MEEMA FAROUK Page 1 to 10

Wannan ne mafarin da yasa Faruk ya dawo Riyadh da zama har yayi karatu ya sami aikin yi, inda lokaci ɗaya Allah ya buɗa mishi yayi kudin kanshi, a lokacin har ya auri ɗiyar uban gidan nasa tunda soyayya me ƙarfi ta shiga tsakanin su, sai dai Allah be taɓa basu haihuwa ba shekara da shekaru
Shekara goma suna zaune da Abiha kafin Allah ya ɗauki ranta, inda ta rasu har lokacin bata taɓa ko da ɓarin wata bane, shi kuma Faruk yaƙi yin aure domin kawai farin cikin ta, yana ganin be kyauta ba muddin yayi mata kishiya saboda gudummawar da mahaifin ta ya ba shi a rayuwa, domin a lokacin ma Mahaifin nata tuni ya daɗe da rasuwa sai mahaifiyar ta, ita kuma ta koma can dangin ta har ta sake aure.
Mutuwar Abiha ya taɓa Faruk sosai, inda ya jima be sake aure ba, a lokacin ne ya yanke shawaran zuwa Nigeria neman ƴan uwan sa tunda ya rasa kowa nasa a nan, zuwan sa ya tarar da su ma su Yaya Ali sun sami ci gaba sosai, tunda duk kansu suna aiki da albashi me tsoka, inda suka rushe gidan su suka yi na zamani ko wanne da nashi part ɗin tare da matan su da yaran su
Abubuwa da dama sun sauya mishi domin an yi rashi kala-kala, inda Jamma tuni ta daɗe da rasuwa itama, sai kuma wasu daga cikin dangin Maman shi na kusa.
Su Yaya Ali sun yi matuƙar mamakin ganin Faruk ya sauya yayi kuɗi sosai, domin ko hausan ma tuni ya ɓace a bakin sa sai ɗaiɗai. Sai hassada ya cika zuciyar su ganin ya fi su
Sai dai shi be duba wannan ba illa alkhairin da yake ta musu. Duk yabi ya zagaye dangi ya gaishe su. Inda da ya tashi tafiya sai su Yaya Ali suka ce basu san zancen ba, wai, “a dole sai ya dawo Nigeria ya zauna da su”.
Shi kuma yace musu, “bazai iya ba tunda ya baro dukiyan sa da komi nashi a can,” domin a lokacin har Company biyu ne dashi a can. Haka suna ji suna gani ya tafi ya bar su domin a tunanin su za su iya juya shi, sai dai yayi musu alƙawarin zai riƙa dawowa yana ganin su.
Allah da ikon sa a faɗi tashin nan da yake yi na ziryan zuwa Nigeria duba ƴan uwan sa sai suka ci karo da mahaifiyar MEEMA, sunan ta Zulaiha ƴar Kaduna ce. Inda lokaci ɗaya soyayyar ta ta shiga Abee kuma be yi ƙasa a gwiwa ba ya sanar mata, duk da a lokacin yana da shekaru sosai ba kamar ita yarinya jagal ba, amma kuma kasancewar sa me kuɗi yana samun jin daɗi sai girman nasa ya ɓoye, tamkar yaro ɗan shekara 35.
Babu abinda ya ƙara faranta mishi rai jin sunan ta Zulaiha sunan mahaifiyar shi, shiyasa ya ɗauki son duniya ya ɗaura mata, inda suka yi soyayya na ɗan ƙanƙanin lokaci domin shi yace, “ba wasa ne ya kawo shi ba, Auren yake so da sauri”.
An so ayi fitina sanda ya kai labarin wajen ƴan uwan sa, domin su a lokacin har sun yanke shawaran za su zaɓa mishi mata, sam suka ce, “basu yarda ya auri Zulaiha ba”.
Amma shi kuma yace, “atabam ita yake so”.
Dole ba don sun so ba suka bar shi ya aure ta.
An yi auren lafiya an gama lafiya inda ya ajiye ta a gidan sa na can Riyadh, kamar jira ake yi tana shiga ta samu cikin MEEMA, zo ku ga murna wajen Faruk, tun a ciki ya ɗauki son duniya ya ɗaurawa ɗiyar sa.
