MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 1 to 10

Ita kuma ta wuce ta buɗe baya zata shiga. Ganin mutumin hakimce a bayan motan sai ta ja ta tsaya ta ƙi shiga

“Madame, enter. We are in a hurry.”

Maganar da me taxin yayi ne ya ankarar da shi na cikin motan ma, don a lokacin wayan sa yake duba wa ko ɗago kai be yi ba. Idanu suka haɗa dashi sai yayi saurin ɗauke nasa

While itama hakan ne, rufe motan tayi ta koma gaba ta shige

Me taxi ya ja motan suka tafi

Babu me motsi a cikin motan har sanda suka isa wani kyakykyawan Hotel ya tsayar da motan, sannan ya kalle ta yace, “Madam here is ok?”

“Is that Hotel?” Ta tambaye sa tana kallon sa

“Yes, it’s a hotel. Look at the name there.”

“Ok” kawai tace tana shirin fita

“Your money is two hundred Madam”.

Shaf ta manta shiyasa ta dakata tana juyo wa ta kalle sa, cikin sanyin murya tace, “give me your account number”.

“Account number? Two hundred You paid for my account? I don’t have it. Just give me Cash.”

“Sorry I don’t know how much money you are using, and I don’t have money now in my hand, I will pay you through my account”.

Zai yi magana suka ji muryan mutumin nan na baya yana cewa, “wai zaman me kake yi ne? Ka sallame ta mu tafi.”

Dayake ita bata ji me yace ba tunda da Hausa yayi

Shi kuma me taxin yace, “kayi haƙuri don Allah haƙƙi na zata bani”.

“Mu je zan biya”. Cewar sa ba tare da ya ɗago kai daga latsa wayan da yake yi ba bcoz hasashen sa ya ba shi kamar ita baƙuwa ce a ƙasar, domin yanayin ta da shigan da tayi ya nuna ba ƴar nan bace

“Ok madam let’s go take your Trollys off, he said he’ll pay your bill”.

“WHO?”

“This is in the car.”

Kallon sa tayi ta ga hankalin sa na kan waya ne. Bata ce komi ba ta buɗe motan ta fice, Sai da ta fita ne kuma ta leƙo kaɗan tace dashi, “shukran”.

Be yi ninyan ɗago wa ya kalle ta ba, amma jin yanda sassanyan muryan nata ya daki kunnen sa hakan yasa ya ji kwaɗayin sake tozali da ita

Ai kuwa idanuwan nasu suka shige cikin na juna. Ita ta soma janye nata idanun tana juya wa ta tafi domin already shi me taxi ya gama ciro mata kayan ta

Shiga motan yayi ya ja suka bar wurin

A hankali ta ja kayan nata ta nufi Hotel ɗin. Ta samu masu aikin don basu tashi ba, faɗa musu tayi, “she needs a room”.

Babu ɓata lokaci suka yi mata bayanin dokokin Hotel ɗin tare da bata takarda ta cike bayan ta biya su kuɗin ta account, sannan suka bata keey ɗin ɗakin bayan ɗaya tayi mata jagora har zuwa bakin ƙofan ɗakin

Murɗa ƙofan tayi ta shige ciki, a bakin ƙofan ta tsaya ganin ɗakin da duhu, sai ta laluba jakar ta ta ɗauko wayan ta ta haska, a nan ta samo inda abun kunna glof ɗin ɗakin yake ta kunna, ta mayar da ƙofan ta rufe. A hankali ta taka ta isa kan sofa ta zauna tana me bin ko ina da kallo yayinda fuskar ta take a cikin tsantsan damuwa. Tunda ta zauna bata iya motsa wa a wurin ba domin kwantar da kanta tayi a kan kujeran ta mayar da idanuwan ta ta rufe, a haka ta zauna na tsawon wani lokaci. Daƙyar ta iya tashi ta rage after dress ɗin ta ta koma ta ƙudundune a kan sofa ɗin, yanda take ji gaba ɗaya jikin ta babu daɗi har zazzaɓi yake son kama ta, hakan yasa ta kasa taɓuka komi, ga shi kuma barcin ya ƙi zuwan mata don tsananin damuwa da tunani sun yi mata yawa, gaba ɗaya kewar Abee ɗin ta ya cika mata zuciya har hawaye take tsiyayar wa. Ta raba daren a haka bata iya kataɓus ba kuma ta kasa barci, sai daga baya ta tashi ta shiga Toilet tayi alwala ta soma gabatar da sallolin da ake bin ta. Bayan ta idar ta ɗaura da nafila tare da nema wa Abee ɗin ta rahamar Allah. Sai da aka kira sallan subahi kafin ta dakatar da nafilolin da take yi ta gabatar da sallan subahi ɗin. Tana idar wa wani nannauyan barci ya kwashe ta a wurin. Bata farka ba sai taran safe, lokacin daƙyar ta iya tashi a wurin saboda tsaban yanda jikin ta yayi mata nauyi da tsami, daƙyar take iya ɗaga ƙafafuwan ta haka ta isa cikin Toilet ta fito ta zauna a kan kujera, idanuwan ta duk sun gama sauya kala sun kumbura sosai daƙyar take iya buɗe su, da gani ka san damuwa ce da rashin barci ishashshe ya mayar da ita haka. Ta fi mintuna talatin a zaune a kujeran ta kasa motsi.

