MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 1 to 10

Meema bata kalle ta ba bare ta tanka ta

Sai ita kuma ta sake cewa, “but why do you want to change him? Please don’t let your worries affect your love, you are suffering a lot from it, Please do peacking you see he calls again”.

“Hmm”. Kawai Meema tace bata kula ta ba

Ummu Hani Said, “here he is”.

Duk ɗaga kai suka yi suna kallon inda Ummu Hani take kallo

Wani kyakykyawar Balaraben saurayi ne tafe zuwa wajen su, fuskar shi ɗauke da yalwataccen murmushi ya iso wajen su

Daga Ummu Hani har Esha tsaya wa suka yi wajen sa suna amsa sallaman da yayi musu

Ita kuwa Meema har ta yi gaba zata wuce, sai Esha ta janyo ta baya tana cewa, “Please O’o Meema”.

Hararan ta Meema tayi bayan ta dakata daga inda take

Shi kuwa kallon ta kawai yake yi yana doka murmushi

Esha says, “we’ll pass the class, when you’re done find us in class”.

Daga haka suka yi gaba ita da Ummu Hani

Kanta a ƙasa bata kalli inda yake ba

Hakan yasa ya ƙarisa kusa da ita ya tsaya yana faman kallon ta, sun ci mintuna biyu babu wanda ya furta komi

Sai ta ɗago kanta ta zuba masa idanun ta, ganin kallon da yake yi mata sai ta balla masa harara tana cewa, “Please I will be late for class. ”

Cikin sanyin muryan sa yace, “why Beauty did you change me? Wlh I really love you! Why do you want to part with me?”

Cikin ido take kallon shi yayinda ta sake ɗaure kyakykyawar fuskar ta tamau kafin tace, “please let’s stop saying that now, let’s do it later”.

“No, I do not agree. I cannot leave here unless you answer my questions. You know that I love you and this decision you have taken has made me very sad. How do you think I can part with you after tasting your honey love? Wlh I love you Meema, if you want I will kneel in front of you because I will apologize”. Ya ƙare maganar kamar zai yi kuka

Itama fuskar ta da alamun gajiya wa in a calm voice she said, “I told you we will talk later. Please let Me go”.

“Ok When?”

Dafe goshi tayi tana kallon sa tace, “Ishaq problems”.

Dariya yayi yace, “on your love I am crazy”.

Taɓe baki tayi kafin tace dashi, “by tomorrow insha Allah”. Tana gama faɗar haka ta wuce ta bar shi nan. Kai tsaye aji ta wuce, tana zama malamin da suke dashi ya shigo class ɗin.

              Zuwa ɗaya suka sami break, sai suka wuce Hostel wajen Zamiya, a can suka yi sallah suka ci abincin da ta girka musu, sai faman hira suke yi suna dariya amma banda Meema da sai jefi-jefi take saka musu baki.

              Three O.clock suka koma class suka yi lecture ɗaya, sannan kowa ya wuce gida.

               Meema na koma wa gida tayi parcking ta fito tayi cikin gidan, gaba ɗaya a gajiye take amma hakan be sa da ta shiga ta wuce ɗakin ta ba, ɗakin Abee ta wuce ta shiga da sallama

Nurse ɗin dake kula dashi ta amsa mata sallaman tana faɗaɗa fara’an ta tare da mata maraba

Da kallo kawai ta bi su daga ita har Abee ɗin nata ta kasa amsa wa, sai dai gaba ɗaya fuskar ta ta sake haɗe wa ganin ta da poo a hannun ta, “taya ma za’a ce wata ce zata riƙa kula da mahaifin ta a irin wannan yanayin?..”

Muryan Abee ɗin ta da ya ratsa mata kunnuwa yasa ta ƙifta idanun ta da suka kawo ruwan hawaye, cike da ƙunci a zuciyar ta ta ƙarisa wajen sa

While Nurse Zara tuni ta shige Toilet don plushing kashin da yayi

A gaban gadon ta durƙusa tana kallon sa, sai ta saka hannayen ta ta kamo nashi hannun guda ɗaya, cikin rawan murya tace, “Abee..”

Murmushi ya sakar mata a hankali yace, “Ummy why are you crying?”

“Nothing Abee, I’m not crying”. Ta ƙare maganar hawayen ta na silalo mata saman kunci

Girgiza mata kansa yake yi, cike da raunin murya na wanda ciwo yaci sosai yace, “Please Ummy I beg you to stop crying ok? I’m not happy to see your tears.”

