MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 1 to 10

“No Doctor what happened to my Dad?” She asked him again with a smirk

Numfashi ya ja kafin yace, “Your father is very sick. We have to take him to the hospital because he needs to be examined. He needs special care.”

Hawaye ne kawai ke zirya a kan fuskar ta ta gaza ma magana

Hannu yasa a kafaɗan ta yace, “Calm down MEEMA insha Allahu he will get up he will be fine”.

Idanun ta kawai ta lumshe still hawayen ciki na tsiyaya, sai kuma ta buɗe su tana shirin wuce sa ta shiga ɗakin

Sai ya tsayar da ita yana faɗin, “No, don’t come in, let’s get an ambulance now and we’ll pass, Sorry ok?”

Bata bi ta kanshi ba ta buɗe ƙofan ta shige, wajen Abee ɗin ta da idanun sa ke rufe yana fitar da numfashi daƙyar ta nufa, Kasancewar doctor yayi masa alluran barci sabida a samu a kai shi Hospital ba tare da wani problem ba. A hankali ta zame a wajen tana riƙo hannayen sa, cikin kuka daƙyar ta kirayi sunan sa, sai dai ta kasa yin maganar dole tayi shiru tana danne bakin ta, ɗaura kanta tayi a cikin sa tana ta shashsheƙan kuka.

              A haka aka zo da ambulance aka ɗauke shi suka wuce Hospital ɗin

Gaba ɗaya MEEMA ta gaza nutsuwa sai kuka take yi, duk rarrashin da Doctorn yayi mata kafin su shiga duba Abee amma ina taƙi yin shiru, haka ma Nurse Zara tana tare da ita tana faman rarrashin ta amma ina taƙi shiru, dole ta tafi ta barta a wajen tana ta sintiri duk ta gaza zama, gaba ɗaya idanuwan ta sun yi jawur sun kumbura suntum, kallo ɗaya zaka yi mata ka gane tana a cikin tashin hankali domin hakan ya gaza ɓoyuwa a kyakkyawar fuskar ta

Daga baya ne House Girl ɗin su ta zo shi ne suka zauna tare har sanda Doctorn Abee ya fito

Da gudu ta isa wurin sa tana kuka tana tambayar shi jikin Abee ɗin

Cike da tausayin ta yace, “I’m so sorry MEEMA: Just be patient. As your father is in a difficult situation, we will have to wait and see what the situation will be like.”

Jiri ne ya kusa kwasar ta sai house Girl ɗin su tayi saurin tare ta ta faɗa jikin ta, kuka sosai take yi tana son tsaya wa da ƙafafuwan ta amma ina ta gaza, dole sai da taimakon House Girl ɗin su dake riƙe da ita ta iya tsayuwa. Cikin kukan take cewa, 

“Doctor help my father please, I love him I don’t want to lose him, please help me don’t let him go”. Break the words and burst into tears

Rarrashin ta kawai yake yi yana bata baki, dole yace wa House Girl ɗin, “she holds her and passes her to his office”.

Haka suka wuce can ta samu ta zauna

Nan yace mata, “Now they put oxygen on him and he is asleep, or later she will check on him. But she calms down and nothing will happen. He will be fine soon.”

Har ya fice bata iya magana ba, a haka suka zauna a Office ɗin har zuwa yamma babu abinda ke tayar da su sai sallah, gaba ɗaya ita MEEMA ta gaza saka komi a cikin ta illa kai kukan ta wurin Allah da take yi, after dress ɗin ma da ta sanya a jikin ta take sallan House Girl ta koma ta ɗauko mata a gida, don daga ita sai kayan barci ta zo, kuma duk rarrashin da tayi mata taci wani abu ta ƙi magana bare ta kalle ta, duk tayi wani zuru-zuru da ita fargaba da tashin hankali yasa ta fita hayyacin ta, mahaifin ta kawai take burin ta gani yanzu.

             Sai bayan magriba ya farka likitan ya zo ya sanar mata don ta je ta duba sa

Shima Abee ɗin tunda ya farka ya nemi a kira ta

Da gudu tabi bayan Nurse Zara da tayi mata jagora zuwa ɗakin da Abee yake ciki. Tana shiga ta ƙarisa wurin sa da sauri tana me kiran sunan sa a lokaci ɗaya hawaye na kwaranya mata, Abee..” ta sake faɗi bakin ta na rawa 

Idanun sa ya sauke a kanta yana mata murmushi

Hannu tasa ta riƙe nashi tana me sake kiran sunan sa da cewa, “Abee, please recover. Abee I need you in my life. I love you so much. I don’t want you to leave me. Please get up.”