               Sai wajen ƙarfe Goma kafin tayi odan abin da zata ci aka kawo mata. Dama har da yunwa ya galabaitar da ita amma sabida rashin daɗin bakin ta yasa ta kasa saka komi a cikin nata tun jiya. Daƙyar a yanzu ɗin ma tayi Breakfast ɗin, ko kaɗan abincin be mata daɗi ba dole ta koma tayi odan tea ta Sha sosai sannan ta tashi ta shiga Toilet, wanka tayi ta fito tayi shirin ta, riga da wando ta saka a ciki, sannan ta ɗaura after dress blue color, tayi rolling kanta da ɗankwalin Abayar babu abinda ake gani nata sai kyakykyawar cuty face ɗin ta da ta sake yin haske sosai tayi fayau kamar mara lafiya, komi bata saka a fuskar nata ba ta tattara kayan ta ta fito. Kai tsaye wajen reception ta wuce ta mayar musu da keey ɗin sannan tayi musu sallama ta fice. Har ta fita hotel ɗin baki ɗaya sai kuma ta juya ta dawo ta tambayi ɗaya daga cikin masu aikin tace mata, “She needs to go to Yola, please tell her where to find a car to take her?”

“Ok but don’t say I’m full of questions, aren’t you a native of this country? Because of your temperament and the way you speak English you are not Nigerian.” Cewar receptionist ɗin cikin fara’a

Gyaɗa mata kai MEEMAN tayi ba tare da ta furta komi ba

Murmushi ita kuma tayi tace, “Yes I can understand. You are really beautiful. ”

“Thank you”. Tace da ita itama tana murmusawa

“Okay, I’ll help you get there Bus Stop and get a car there.”

“Ok no problem”.

Ita kuma matar fita tayi ta shiga cikin hotel ɗin, babu jima wa ta dawo ita da wani na miji. Sai ta nuna masa MEEMA tace, “ita zaka kai Tasha, sai ku yi magana da ita zata biya ka”. Sannan kuma ta kalli MEEMAN tace, “This will take you”.

Godiya MEEMAN tayi mata sannan suka fice ita da saurayin. A cikin keke napep ɗin sa suka wuce ya kaita tasha. Shi ta roƙa ya taimake ta ya sama mata motan da zai kaita Yola. Taxi ya samo mata tace, “she will pay in full and be taken alone”.

Me taxi da ya ji zunzurutun kuɗin da zata biya shiyasa ya amince zai kaita ita kaɗai

Haka shima me napep ɗin ta biya sa kuɗi me yawa sannan suka tafi

Sai da tace, “It has started to change where it will change Nigeria’s Money”.

Bayan sun je shi ya amsa ya canzo mata kafin suka tasar wa hanyar Yola, tafiya suke sosai don tsula gudu kawai yake yi. Duk da haka sai magriba suka shiga cikin Adamawa

Me taxi ɗin tambayar ta yayi, “inda zai wuce da ita ya sauke ta?”

A nan ta sanar dashi address ɗin gidan su Abee ɗin ta, da sunan me gidan, kasancewar gidan yayi suna domin Kakan sa Alh. Riskuwa shi ya fara zama a anguwan nasu, shiyasa zai yi wuya idan ka je ɓarayin a kasa gane gidan nasa, kaf anguwan babu wanda be san gidan Alh. Riskuwa bafulatani ba duk da a yanzu ɗin jikokin sa da tattaɓa kunnen sa suke zaune.

         Duk da haka me Taxi ɗin ya sha wahala yana tambayar gidan kafin ya samu wanda ya san anguwan ma, dayake ba ta ɓarayin suka sauka ba. Sun kai bakin gidan wajen ƙarfe 09:12pm na dare. A nan ya sauke ta ta biya shi kuɗin sa. Sai godiya yake mata saboda kuɗin da ta ba shi masu yawa ne, haka ya ja motan nasa ya tafi

Ita kuma tana tsaye tana bin anguwan da kallo ko ina tsit kake ji babu kowa, don har wasu sun kulle gidajen su, dare yayi sosai sai dai akwai hasken farin wata. MEEMA bata saba tsintan kanta a irin wannan rayuwan ba shiyasa duk ta tsure jikin ta har rawa yake yi, daƙyar ta iya ƙarisa wa bakin Gate ɗin gidan ta hau buga wa tana yi tana kalle-kallen bayan ta. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button