KADDARA 70

ba zai iya gudarta. Dan duk abinda namiji ya ƙware wajen yima matarsa ta farko ke amarya kikaji daɗi har kika zuga ya ƙara fusata kema wataran sai ya aikata
miki fiyema da wanda yay mata. Itama kuma ta musu nasiha ta kuma karɓi Farah hannu biyu kamar komai bai faru ba, Farah ɗinma kuma ta mutuntata da gurfana a
gabanta ta nema gafararta.
Mmn sadiq tace karta damu komai ya wuce wlhy ALLAH dai ya kiyaye na gaba ya ƙara musu zaman lafiya da haƙuri da juna. Dan shi kishi tamkar jinin jiki
ne ga mace, sai dai idan ta iya sararafashi zataci riba a duniya da lahira. Zafafa kishi a zuciya babu abinda yake haddasawa sai ƙunci da tarin baƙin ciki
da kaucema dokokin UBANGIJI batare daka fargaba. Kaɗan daga aikin kishi ya ɗoraka a hanyar zuwa wuta ya sakeka a ciki ya kama wani kuma. Amma daka iya
sarrafasa sai gaka ka tsira da mutuncinka da farin cikinka. Ka kuma zama tauraro ga mijin ga kowama, duk mai son ganin bayanka sai dai shi ya wahala kaiko
ALLAH yayta ɗaga darajar ka.
Sunji daɗin nasiharta sosai sun kuma mata godiya su duka. Dan shi kansa AK daya dawo ɗaukarsu yanda ya samesu sunata wasa da dariya sai hakan ya ƙara
masa farin ciki dajin ƙaunarsu. Ya dinga kashesu da salon looks nashi da duk yake rikita manyan mata sujisu suna sake dulmiya a tarin sonsa da ƙaunarsa.
Daga haka rayuwa ta cigaba da turzawa. AK na ƙoƙarin gina adalci a tsakanin matan nasa. Duk ƙwaƙwƙwafinka baka isa banbance wayafi so ba. Ya bar
wannan sirrin a ransa da ga shi sa UBANGIJIN daya haliccesa. Idan saɓani ya shiga tsakaninki da shi bazai taɓa yarda ya wulaƙantaki gaban ƴar uwarkiba sai
dai kuyi abunku ku kashe ku rufe ke da shi a ɗaki. Ku kuma shirya batare da kowa ya sani ba.
Idan a tsakanin saune saɓanin ya shiga tunda yau da gobe sai ALLAH sukanyi ƙoƙarin ganin sunyi saurin fahimtar juna kafin abin yay musu zurfi.
Su Anam gaba ɗaya saboginsu ya koma sashen Farah saboda jansu da take a jikinta. Little ne dai duk yanda taso ya sake da ita yaƙi. Komai zakaga yana
yinsa a ɗarare indai tana a waje. Kuma babu abinda take masa mara ƙyau sai ma sakin fuska da ganin ya saki jikin da ita, amma hakan ya gagara. Takansha
kukanta a ɗaki da godema ALLAH. Wani lokacin idan AK ya gani ya lallasheta da nuna mata ƙuruciyace kawai ke damun little ɗin zai daina wataran.
Takance ita badan wani dalili take kukanba dan har ranta ta cire kallon little daga wani sashe na jikinta. Hundred percent kallon jinin Zinneerah
kawai take masa. Amma koyaya tanason ya dinga sakewa da ita kamar su Anam.
Itama Zinneerah abun na damunta dan kulum cikin yima little ɗin nasiha take amma abu ya kasa ƙarewa duk da dai yana ragewa Alhmdllh.
Yaye su Amaan Zinneerah tayi dan zata fara karatunta da AK yay alƙawari. Sai dai kuma ya fara mata zancen samun ciki tana zillewa dan ita tasan
wahalar data sha. Ganin yanda take zame-zamen ma ya fara faɗa ko wani abu tasha akan hakan.
Rantsuwa ta dinga masa ita batasha komaiba wlhy ALLAH ne dai bai kawo ba, tunda yanzune ma fa ta yaye su Anam ai. Badan ya yardaba ya barta. Amma dai
yace zai ƙara himma yaga ƙaryar zame-zame.
Ita dai dariyace kawai tata dan bata da abin faɗa kuma.
Rayuwa ta shuɗa abubuwa da yawa sun faru wasu sun canja. Su Sa’a dasu Adilah, Raheena matar Khalipha tuni sun hahhaihu. Hakama ansha bikin su Bahijja
dasu Moos’ab.