Bayan wasu watanni aka haifi MEEMA kyakykyawa ƙin kowa ƙin wanda ya rasa, sak mahaifin ta bafulanan usuli don basu da maraba, inda ya mayar mata da sunan mahaifiyar sa Zulaiha, sannan kuma sunan Ummeen ta itama. Shiyasa suke kiran ta da MEEMA tun tasowar ta, kuma da haka take amfani dashi a school wato *MEEMA FAROUK.*
Ta taso cikin gata sosai fiye da tunanin mutum, bata san babu ba ko hantara har sai sanda ta soma girma ta fara gane ƴan uwan Abee ɗin ta dake zuwa gidan sun takurawa iyayen ta, har ita kanta basu bari ba domin sun dinga dungure mata kai kenan, kuma duk idan sun zo sai sun saka iyayen ta kuka saboda baƙaƙen maganganun su, shiyasa tuni Abee ya dena zuwa Nigeria gaba ɗaya
Inda akwai wani lokacin da suka yi faɗa baram-baram yace, “kar su sake zuwa mishi gida”. Wannan dalilin ne yasa suka dena zuwa gaba ɗaya, sai dai idan suna neman kuɗi me yawa a wurin sa sai su zo dole sai ya basu. Idan ba kuɗi ba kuwa babu abinda ke kawo su. Da haka suka sami salama.
Duk da iyayen MEEMA ƴan Nigeria ne amma bata taɓa koyan Hausa ba, ba wai don sun ƙi koya mata bane, a’a sai dai don ba ya birge ta Yaren, bata damu ko kaɗan ta koya ba, kuma su ma basu cika yi ba tunda shi Abee har hausan ma ya ɓace a bakin sa sai kaɗan, idan kuma yana yi tamkar yana yare, ba kowa ke iya ganewa ba. Iyakan Turanci da Larabci suke yi.
Wannan shi ne taƙaitaccen tarihin su.
✳️✳️✳️✳️✳️
Shigowar Nurse Zara ne ya sanya Abee ya buɗe idanun sa da suka kaɗa suka yi jazur
Da sauri ta ƙarisa wajen sa tana mishi sannu
Be iya amsa wa ba sai da ya ja lokaci kafin a hankali yace da ita cikin larabci, “ko zata iya ɗaukar MEEMA ta kaita ɗaki ba tare da ta tashi ba?”
Dariya ma maganar taso bata, taya zata iya ɗaukar ganɗamemiyar budurwan da ta girme ta ta kai ta ɗaki kuma ba tare da ta tashi ba? Duk da dai ta fi ta jiki amma dai ta san MEEMA ta girme ta. Sai tayi saurin girgiza mishi kai itama ta mayar masa cikin harshen larabcin, “baza ta iya ba”.
Sai yace mata, “ta tafi”.
Haka ta fice tana rufo musu ɗakin.
Dole ya bar MEEMA a kan jikin sa taci gaba da barcin ta yana faman kallon kyakykyawar fuskar ta wanda ya kasance irin nasa sak. Murmushi ne tare da hawaye ya saki lokaci ɗaya. Babu abinda yake ƙauna sama da MEEMA a duniyar nan, ba don haka ba da tuni ya roƙi Allah ya ɗauki ransa saboda ƙuncin da ke cikin ransa, amma kuma tunawa da ita a rayuwar sa yana saka shi jin sanyi a ransa, wanda yake fatan samun lafiya nan gaba domin yaci gaba da rayuwa da ita a duniyar sa. Duk da ya san dole wata rana zata yi aure ta bar shi, kuma har a zuciyar sa yana son ganin kafin ya mutu ya danƙa ta wajen wanda zai zame mata jigo a rayuwar ta, ma’ana mijin ta, ba ya fata ya mutu ya bar ta hannun ƴan uwan sa, tun yanzu ma sun zo amsar ta wanda ya san duk saboda kuɗin sa ne, suna ga kamar zai mutu a yanzu shiyasa za su ɗauke ta don su mallaki komi nata. Ba ya fatan hakan ya faru dole ne yayi wani abu a kai, amma taya? Ta ina zai faro wajen samar mata abokin Rayuwa? Ta ina zai saka ta ta yarda tayi aure bayan tace, “muddin yana numfashi a duniya to babu ita babu aure a rayuwar ta! Baza ta taɓa tafiya ta bar shi ba har sai idan ya samu lafiya ne”. A koda yaushe wannan kalaman nata take yawan sanar masa. Be san ta ina zai fara shawo kanta ta amince da ƙudirin sa ba.
Lumshe idanun sa kawai yayi yana haɗiyar wani yawu me ɗaci.
????????????
*MEEMA FAROUK*
????????????
*NA_NAFISA ISMA’IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????
“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*SAKAMAKON SALLAH 1*
_Mun sani cewa a shika-shikan musulunci ɗin nan guda biyar bayan imani sai tsayar da sallah. Abdullahi Ibnu Mas’ud ya ce, “Na taɓa tambayar Manzon Allah cewa wane aiki na ɗan Adam Allah ya fi so?” Sai Annabi ya ce, “sallah”. Na sake cewa, “daga ita fa?” Sai Annabi ya ce, “kyautata wa iyaye”. Na sake cewa, “daga wannan fa?” Sai ya ce, “sai jihadi.”_