MEEMA FAROUK Page 1 to 10

Da jirgin Zamiya ya sauka drever MEEMA ta sanya ya ɗauko ta. Koda suka haɗu sai duk suka rungume juna cike da farin cikin sake haɗuwa wuri ɗaya.
“I’m so sorry MEEMA for not coming until today, please be patient. May God have mercy on Abee and forgive him”. Zamiya tafaɗa idanuwan ta a kan MEEMA da ta riƙe mata hannu
Murmushin yaƙe MEEMAN tayi kafin tace, “no problem, thank you very much for your coming”.
Cike da fuskar tausayi Zamiyan tace, “Are you alright now? But you are not going to be alone in this house, are you? You should go back to Ummee.”
“We’ve already told her, if she doesn’t come back she will follow ME to our house.” Ummu Hani Said
Kallon su kawai MEEMAN take yi, sai dai gaba ɗaya a ranta damuwa ne ke damun ta, duk da har yanzu basu san asalin abinda yasa Ummeen ta ta tafi ta bar su ba, ta sanar musu cewa, “Ummee sun rabu da Abee ne”. Dalilin da yasa ta tafi ta bar su kenan, domin ba ta fatan su san real labarin, tana ga kowa ya ji dole ne zai yi tirr da mahaifiyar ta, abun kunya ne ma a gare ta ace an san Ummeen ta ta tafi ta bar su. Shiyasa kawai da suka matsanta mata sai tace musu, “dama tana da ninyar zuwa Nigeria wajen ta”.
A ranan a gidan suka wuni kafin suka wuce suka bar ta da Zamiya don a wajen ta zata zauna. Zaman Zamiyan na kwana biyu yasa ta ɗan sake jikin ta sosai saboda tana jan ta da surutu tare da mata abinda zai ɗebe mata kewa, shiyasa da zata tafi tayi kewar ta sosai har ƙwalla tayi.
Zuwa kwana biyu duk ta gama haɗa kan komi na Abee ɗin ta, lauyan Abee shi yayi mata jagora ta haɗa takardun ƙadarorin shi da ya mayar da sunan ta, dama already duk dukiyan sa ya mayar mata a account ɗin ta kafin ya rasu, lauyan ta saka ya samo masu siyan companies ɗin suka taya, da fari ta so siyar da su duka ne sai kuma ta sauya shawara aka yi cinikin ɗaya, ɗayan kuma ta danƙa shi a wurin Lauyan Abee zai riƙa kula mata dashi sai kuɗaɗen su riƙa shiga account ɗin ta.
A ranan da zata tafi Nigeria kuka sosai ta sha, haka ma house Girl ɗin su da duk masu aikin gidan, babban Trolly ta cika da kayan ta da sauran abubuwan amfanin ta, har computers ɗin ta dana Abee duk ta haɗa ta tarkata, sai kuma ɗan ƙaramin Back Shima da ta cika iyakan abubuwan da ta kwashe a gidan, gidan kuma ta danƙa a hannun su don ta kasa siyarwa, za su ci gaba da kula dashi tana tura musu albashin su ta account
Gaba ɗayan su da drever suka raka ta har airport ta hau jirgin da zai wuce Nigeria. Seat ɗin ta na line 3 ne, ita ce a ciki shiyasa tunda ta zauna ta kafa kanta a window ta mayar da idanuwan ta ta rufe. Har jirgin ya cika ana ta maganar a saka belt while bata motsa ba
Wanda yake gefen ta da ya gama saka nashi a karo na farko sai ya kalli inda take, kamar bazai yi magana ba domin har ya kawar da kansa sai kuma ya sake kallon ta yace, “excuse me”. Bata ji sa ba har sai da ya saka hannu ya buga jikin kujeran nata kafin tayi firgigit tana kallon sa idanun su cikin na juna. Janye nasa yayi yana ɗan lumshe su kafin ya buɗe, ba tare da ya kalle ta ba yace, “put on your belt”.
Sai a lokacin ta janye nata idanun tana kallon jikin ta, sai kuma ta saka hannayen ta a kasalance ta saka belt ɗin ta sake kafa kanta a window, sai dai a wannan lokacin bata rufe idanuwan ta ba waje kawai take kallo, bata sake motsa wa ba har sanda aka zo tambayar su abinda suke so a kawo musu. Ko juyo wa bata yi ba ta girgiza kanta alamun ba ta son komi
Wanda ke gefen ta shima be amshi komi ba, jarida kawai yace, “a kawo masa.” ya kara a fuskar sa yana karanta wa. Shima ɗin be sake motsa wa ba har jirgin nasu yayi landing a garin Abuja.
