MUSAYAR RUHI 5-6

*⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*
*Page 5 & 6*
*S* osai jikin shi yayi sanyi sake dubanta yayi yace ” kina nufin zaki’iya barina dukda irin son dakike iqirarin yimin ? ” kauda kanta tayi tace ” zakaso na’aykata zina ? ” sosai maganar tadaki zuciyar shi amma seyayi qoqarin shanyewa ” yace ” lna roqon Allah yakareki daga aykata hakan har abada amma tsayin lokaci bakida aure kinkumayi haquri maiyasa yanzu bazakiyiba ? ajiyar zuciya tasauke tace “
wannan yazama dole nayi haquri sabida banida miji amma yanzu inadashi kaga kenan haquri baikamaceniba ” jinjina kai yayi yace ” hakane nikuma zanyi iya qoqarina wajan samar miki mafita muje mugaida su Ammi ”
Kama hannunta yayi suka fita wajan Maimartaba sukafara zuwa bayan sungaidashi suka zauna kiran jakadiya Maimartaba yasa akayi yasata takira duka matanshi babu jimawa kowa ya halarci parlour addu’a Sarki Jabir yayi sannan yafarayimusu nasiha bayan nan yabama su Ammi dama itama nasiha tayimusu sosai anazuwa wajan hajiya hajara da hajiya Mariya cewa sukayi aysu basuda abincewa duk sunfad’i abinda yakamata amma ni inadawata tunasarwa cewar hajiya hajara auran Yarima Hamut shine aure nafarko kuma auran babban magajin Sarki amma banga anshirya wasu daga cikin al’adun cikin masarautar nan ba musamman shinfid’a farin qyalle asaman gadon Gimbiya dan tabbatar da cikar kamalarta dakuma tabbatar dacewa takawo kimarta cikin masarautar nan to yaya abin yake ko akwai wata matsalane ? ”
Nisawa Sarki jabir yayi yace ” kemakince al’ada ba addiniba don haka babu wannan maganar yin hakan baidaceba zamani yacanza abubuwamasun canza dan haka anbar wannan shirman kuta……. ” hakan bazai yiwuba yazama dole ayi Jabir ina raye bazakuzomin dawasu sauye sauye ba dan haka Jakadiya kije kitanadi farin qyalle kamar yadda akasaba sannan kitambayi gimbiya idan tana cikin tsarki idan kuma tana cikin lalura irin ta mata toki tambayeta yaushe zatayi tsarki semujira zuwa lokacin dazatasamu tsarki se a aywatar da lamarin ” Mahaifiyar Sarki Jabir kefad’in haka duban Sarki Jabir tayi tace ” koda bayan raina banyarda ajanye wannan al’adarba ” zama tayi tashiga yima Hamut fad’a shida Hamidat shiko Hamut sosai hankalinshi yatashi sabida bayaso kowa yasan matsalar dayake ciki ayanzu itama Ammin sosai hankalinta yatashi bayan tagama aka sallamesu suka koma part d’in su
Suna shiga Hamidat tanufi cikin bedroom d’in ta cikin ‘bacinrai bin bayanta Hamut yayi zama yayi bakin bed yajawota jikin shi cikin lallashi yace ” my B dan Allah kiyimin wani taimako d’aya kicema Jakadiya kina cikin jinin haila sannan kice kwanaki 7 kikeyi kuma jiya kikafara in sha Allah nanda kwanaki 6 zansamu mafita gobe doctor zezo daga China inasaran samun lafiya da taimakonshi da yardar Allah dan Allah My B kiyimin wannan koda shine alfarma taqarshe dazakiyimin arayuwata ”