Daƙyar ya iya furta, “Ummy sickness and death all belong to God, I have no power to continue living except the one God has chosen for me”. Sai ya tsakaita kafin ya sake sakin murmushi zuciyar sa na ƙuna da ganin tana hawaye be da yanda zai yi ya share mata. Ya fito ta yayi alamun ta matso

Da sauri ta matso sosai tana me ɗaura kanta a jikin sa

A hankali ya soma raɗa mata magana cike da rauni wanda daƙyar yake furta kalaman

Ita kuma sai zubar da hawaye take yi har sanda ta kasa jure wa da kalaman nasa ta hau girgiza masa kai tana cewa, “laà Abee I can’t..” abinda take iya furta wa kenan tana kuka sosai

Shi kuma lumshe idanun sa yayi while hawaye masu zafi suna sauko masa a kunci. Yana riƙe da hannun ta gam ya ƙi saki

Ita kuma sai kuka take faman yi

Sai da Nurse Zara ta shigo ta janye ta kafin ta samu ta fita tana me sake ɓarke wa da wani sabon kukan, a jikin ƙofan ta zame tana kuka sosai duk fuskar ta ta sharɓe da hawaye tayi jazur

Me aikin su da Nurse Zara suka kama ta suka mayar da ita Office ɗin Doctor.

              Daga ranan kullum a cikin ƙunci da kuka take kwana, a kan sallaya take wuni tana sallah da roƙon Allah ya warkar da Abee ɗin ta, ko abinci ta dena ci sai an yi da gaske, a kuma asibitin take kwana ko jirga wa ba ta yi, kuma tun daga ranan ba’a sake barin ta ta duba Abee ba sabida ganin tana ɗaga hankalin ta, ga shi ciwon nasa yanzu yayi tsanani sosai.

           Five days after his arrival, he died at the hospital. Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un bazan iya misalta muku tashin hankalin da MEEMA ta shiga ba, gau ta sume bata sake sanin inda take ba har sai da aka yi kwana uku da jana’izar shi, a ranan da ta farka ƙaramin hauka tayi musu a kan, “sai sun dawo mata da mahaifin ta,” duk ta fita hayyacin ta tamkar mahaukaciya, da farko sun yi tunanin ta haukace ne ashe zafin rabuwa da mahaifin ta ne ya janyo mata rasa tunanin ta gaba ɗaya, sai da aka koma ɗaura ta a kan magani don abubuwan da take yi bata da maraba da mahaukata. Da ban baki da nasiha tare da treating ɗin ta har aka samu ta soma samun sauƙi

Likitan mahaifin ta shi ya ɗau ragamar komai na jana’izar Abee har aka yi aka gama lafiya, kuma ya samu mutane ba kaɗan ba sabida babban masallaci na garin Riyadh ɗin aka kai shi aka yi masa Sallah.

               Sai da aka yi kwana bakwai da rasuwan sa kafin aka sallami MEEMA. House girl ɗin su ita ke kula da ita domin tsananin tausayi take bata, ita take ta ɗawainiya da ita a asibitin har suka koma gida, a lokacin sam baza kace MEEMA bace sabida yanda ta sake rame wa tayi fari fat tamkar mara jini a jiki. Ko magana ba ta iya yi kullum sai zubar da hawaye, ta kasa yarda cewa Mahaifin ta ya rasu ya bar ta, har ji take yi a wannan lokacin gwara mutuwar ta da rayuwar ta, ta gummaci ta bi shi a irin wannan Rayuwar, a yanzu tana buƙatar mutuwar ta fiye da rayuwa, ta rasa komi nata, bata da kowa sai ita kaɗai, taya zata iya rayuwa a haka? Komi nata na farin ciki ya wargaje ya barta. Mutuwa shi ne ya fi cancanta a gare ta.

              Amma a haka babu gajiya house Girl ɗin ta take bata kulawa. Ita take lallaɓa ta ta samu ta ci abinci, sai ta kwana ta wuni daga ruwa sai ruwa take zuba wa a bakin ta, idan kuma ta matsa mata da cin abinci har marin ta take yi ta daka mata tsawa ta kore ta, amma kuma haka anjima zata sake kawo mata, da haka har ta soma shawo kanta wani lokacin ta ɗan kalle ta taci abincin, wani lokacin kuma idan ta birkice tayi ta zagin ta tana daka mata tsawa a kan, “ta tafi ta barta ko ta kashe ta, tana damun rayuwar ta,” duk waɗannan abubuwan haka house Girl ɗin take iya ƙoƙarin ta wajen jure wa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button