MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 1 to 10

           Ta jima a wurin tana buga wa kafin me gadin ya fito da goran sandan sa yana haske-haske da tocilan hannun sa, a fuskar MEEMA ya sauke yana dalle ta da cewa, “kee lafiya daga ina?”

Hannu ta sanya ta rufe fuskar ta tana kau da kai, bata iya magana ba domin bata san ma me yake cewa ba

Shi kuma ƙara dage wa yayi yana haska ta don a tsorace yake da ganin ta, musamman kyawun nata da ganin ta fara fatt da yayi. Daure wa yayi kawai yana sake tambayar ta, “daga inda take kuma wa take nema?”

“Please remove this item on my face”. Tayi maganar tana ɗan goce wa

Dayake shi kuma ya iya turancin sai ya kawar yana sauya harshe ya sake tambayar ta, “Where are you from, Ma’am? Please leave there before I hit you.”

“It was here that I was told the house of Uncle Aliyu my father’s Brother to his place I came.” She spoke looking at him

Me gadin sake haska ta yayi sosai har yana leƙe kafin yace, “You mean you come his home?”

“Yes”.

“So stop here let me go and let them know”. Yafaɗa yana garƙame Gate ɗin ya wuce

Ita kuma jingina tayi da jikin Gate ɗin tana ta kalle-kalle

Har sanda ya dawo shi da Kawu Zubairu yana cewa, “ina take ne?”

“Tana waje”. Inji me gadin. Da sauri ya buɗe masa Gate ɗin suka fita suna haske ta da tocila

“Zulaiha”. Cewar Kawu Zubairu yana sake haska ta da kyau don sake gasgata idanun nasa.

_bakwa yin Comments. Gaskiya zan dena tunda ba kwa so._

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button