Zinneerah ta dage da ƙyar ta ƙara santaloma AK ƙyaƙyƙyawar budurwa data ci sunan Mammah. Sai dai yasha mita suna mata dariya shi da Farah akan saura
shidda ya rage ta ciko musu tunda bakwai ne a lissafi. Baki ta dinga kumbura musu da cewar ita wajen Granny zata koma tunda basa sonta. Aiko suka sami abun
tsokanarta daga shi har Farahn da itama a yanzu ake shirin mata aikin mahaifarta saboda cigaba da aka samu akan masu matsalarsu. Fatansu kuma ALLAH yasa a
dace.
Dan yanda takema su Anam saita baka tausayi. Gaba ɗayama yaran yanzu sun koma hanunta. An barma Zinneerah Little da mai sunan Mammah da suke kira
Nu’aymah.
Anyi aiki kuma Alhmdllh an dace. Dan ƴan watannin da Farah ta ɗauka na jinya sai gata ta warke sarai kamar ba’ai mata komaiba, ta koma normal rayuwarta
da fatan ALLAH ya kawo rabo mai albarka. Dan AK ya dage ba wasa. Addu’arsa kullum ALLAH yasa su harbu su duka dan shi fa ƴaƴannan basu gama isarsa ba.
Bayan kusan watanni takwas da aikin saiko gashi andace Farah da ciki. Zokaga murna wajen ƴan uwa da abokan arziƙi tare da uban gayya AK. Nanfa suka
shiga bata kulawa da tattali dan cikin nata mai laulayine sosai tana shan wahala. Da yawan nauyinta sai ya dawo kan Zinneerah. Ga karatu ga yara dan ma
akwai mama A’i da Saliha a gidan.
Haka a ka dinga cuɗawa cikin amincin ALLAH har ciki ya shiga watan haihuwa ta haihu lafiya ƴarta mace ƙyaƙyƙyawa mai kama da sauran ƴan uwanta. Zokaga
murna wajen su Amaan anyi ƙanwa, har iyayi sukema little da suke kira da big bro waisu an musu ƙanwa. AK da Zinneerah kanyi dariya, yakance, “Mami to
gaskiya kema ki dage ki cikoma big bro sauran shidansa, dan nima su naketa jira fa”.
Duk sanda ya faɗi haka sai tace, “Ka rufamin asiri Yayanmu ga Momy nan tayo ɗaya ita zata cika mana sauran biyar ɗin ai”.
Farah kuwa ta karɓe da “Uhm-Uhm Mami ƙarasa biyar ɗin nan wlhy akwai wuya kece da biyu, ni nawa ukun nan sun isheni. Amaan, Anam, Manha”.
Baƙaramar dariya suke mataba akan hakan, dan gaskiya tasha wahalar cikin nan sosai, musamman ma a wajen haihuwarsa kamar bazata kai ba.
Ƴan uwa da abokan arziƙi nata tururuwar zuwa har ranar suna.
Ƴan katsina dasu Mammah sun cika gida fam ansha shagali, itama dangin Zinneerah sunzo Alhmdllh dan zuwa yanzu kam an zama ɗaya sai haƙurin yau da gobe.
Dan itama Farah ɗin tasha zuwa Danya musamman akan duba Inna da har yanzu aketa ibadar ALLAH na jinya. Yarinya taci sunan Mahma Zaliha. Za’ake kiranta
Manha.
Tunda abin nan ya faru sai a sunan nan Zinneerah ta ƙara ganin Aunty Zakiyya. Tanata ɓoye-ɓoyen karsu haɗu dan kunya. Ita Zinneerah ma saita bata
dariya. Ta shirya da kanta ita taje ta sameta aka gaisa.
Ansha suna an shashshare dan walima kawai akayi tamkar sauran ƴaƴansa. Aka bar su Zinneerah da zaman gyaran gida da barcin gajiya.
AK na jera kalmar Alhmdllhi da wannan ni’imomi na samun haɗin kan zuri’arsa da yayi. Fatansa kawai ƙarewa da rayuwa lafiya tare da samun ƙwarin gwiwar
bama ƴaƴansa tarbiya har lokacin data ALLAH zata kasance akan kowannensu.✍????????????
*_TAMMAT BI HAMDULLAH_*
_To nima dai bara na dakata da alƙalamina a nan, kuma ku huta dan ansha fama. Abinda na rubuta dai-dai ALLAH ka haɗamu a ladansa. wanda nayi kuskure ALLAH