MAKAUNIYAR KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAUNIYAR KADDARA 70

ka yafe min daku masu karatu baki ɗaya_.

*_LITTAFI nishaɗi ne, faɗakarwa ne, tunatarwa ne, ilimantarwa ne. Idan kayi gamo da faɗakarwa ɗauki ka amfana gwargwadon iyawarka, idan kaci karo da 

tunatarwa ɗauki ka amfana gwargwadon fahimtarka, idan kaci karo da ilimi a ciki, ɗauka ka amfana gwargwadon nazarinka. Idan kaci karo da nishaɗi, tabbatar 

ka tace shi ka rairaye koda ace zaka iya kwatantashi a zahiriyyarka. Idan nazarinka ya baka mai cutarwane barsa a nan inda ka-gansa nishaɗine kawai ba 

lallai saika sakama zuciyarka ba. dan babbar matsalar masu karatu. kunfi ɗaukar nishaɗi ku fifitashi a littafi ko ku ƙalubalanci marubuci da shi, ko aiki 

dashi. Sannan ku kuma kunmafi kowa son ganin nishaɗin a littafin fiye da duk sauran abubuwa masu ma’anar. Ƙalilanne a cikinku sukafi yarda da ilimi, 

faɗakarwa, tunatarwa da makamantansu, amma ƴammatan nan namu (kuyi haƙuri) ku daina sakama ranku tunanin rayuwar novels da wasu abubuwan nishaɗin cikinsa a 

zukatanku da tunanin samun irin rayuwar. Kisa a ranki ALLAH ya baki miji nagari mai addini dazai kwatanta miki rayuwa mai albarka agidan aurenki ba nishaɗin 

hikayoyin marubutaba. Sai dai kamar yanda kuke tunanin babu rayuwar novels ko yanayin jin daɗin cikinsa a zahiri wlhy akwai, akwaima wanda suka ninka 

rayuwar novels jin daɗi da nishaɗi a cikin gidajenmu, sai dai basu da yawa. Masu shan wahalhalun gidan aure sun rinjayesu. Mata ku ƙara haƙuri, kuyi haƙuri 

kuyita haƙuri. Idan baki samu hakanba karki damu, ki nutsu wajen ibadar ALLAH dan aure ibadane. Wata rana sai ALLAH yay miki sakamako da abinda yafi duk 

wannan jin daɗin da kika rasa. Dan duniya zaman wucin gadine. Kowa burinsa samun aljanna maɗaukakiya. (ALLAH ka sadamu da aljannarsa musami farin ciki mai 

ɗorewa na har abadan acan????????????)._*

*_YA rabbi ka gafartama mahaifina, ka yafe masa da dukkan ƴan uwa musulmi da suka rigamu tafiya. ALLAH yasa ranar mutuwarmu ta zama ranar farin cikinmu, 

ALLAH ya ƙara mana tsoronsa a zukatanmu da soyayyar MANZON ALLAH (S.A.W)????????????_*

_Duk wanda naima kuskure a yayin rubuta littafin nan ya gafarce ni, dan ban saniba ko shine littafi na ƙarshe da zan rubuta a rayuwata. Nima na yafema kowa 

waɗanda suka saya, muka kasance tare dasu a inuwa ɗaya, kuma suka cika alƙawarin ƙyautata mana basu cutar damu tako wata hanyaba. ALLAH ka ƙara mana haƙuri 

da juriyar zaman tare. mun gode, mun gode, mun gode ƙwarai da gaske da ƙoƙarin haƙurin bibiyarmu da kukayi. Zafafa biyar basu da bakin nuna muku farin 

cikinsu sai dai muyitama juna fatan alkairi har ƙarshen rayuwa????????????_.

*_ZAFAFA biyar na sake muku bankwana a karo na ƙarshe, tare da bangajiya sai mun haɗu a ZAFAFA BIYAR 2K22 insha ALLAHU_*.

Ƙauna irain trillions ɗin nan. Dan kuɗin na dabanne, idan nace na daban ina nufin nadaban har acan ƙasan zukatan ZAFAFA BIYAR????????????????????????????????????????????????????????????.

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button