Lu’u lu’u 1

*1*

 

*K’ASAR TEXANDA*

*09/07/2000*

 

Shekara ta 2000 (dubu biyu) ita ce shekarar da wasu suka dinga farfagandan cewa za’a tashi duniya, sai dai lamarin Ubangiji ya fi da haka, dan a lokacin da ake taradaddin za’a bar duniyar, a lokacin ne kuma wasu ke zuwa duniyar, wasu kuma a lokacin suke bayyanuwa a duniyar ma, daga ciki kuwa akwai bayyanar cikin *haske marar iyaka* ga Juman.

*MASARAUTAR KHAZIRA*

 

A hankali ta bud’e idonta akan rufin d’akin mai kalar sararin samaniya, lumshe su ta sake yi sannan ta sake bud’ewa dai a kan rufin, cikin nauyin jiki ta juyar da kan ta b’angaren da take da tabbacin nan sarkin na ta ke kwantawa, kasancewar ta mace ta farko a gareshi saidai akwai k’wark’warori da yake zuwa garesu duk sanda ya so. Wayam ta ga inda yake kwancin wanda hakan ya tabbatar mata da lallai ya kai wa wata baiwar ziyara.

A sanyaye ta mik’e zaune akan gadon tana mayar da dogon gashinta baya, dafe goshinta tayi a hankali ta shiga tariyar mafarkinta, ko kuma tace mafarkanta dan yanzu kam abun har ya fara zama mata jiki, wata hud’u kenan da take yawaita wad’anan mafarkan, indai har zata rintse idonta da sunan bacci, to tabbas zatai mafarkin wannan yarinyar mai abun al’ajabi.

D’aga kan ta tayi tana huro iska tare da mik’ewa tsaye, wasu sauk’akk’in takalmi ta saka dake gefen gadon, hannu ta zura ta d’auki doguwar rigar baccinta fara tas mai zubi da alkyabba ta saka ta nufi hanyar fita, a falo na farko babu kowa babu komai sai kayan d’akin da suka k’awatashi, tana bud’e d’aya k’ofar dogarin dake tsaye yayi saurin sunkuyar da kan shi k’asa, ba yabo ba fallasa ta kalleshi tace “Ka je b’angaren hadimai ka kira min *Habbee*.”

Sake sunkuyawa yayi yace “Angama sarauniya ta.”

Falon na farko ta dawo ta zauna k’afa d’aya kan d’aya tana jiran isowar Jakadiyar ta ta da tafi aminta da ita, bugu da k’ari suna sirri su kashe su binne a tare.

Jim kad’an sai ga dogarin ya k’wank’wasa k’ofar tare da bud’ewa a hankali, tsaye yayi gaban k’ofar ya rusuna yace “Sarauniya ta, Jakadiya Habbee ta amsa kiranki, tana neman izinin k’arasowa gareki?”

Da hannu ta masa alamar za ta iya shigowa batare data kalleshi ba, juyawa yayi rike da doguwar sandar shi, sakan (second) k’alilan dattijuwar ta shigo da girmamawa da kuma rusuna kan ta k’asa, saida ta zauna k’asa gabanta tace “Uwar-gijiyata, fatan tsawon rai da lafiya d’orarriya, na zo da hanzarina domin son sanin abinda ke damun sarauniyata da har ya hanata bacci a tsohon daren nan.”

Sauke k’afarta tayi daga kan d’ayar sannan ta d’ora gwiwar hannayenta a kan cinyoyinta ta tallabe hab’a, kallon Jakadiyar tayi cike da damuwa da alhini tace “Jakadiya.”

Da sauri ta amsa da “Na’am ranki shi dad’e.”

A sanyaye tace “Ina shiga damuwa sosai akan mafarkin nan nawa, gashi malaman gidan abun bauta ma sun kasa fassara min mafarki na, shi ne dalilin da yasa na kiraki dan ki bani shawara, me ye abun yi?”

Sunkuyar da kai ta sake yi ba tare da sun had’a ido ba tace “Uwar-gijiyata indai har yanzu kina mafarkin nan, to fa abun yi shi ne mu nemi sanin fassararsa, ina ga zaifi ki je ki ga babban malamin gurin bauta kai tsaye.”

Kallonta tayi ta sauke numfashi tace “Hakan zai fi ko?”

Jinjina kai tayi tace “Hakan shi ne mafita ranki shi dad’e.”

Yatsina fuska tayi tace “To amma fa Jakadiya kinsan babban malami yana da kusanci da sarkina, duk tattaunawar da zamuyi dole sarki zai san komai, ni kuma ina tsoron kar mafarkina ya zama na sharri.”

Girgiza kai Jakadiya Habbee tayi tace “Babu abinda zai faru uwar-gijiyata, mafarkinki alkairi ne.”

