MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 1 to 10

Abee daƙyar yace dasu, “babu inda ɗiya ta zata bi ku wlh, na gode da taimakon naku Yaya zaku iya tafiya”.

A zuciye Yaya Ali yace, “haka kace ko? Mu yi tattaki tun daga uwa duniya amma kaƙi bin umarnin mu? To shikenan Allah ya gani mun sauke haƙƙin ka tunda haka ka zaɓa. Taho mu je Zubairu yau zamu koma gida”.

Haka suka fice gaba ɗayan su a fusace.

        Sai lokacin MEEMA ta ɗago kai tana kallon Abee ɗin da idanuwan ta da suka kaɗa suka yi jazur tace, “What are they saying Abee? Please tell me.”

“No Ummy stop talking ok?”

Gyaɗa masa kanta tayi inda sosai hawayen ta suke tsiyaya

Girgiza mata kai yayi yana cewa, “Stop crying please I don’t want to see your tears flow. Please Ummy”.

Hannayen ta ta saka tana share hawayen, sai kuma ta saka hannun tana shafa inda Zubairu ya mare ta, wurin sosai ya kumbura yayi ja har yatsun sa sun fito, sai ta sake shigewa jikin Abee ɗin tana ɓoye fuskar ta jin wasu sabbin hawayen sun sake zubo mata

Be ce mata komi ba illa a haka suka ci gaba da zama, yana jin yanda take fitar da numfashi da shashsheƙa na tsawon lokaci kafin kuma yaji fitar numfashin nata ya sauya, hakan yasa ya gane ta samu barci, shima lumshe idanun sa yayi yana me jin hawaye sun cika mishi ido, ba komi ya tuna ba sai rayuwar su na baya, da yanda ada suke tsantsan cikin farin ciki ako da yaushe, sai dai kuma lokaci ɗaya Allah ya jarabbe shi da wahalhalun ciwukan nan, Cancer da ciwon sugar, yayi jinya na ɗan wasu watanni a asibiti inda lokaci ɗaya kuma side ɗin jikin sa ya dena aiki gaba ɗaya, mafarin kenan da suka sake rasa gaba ɗaya farin cikin su

Daga baya likitocin sun sallame shi domin sun ce, “jinyan sa sai dai a gida, saboda zai daɗe be warke ba, kuma hakan zai cinye musu kuɗi sosai ga wahalhalun zirga-zirga na asibiti,” dole aka mayar dashi gida likita na kula da shi

Tashi ɗaya mahaifiyar MEEMA ta nuna gajiyawar ta da mishi hidima na yau da kullum a matsayin shi na majinyaci wanda be iya taɓuka wa kansa komi

A wani ranan da baza su taɓa manta wa ba MEEMA ta tafi school, sai dawowa tayi ta tarar da Ummeen ta ta tafi. Wanda sanadiyar tafiyan nata ne ciwo ya sake yin tsanani ga Mahaifin ta, domin ada yana iya magana sosai amma daga baya ya dena magana gaba ɗaya

MEEMA ta sha kuka wanda hakan ya saka har sai da tayi jinya tsaban ruɗu da tashin hankalin da take ciki, tana ganin lokaci ɗaya Allah ya jarabbe su da matsaloli kala-kala har hakan yayi sanadin tafiyan mahaifiyar ta, ta kasa yarda mahaifiyar ta zata yi musu haka ita da mahaifin ta, duk rayuwar da suka gina tsawon shekaru amma lokaci ɗaya ta rushe musu, meyasa baza tayi haƙuri na ɗan lokaci Abee ya samu lafiya ba? Meyasa zata nuna gajiyawa da laluran Abee ɗin ta? Ashe dama ba son su take yi ba da har zata iya tsallake su tabar su a wannan duniyar? Haƙiƙa abin ya taɓa ta wanda lokaci ɗaya gaba ɗaya duniyar tayi mata zafi ta sauya mata, wanda tana ji kamar gwara mutuwar ta da wannan rayuwar, sai lokaci ɗaya MEEMA ta sauya sabida ƙunci da raɗaɗin da Ummeen ta ta sanya mata, ga kuma uwa uba wanda tafi ƙauna yana kwance tamkar matacce, hakan na nufin ta rasa kowa nata kenan? Ada ita me son fara’a ce matuƙa, ga surutu kamar aku don idan ta soma zuba ba ta jin bari, shiyasa wannan halin nata sai ya zamana kowa nata ne, idan har ta zauna a wuri dole sai ka santa, mahaifin ta ya koya mata sangarta da shagwaɓa domin ita bata san bari ba, hakan yasa ta taso yarinya me kazar-kazar da son Wasa har girman ta, tana jin ta tamkar dai yarinya ƙarama ce, ga dolanci irin na ƴan fari kuma gata Auta. Ga kuma yanda iyayen ta suka ɓata ta da gata. Lokaci ɗaya sai kuma komi ya juya mata baya, ta dawo tamkar Miskila.. ba ta dariya bare murmushi kullum gani take yi rayuwar ta mafarki ne akwai ranan da zata farka shiyasa ko yaushe cikin tunani take da damuwa, idan ka ganta tana murmushi to tabbas tana gaban Abee ɗin ta ne domin saka shi farin ciki.