Sai da aka soma fita tukun MEEMA ta ɗago kanta ta kalli wanda ke kusa da ita da yake ƙoƙarin tashi zai ciro jakan sa, murya a matuƙar sanyaye tace, “Afuwan uridu an as aluk”.
Ɗago idanuwan sa yayi ya zuba mata su ba tare da yayi magana ba
Hakan ne yasa ta ɗan dafe goshin ta kuma sai ta maimaita masa da harshen turanci, “Please I want to ask you”.
Ɗauke kansa kawai yayi ya mayar kan jakan sa, sai da ya sauko kafin yace da ita, “I hear you”.
Ran MEEMA babu daɗi tace, “We come to Yola?”
Be san sanda ya kalle ta ba jin abinda tace, ƙare mata kallo kawai yake yi yana nazartan ta
Ita kuma ganin kallon da yake mata sai ta ɓata fuska tana tura baki tare da ɗauke kai
Hakan yasa ya waro idanu waje still idanun sa a kanta, be furta komi ba ya ɗauki kayan sa ya wuce
Da kallo tabi bayan sa zuciyar ta cike da haushi, sai kawai taja tsaki tana miƙe wa itama ta soma ciro nata kayan ta fita a jirgin. Tun da ta saka ƙafafuwan ta a waje take bin duk inda Allah ya kai idanuwan ta da kallo, wannan shi ne rana ta farko da ta taɓa zuwa Nigeria a rayuwar ta, duk da ta sha jin labarin ƙasar wajen mahaifin ta amma bata taɓa mayar da hankali a kan wai tana son ta ga ya ƙasar take ba koda a hoto ne, ko kuma tazo ta gani a matsayin ƙasar iyayen ta, in fact ma ita ko sau ɗaya bata taɓa jin ƙaunar ƙasar ba, amma yau sai gata a cikin ta, shiyasa ta zama kamar village Girl sabida yanda take kallon mutanen ciki, daƙyar take ma iya tafiya tsaban kalle-kalle har tuntuɓe take ci. Bata san ina zata nufa ba shiyasa ta tsaya a tsakiyar airport ɗin tana ta ganin yanda mutane ke zirga-zirga, duk da dare ne amma gaba ɗaya wajen ya haske da ƙwan fitila. Sai da ta ji ƙafafuwan ta sun soma gajiya kafin ta tasar wa ƙofan da ta ga ana fita. Yawanci ganin mutane take yi sai hawa mota suke yi suna tafiya, sai kuma wasu suna wuce wa wajen ƴan taxi suna hawa, da yanda kuma masu taxi ɗin suke biyo fasinja suna tambayar inda za su je. Hakan yasa itama ta nufi can ɗin kanta tsaye tana jan kayan ta daƙyar
Ɗaya na hango ta ya taho da sauri yace da ita, “tafiya zata yi?”
Bata san me yace ba shiyasa tace mishi, “I’m going to Yola”.
“Yola kuma Hajiya? Ai babu inda zaki samu motan Yola a nan, gwara ma ki kama hanya ki san inda dare yayi miki”. Ya wuce abin sa yana ci gaba da tare fasinja
Tsaye tayi a wurin kawai don bata fahimci inda zancen nasa ya nufa ba
Wani yana hango ta shima ya zo ya hau tambayar ta inda zata je
The same amsar da ta bawa wancan shi ta ba shi
Shi da yake ya iya turanci sai ya sanar mata, “babu motan Yola a nan, saboda yanzu dare yayi baza ta samu ba sai gobe”.
Jin hakan yasa ta roƙe sa a kan,
“Take her to Yola. She will give him whatever it is.”
Cikin turancin yace mata, “Madam nan fa Abuja kike ba Yola ba, tafiyan da zamu yi awanni taya zan ɗauke ki a wannan tsohon daren? yanzu fa ƙarfe 09:00pm”.
Bata kai ga yin magana ba mutumin da suka zauna tare a jirgi ya iso wajen. Kallon me motan yayi fuskar shi babu walwala yace, “mu je ka kai Ni barikin sojoji”.
“Ok to”. Me taxi ɗin ya amsa mishi da sauri yana amsar Jakar sa ya wuce mota shi kuma ya bi bayan sa. Bayan ya saka mishi kayan a cikin Boot sai ya dawo wurin MEEMA da ke tsaye kamar status a wurin ta kasa motsa wa yace da ita cikin turanci, “ta faɗa inda zata je ya sauke ta sabida motoci sun ƙare, idan ba haka ba zata sha wahalan samun abun hawa idan ta bar wurin”.
Hotel kawai ta iya furta wa a laɓɓan ta
Shi ne yace, “to su je”. Taimaka mata yayi da kayan suka wuce, ya sanya mata a Boot