MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 1 to 10

Sai kuma ta dakatar da ita tana ce mata, “Ƙaàlat lahum an yaruûhaà huna”. (“tace musu ga ta nan.”)

Bayan ta fita sai ta tashi ta zare Hijab ɗin jikin ta, daga ita sai shimin jikin ta sannan ta zira room slippers a ƙafafuwan ta ta fice, tana sauka downstairs ta hange su su biyu a cikin parlour’n, bata gane ko su wane ne ba sai da ta iso gab da su sannan fuskokin su suka yi mata maraba, baza ta taɓa manta waɗannan mutanen ba, duk da kusan shekaru shida kenan rabon su da tako wannan ƙasan, yayyin mahaifin ta ne dake zaune a Nigeria da suka haɗa uba ɗaya, waɗanda suka watsar da su suka raba hanya da su, saboda tsantsan tsanar da suka yiwa mahaifin ta, shiyasa ma ko zuwa nan ɗin ba sa yi.

             Tana isowa tabi su da kallo hannayen ta a ƙugu, ko ba’a faɗa mata ba ta san ba arziƙi ya kawo su ba kamar yanda suka saba zuwa a shekarun baya, tunda su ko kaɗan basu da mutunci, shiyasa itama yanda take ji a ranta duk abinda suka zo dashi tana dai-dai dasu, zuciyar ta sosai take mata ƙunci baza ta taɓa raga musu ba idan har za su taɓa mata Abee 

Wanda yake shi ne Babba ya soma magana da faɗin, “ke baki da kunya ne zaki zo ki tsaya mana akai dan uban ki?”

Sai ɗayan yace, “taya zaka tambayi kunya a nan Yaya bayan ka ga yanda tazo mana a tsatstsaye tana turo mana ƙirji? Ai daga gani ka san babu kunya domin Faruk be koya mata ba, shiyasa yaƙi yarda ya koma ƙasar sa tunda ya san abinda yake faman yi a nan. Yanzu dan ubanki ke da kika zo gaban mu kika yi ƙere-ƙere rashin kunya zaki yi mana ko me? Uban naki shi ne dai-dai damu ba ke ba”.

Duk maganganun da suke faɗa ko ɗaya MEEMA bata ji su ba domin ba ta jin Hausa. kuma su ma sun san da hakan; amma dayake tsiya yaci ransu shiyasa suke ta maganar ba tare da sun tuna ba

She then said to them, “what are you saying I do not hear you”.

Tsaki Yaya Ali yaja yana cewa, “matsiyaciya ubanki muka ce shegiya..” sai kuma ya juya harshe cikin turanci yace, “ina shi uban naki muka ce?”

Wani kallon banza ta watsa musu kafin tace, “He is not here, what you want?”

Salati suka saki lokaci ɗaya suna kallon ta

“Yanzu Zulaiha mu kike faɗa wa wannan maganar? Yanzu har idanun ki sun buɗe da zaki yi mana rashin kunya a matsayin mu na Yayyin ubanki? Tirƙashi..” cewar Yaya Ali cikin harshen turanci

Ita kuwa bata ma tsaya sake jin ta bakin su ba ta juya zata wuce

Sai Zubairu ya kwaɗa mata kira, “Zulaiha.. Zulaiha”.

Amma ko juyo wa bata yi ba ta haye Steps da gudu tayi ɗakin ta, kan gadon ta ta haye tana ɗaukan wayan ta ta soma Game cikin sauri-sauri, sosai ranta ke a matuƙar ɓace shiyasa ta kasa controling kanta tsaban yanda ranta ke ƙuna, sai kuma ta jefar da wayan a saman gadon tana miƙe wa da sauri, fita tayi da gudu ta nufi downstairs, ganin babu su a parlour’n sai ta nufi ɗakin Mahaifin ta da sauri ta bankaɗa ƙofan da ƙarfi

Yaya Ali da Zubairu dake gaban gadon da Abee yake kwance sun tasa shi gaba suna ta tsitsiye shi da bala’i duk da kuwa sun ga mawuyacin halin da yake ciki, hakan be sa sun dakata daga amayar masa da tijaran da suka ɗibo ba, ko tausayi babu a lamarin su. Buɗe ƙofan da MEEMA tayi ne sai duk suka tsaya suna mayar da kallon su kan ƙofan, inda suka sauke idanuwan su kanta da itama take bin su da kallo idanuwan ta sun kaɗa sun yi jawur tsaban ɓacin rai.

???????????? 

*MEEMA FAROUK*

               ????????????

*NA_NAFISA ISMA’IL*

*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????