       Shima da yaci gaba da samun kulawa domin tuni an kawo Nurse tana kula dashi ita take mishi komi, sai kuma likitan dake duba shi. a sannu a sannu ga shi har yana iya yin magana, shima daƙyar domin wani lokacin ba ya iya yi duk da yana son Yi

Babu abinda ya fi komi saka MEEMA farin ciki illa ganin Mahaifin nata ya soma magana, hakan na nufin wata rana zai warke ya tashi kamar yanda yake a baya. Kuma za su ci gaba da rayuwar su ta farin ciki ko da babu Mahaifiyar ta a tare da su. Idan ta tuna hakan shi ne take jin salama a rayuwar ta

Da farko ta dena zuwa school, sai da mahaifin ta ya soma samun sauƙi sannan ya matsa mata a kan, “ta koma”. Yanzu haka tana degree ɗin ta ne a fannin Mas.Com. kuma tana zangon ƙarshe domin watanni ya rage mata. She’s 26years all.

         Abee shi ɗaya ne wajen mahaifiyar sa, asalin su ƴan Yola ne Fulanin can. Mahaifiyar shi ita ce ta farko wajen mahaifin su Alh. Ahmad Riskuwa. Matan sa biyu da Maman Faruk sunan ta Zulaiha da kuma Jammatu, amma suna kiran ta da Jamma

Bayan Shekaru me tsawo da Zulaiha bata haihu ba sai iyayen Ahmad suka sanya shi ya ƙaro aure ya auri Jamma, ita kuma daga zuwan ta ta haifi Yaya Ali, bayan shi ta jima kafin ta sake haihuwa, inda ta sami cikin Zubairu

Ashe itama Zulaiha tana da cikin amma babu wanda ya sani. Sai da Jamma ta haifi Zubairu kafin cikin Zulaiha ya bayyana. Aikuwa ta sha habaici wajen su Jamma da ƴan uwan Ahmad, sai dai bata biye musu ba tunda Allah ya bata nata ba juya bace ita kamar yanda suka ce ɗin

Zubairu na da watanni huɗu aka haifi Faruk

Zo ku ga murna wajen Ahmad domin ji yake yi kamar ba’a taɓa haihuwar masa ba sai yanzu, domin ƙaunar da yake yiwa Zulaiha ya wuce kwatance, shiyasa dangin shi suke jin haushin ta sosai, sai kuma suka sami dama wajen rashin haihuwar ta suka saka shi ya ƙaro aure.

     Tun tasowan yaran Ahmad ya rigada ya bambanta su, domin ba ya iya ɓoye soyayyar shi ga Faruk. Wannan dalilin ne Jamma da yaran ta suka tsani Faruk sosai, ko kaɗan ba ya jin daɗin zama dasu illa wajen mahaifin sa da Mahaifiyar sa

Ana haka Jamma ta soma biye-biye wajen bokaye domin ta raba Faruk da soyayyar mahaifin shi, inda kuma ta sanya wa Zulaiha ciwo lokaci ɗaya ta mutu

Mutuwar nata shi ya jawo Ahmad ya samu ciwon zuciya, inda yayi jinya me tsayi kafin ya rasu.

     Faruk ya taso cikin maraici da uƙuban rayuwa, wanda ya gummaci mutuwar sa da rayuwar sa. Sai dai Allah shi ne me rayawa shiyasa har ya kai girman sa. A lokacin da mahaifin sa ya rasu ya gama secondary School ɗin sa, koda ya mutu kuma an ƙi ba shi gadon shi bare yaci gaba da karatu, sai ya koma aikin ƙarfi tare da taimakon dangin mahaifiyar shi da suka rage mishi, a haka yake rayuwa yake samun abin saka wa a bakin sa, domin be da wani amfani a gidan su tunda har koran sa ma sun yi, sai daga baya ne da ƴan uwan Maman shi suka nema masa ƴancin sa shi ne suka bar shi yana kwana a zauren gidan

Rayuwa taci gaba inda har su Yaya Ali suka gama karatun su suka sami aikin yi

A lokacin ne Allah ya taimaki Faruk ya haɗu da wani uban gida me kuɗin gaske yana mishi gadi, tsawon lokacin da ya ɗauka yana mishi aiki wanda ya yaba da hankalin sa, sai ya ɗauke sa ya tafi dashi can Riyadh kasancewar a can matar sa da ɗiyar sa ɗaya suke zaune, a nan kuma Nigeria kasuwanci yake yi yana da Company, nan Faruk yake mishi gadi. Ya mayar dashi can ne sabida ya riƙa taimaka mishi a can tunda ya yaba da hankalin sa, ga kuma tausayi da yake ba shi domin ya san komi cikin rayuwar sa tunda ya taɓa tambayar shi, shiyasa ya yanke shawaran kai shi can Riyadh ya kula masa da dukiyar sa sannan kuma ya saka shi makaranta, tunda yayi alƙawarin sai ƴan uwan sa sun yi alfahari dashi, sai sun dawo suna dana-sanin koran sa da suka yi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button