Ajiyar zuciya ta sauke tace “Shikenan, da sassafe zamu je mu gan shi.”

Cikeda girmamawa ta amsa mata da “To ranki shi dad’e, ni zan koma, a kwana lafiya.”

Da ido kawai ta amsa mata kafin ita ma ta mik’e tana turo d’an k’aramin bakinta ta koma makwancinta, kuma har lokacin sarki Musail bai dawo ba.

Washe garin ranar litinin 10/07/2000 sarauniya Juman ta isa wurin bautar dake nesa da masarautar Khazira dan had’uwa da babban malamin fadar wato *Dhurani*, tsaye yake a gabanta hannayrnshi akan had’e kusa da cikinshi yana kallonta, yayin da take zaune akan kujerar katako doguwa kan ta k’asa, dan yana da matuk’ar girma a k’asar ta yanda wasu abubuwan shi ke ba wa sarki Musail shawararsu kafin ya gabatar, cikin kulawa a harshen slovaque yace “Sarauniya ta, me ye mafarkin na ki?”

Ba tare data d’ago kan ta ba ta shiga girgiza kai tana bud’a baki kamar za tayi magana kuma damuwa da tsoro na hanata, a sanyaye ta d’aga kai ta kalleshi tana yatsina fuska tace “Babban malami, mafarkin nan yana damuna, kuma kullum kusan kala d’aya ne, yarinya da bata fi shekara biyar ba a duniya, amma sai na ganta a kan kujerar mulki cikin shiga irin ta sarakai, abun al’ajabi shi ne, idonta da kuma haskenta mai matuk’ar d’aukar ido, wannan hasken ya isa ya haskaka garin nan da kewayensa, kayan jikinta ma ban tab’a ganin wani gawurtaccen sarkin daya tab’a saka ko da kwatankwacin irinsu ba, suna da d’aukar hankali da k’yalk’yali tamkar madubi.”

Sake kafeshi tayi da ido tace “Babban malami, wasu lokuta a saman ruwa nake ganinta tana tafiya, kuma kullum k’ok’arin bani hannu take tana fad’a min wai na kawo hannuna ta cece ni, na…na rasa gane… Wannan abun, na rok’eka kayi wani abu a kai ba tare da sarki ya ji.”

Tunda ta fara magana Dhurani ya tsura mata ido yana kallo, tabbas wani yanayi ya shiga da asalinsa b’acin rai ne musababbin sa da tashin hankali, da sauri ya juya ya shige wata k’ofa dake cikin wurin bautar ya rufo, gaban wani teburi ya k’arasa ya bud’a wani k’aton littafi dake gabanshi, dama yana ajiyar wurin saboda jiran wannan ranar, sake karanta wurin yayi a k’alla ya maimaita ya fi sau goma kafin ya rufe.

D’aga kan shi yayi ya kalli rufin d’akin goshinshi na tsatsafo gumi, lumshe ido yayi yana tunanin mafita akan bala’in dake shirin tunkarosu, da sauri ya bud’a ido skamakon jin wata shawara da zuciyarshi ta yanke mishi, sauke kan shi yayi k’asa ya sauke nannauyen numfashi ya juyo hannunsa rik’e da littafin yana murmushin mugunta ya fito.

Sarauniya Juman da tunda ta ga ya bar ta nan ta shiga tashin hankali da jin cewa lallai mafarkinta ba alkairi bane kamar yanda tayi zato, mik’ewa tayi ta juya a sanyaye zata bar wuri dan Habbee na bakin k’ofa tana jiranta, fitowarshi tasa ta juyawa sai kuma ta tsaya, sake nuna mata wuri yayi inda ta tashi yace “Zauna sarauniyata.”

Komawa tayi ta zauna tana kallon shi a raunane tace “Babban malami lafiya ko?”

Murmushi yayi yace “Lafiya lau, karki damu.”

Kujerar dake gefenta ya zauna yana kallonta yace “Ita wannan yarinya da kike gani a mafarkinki, *’yar da zaki haifa ce* wato *Zafeera*, ma’ana haske marar yankewa.”

Mamaki ne fal a kan fuskarta inda ta shiga jujjuya kan ta, da k’yar ta kalleshi tace “Zafeera? ‘Yar da zan haifa? To amma ai…”

Da saurita kalleshi kuma tace “Yaushe?”

Wani murmushi yayi yace “Ai fara mafarkinta da kikayi alamu ne na cikinta na jikinki.”

Dafe mararta tayi mamaki bai bar fuskarta ba ta sake fad’in “Amma kuma ban ga wani alamu na samun ciki ba, a k’alla wata hud’u dana fara mafarkin nan, idan har haka alamu ne na samun cikin ta, to fa ina ganin jini a kowane wata, ta ya haka zata kasance? Bayan cikina na farko ban ga haka ba.”

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button