“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

          *SADAUKARWA*

_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._

                 *NO_ 3 & 4*

     Gaba ɗaya idanuwan ta sun rufe ta manta da cewa su ɗin ƴan uwan mahaifin ta ne, ta nufi ciki a zuciye tana cewa, “what are you doing here What brings you to my Abee room? Get out .. get out…”

Zubairu ne ya dage ya falla mata marin da sai da yasa ta duƙe a wajen tana tsandara ihu

Daga Nurse Zara da House girl ɗin su dake Parlour sun yi cirko-cirko sai da suka tsorata saboda ihun MEEMA da suka ji, musamman ma Nurse Zara tunda bata san su ba sai House girl ɗin ne tayi mata bayani da suka nemi shiga ɗakin Abee zata hana su, dayake ita ta san su tun shekarun baya da suke zuwa.

        Yanda MEEMA take ihu zaka ce an yanka ta ne saboda abinda bata taɓa ji bane ya faru a rayuwar ta, tunda uwar ta ta zuƙuna ta haife ta ba’a taɓa marin ta ba, shiyasa duk ta gama gigicewa ta rasa gabas da yamma

Abee kuwa tuni ya soma kuka saboda ganin abin da Zubairu ya yiwa ɗiyar sa, idan da ace yana da ƙafafun tashi wlh babu abinda zai hana shi be rama mata ba saboda yanda zuciyar sa take tafarfasa, cikin rawan murya da kuka daƙyar ya soma maganar cikin gurɓataccen hausan sa yace, “Yaya Zubairu meyasa ka maran min Ummy? Meyasa.. meyasa? Me tayi muku? Don Allah kar ku kashe min ita na roƙe ku”.

Yanda Abee ke yi ne sai duk suka saki baki suna kallon shi

“Ikon Allah yanzu kai Faruk don an yi mata wannan ɗan marin shi ne kake kuka ka tayar da hankalin ka haka? Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.. tabbas  maganar da ake faɗa ya tabbata, ashe bayan rashin auren da ka ƙi kay mata take yawon karuwanci kai ma bin ta kake yi wato? Ita shafaffiya da mai baza a taɓa ta ba tunda kana samun abinda kake so ko?…”

“Enough Yaya… Enough…?” Yayi maganar cikin rawan baki sosai wanda daƙyar ya iya faɗi tsaban tashin hankalin dake cin sa da jin abinda ɗan uwansa yake faɗa

Yaya Ali da yayi maganar sai ya sake cewa, “dalla rufe mana baki ko zaka ce ƙarya ne bayan ga shi mun gani? Shiyasa Allah ya kama ka ga ka nan a kwance babu ƙafafu ciwon Cancer ya kama ka, to, wlh kaɗan ma ka gani muddin baka canza alƙibla ba, ka gudu ka bar ƙasan ka ka zo nan ka ɗauki al’adun wasu, sannan ka koya wa ɗiyar ka karuwanci ga ta nan taƙi aure ganɗamemiya da ita, ƙannin ƙannin bayan ta mun aurar da su amma kai kaƙi, shiyasa ma matar ka ta gudu ta barka tunda muna da labarin komi, abin ma da yasa ka gan mu a nan don mun ji labarin ciwon ka ne, kar duniya ta tsine mana a matsayin mu na ƴan uwan ka muka zo mu taimake ka, zaka bamu wannan mara kunyan yarinyan taka mu je can mu aurar da ita ko ka rage nauyi a kanka”.

Duk maganganun nan da Yaya Ali yake yi gaba ɗaya Abee ya tsaya yana sauraron sa inda hawayen fuskar sa ke sake kwaranya kamar an kunna famfo, domin ya ma kasa magana

MEEMA da sai yanzu ta gama dawowa hayyacin ta, sai ta tashi da gudu ta faɗa jikin Abee ɗin ta ta sake sakin kuka me tsuma rai, sosai take kuka tana kiran sunan sa, so take yi ta ce mishi ya dena kuka amma bakin ta ya ƙi furta wa illa kukan da take yi

Shi kuwa sosai jikin sa ke rawa yana hawaye babu daman taɓa ta, domin gaba ɗaya jikin sa ba ya aiki

Zubairu yace, “ka gani ko Yaya Ali, tun bamu je ko ina ba suna son su nuna mana halin karuwancin”. Sai ya kalli MEEMA ya daka mata tsawa da cewa, “tashi ki je ki haɗo kayan ki mu tafi”.

Ita duk bama tasan me suke magana a kai ba, ko kaɗan taƙi ɗagowa a jikin Abee illa kukan ta dake ƙara yawaita

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button