Tamke bakin ta tayi tana saka hannu biyu ta share hawayen tana faɗin, “ok Abee I’m stop, you see?” Sai ta ƙare maganar da sakin murmushin da ya bayyana jerin ƙananun fararen haƙoran ta, wanda har dumples ɗin ta suka samu damar fito wa

“Ok, did you go to school today?”

“Na’am Abee, I went to school, but I’m sorry I didn’t come in to check on you. ”

Murmushi yayi yana gyaɗa kansa yace, “don’t worries, go eat and rest ok?”

Amsa mishi tayi kafin ta ɗago hannun nasa a hankali ta sumbace sa, sannan ta tashi daga durƙuson da tayi, a time ɗin ne Nurse Zara ta fito daga Toilet ɗin, kallo ɗaya Meema tayi mata ta ɗauke kai tana fice wa

Ita kuma Nurse Zara ta gyara mishi pilown da ya sauke kansa, sannan ta tambaye sa “ko da abinda yake buƙata kuma?”

Girgiza mata kai kawai yayi

Sai ta juya ta ɗauko airfreshna ta fesa a ko ina sabida warin kashin da ya ɗuma ɗakin ya fice, bayan ta gama ta fice a ɗakin.

                  ******

               Da kuka Meema ta koma ɗakin ta, tana shiga ta faɗa kan gado tana ci gaba da rera kukan nata, wanda inda da sabo ya rigada ya zame mata jiki, a kullum tausayin Mahaifin nata ƙara yawa yake yi a zuciyar ta, ta kasa saba wa da wannan ƙaddaran da Allah ya ɗaura masa, kullum gani take yi tamkar zai tashi ya koma kamar da, ya riƙa mata wasa kamar yanda ya saba yin mata, su riƙa cin abinci tare suna wasa da dariya tare, amma kuma ciwo ya yanke mata wannan ƙauna da jin daɗin, wanda tana ganin babu ranan da zata sake shiga cikin farin ciki idan har ba mahaifin ta bane ya warke ya koma kamar da ba, ba ta ganin akwai ranan da walwala da jin daɗin ta zai dawo

Hawayen ta ta saka hannu tana share wa yayinda wasu suke sake ɓullo mata, babu abinda ke sake bata haushi illa yanda mahaifiyar ta ta kasa kula da Abee ɗin ta, sai wata ce take iya cin kashin sa taci fitsarin sa, sannan kuma ta ƙetara muhallin da ba nata ba, a kullum sake jin tsanar mahaifiyar ta take yi, tana ganin kamar har da baƙin cikin ta Abee ɗin ta ya kasa samun lafiya, ko da be faɗa mata ba ta san yanda yake jin ƙuna da azaban tafiyan ta, ta zaɓi son duniya da son zuciya ta rabu da su, a kan abinda be taka kara ya karya ba, ita a ganin ta babu mahaifiyar da zata tafi ta bar ɗiyar ta da mijin ta a halin ƙunci da neman taimako, mahaifiyar ta ba mutum bace, kuma bata da zuciyar imani

Fashewa tayi da wani sabon kukan, cikin tsananin ƙunan zuciya tace, “I hate you so much Ummee! I hate you!! I hate youuuu”. Hannu ta sa ta rufe fuskar ta, in slow voice tace, “Why Ummee? Why did you leave us?”. Ta jima tana kukan wanda har kanta ya ɗau zugin zafi, sannan ta dakata tana tashi ta zame kayan ta ta shiga Toilet, wanka tayi ta ɗauro alwala ta gabatar da sallan Asar bayan ta saka shimi iya gwiwa da dogon Hijab, tana idar wa ta ɗaga hannu ta soma kwararo addu’o’i tana kuka, gaba ɗaya duk wani addu’ar ta yanzu nema wa Abee ɗin ta lafiya take yi, domin shi ne farin cikin ta a yanzu, idan har babu shi haƙiƙa ba ta ba sake farin ciki a duniya.

            House girl ɗin su ne ta shigo da sallama

Hakan yasa ta dakatar da addu’ar nata tana shafa wa a fuskar ta, sannan ta sauke kumburarrun idanun ta a kan ta ba tare da tace mata komi ba illa amsa sallaman da tayi a ranta

“Sayyadaty, hunaki duyuufu fiis saàlun, jaà’uu ila Abee”. (“Ma’am akwai baƙi a Parlour, sun zo wajen Abee ne”.)

Jimm MEEMA tayi har a lokacin tana kallon ta, sai kuma tace, “izhab wa’as’al man hum?” (“Je ki tambaya su wane ne?”)

“Ok Ma’am”. Ta miƙe da nufin fice wa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button