Fesar da iska tayi daga cikin bakinta tace ” shi kenan amma idan lokacin yayi babu wata mafita fa yaya zakayi ” sake dubanta yayi yace ” haba B yakikeyin abubuwa kamar babu soyayya tsakanina dake kisanifa danke nikeyin komi hatta aykin pilot kekinsan bashine ra’ayinaba bakuma shine ra’ayin iyayenaba nawa ra’ayin irin na bro nane ra’ayin iyayena kuwa nazama doctor kekuma nazama pilot shine burinki sabida girman son danikeyimiki nabar ra’ayin iyayena nabar nawa nabi naki sabida nazo gareki nayi gaggawa sanadin hakan nafad’o yau gashi sanadin zamana pilot nacikaro da wannan muguwar matsalar wadda zata’iyasaka kimata raguwa nayi tunanin kece mai lallashina kece maizama dani har abada amma segashi ko kwana 1 kinaneman kigagara zama dani kinbani mamaki Hamidat wallahi kinbani mamaki kintambayeni idan kwanaki 6 suka qare bansamu mafitaba yayazanyi ko to kiji da kyau zan sakeki kuma nasanarmakowa cewa banida lafiya ni Hamut bancika namiji ba bazan iya kusantar mace ba zanyi hakan koda kuwa sanadin hakan baqinciki zaisa narasa rayuwata sannan zuciyata zatababbatar mini cewa nafad’i a soyayyar dana gina da yarinyar datun tana 12 yrs har zuwa 23 yrs amma nasamu fad’uwa godiya zanyi miki ko me Hamidat kodiyar tadace dake Thanks har abada hakan zanta furtawa agareki ” yaqarashe fad’ar hakan cikin rawar murya yamiqe yafita afusace
Bayan fitar shi Jakadiya tashigo tambayar Hamidat tayi tabata amsa akan cewa tana cikin jini shiko Hamut fita yayi daga part d’in yanufi part d’in Ammi kaitsaye cikin bedroom d’in ta yanufa zaune yasameta itama tana cikin nazari kwanciya yayi saman bed d’in yad’aura kanshi saman cinyarta yasaki kuka maicin zuciya hatta numfashinshi kaucewa yashigayi sabida tsananin kuka sosai Hankalin Ammi yatashi dafa qirjinshi tayi tashiga yime addu’a tsayin lokaci sannan tace
” Hassan daure kaitafad’in Innalinlahi wa’inna ilaihirraju’uuuu koda acikin zuciyar kane kaji Hassanuna dan Allah nasan zuciyarka akwai taushi da sanyi kaji ” fad’i yashigayi cikin zuciyar shi ahankali yaji zuciyar shi tanayin sanyi har yafara furtawa a fili tsayin lokaci sannan yatashi zaune yadubi Ammi yace
” Ammi Hamidat zatabarni Ammi ashe Hamidat bazatayimin halacci ba nafara sarewa inaji kamar bazan warkeba kenan bazan iya amsa sunan…… ”
Dakatar dashi Ammi tayi tace ” haba Hassan nasanka dahaquri kasani idan Hamidat taqika inada tabbacin Allah zaisakamaka dawadda tafita kuma in sha Allah zakasamu lafiya bakata’bayin tunanin Allah zaijarafceka dawannan laluraba kuma segashi yajarafceka kuma in sha Allah zaisake jaraftarka da sauqi ammafa idan ka’amshi wannan qaddarar hannu 2 kayi godiya ga Allah kayi haquri Huseen yacemin gone doctor zaizo in sha Allah zamusamu mafita zaka warke kaji kaje kaci abinci kayimin alqawarin zakaci ” jinjina kai yayi sannan yafita binshi dakallo Ammin tayi cikin tausayawa
Hajiya Fulani yau itace da Ayki kamar koda yaushe tashirya tsaf tanufi part d’in Sarki Jabir tana shiga yamiqe daga zaunan dayake zaishiga bedroom cikin sauri tasha gabanshi dandanan hawaye suka cika idanunta tace ” dan Allah Maimartaba idan wani abu nayimaka kasanar dani tsayin wasu shekaru baka kulani idan kasakenine kasanar dani dan Allah nasan matsayina ” tsaki yaja yabi gefanta yawuce batare dayace komi ba
Inasake tunasar daku cewa banayin typing ranar Friday
Comments and shine please
_Marmyn Zarah Ce_ ????????????????